Majalisar Shari'ar Musulunci Ta Goyi Bayan Rufe Makarantu, Ta Kirayi Jihohi 3 Su Bi Sahu
- Majalisar shari'ar Musulunci ta Najeriya ta goyi bayan rufe makarantu a Ramadan, ta ce hakan zai taimaka wa dalibai wajen kare lafiyarsu daga zafi mai tsanani
- Majalisar ta bukaci jihohin Zamfara, Sokoto da Jigawa su ɗauki wannan mataki, tana mai cewa an dauki wannan shawara ne don amfanin addini da kiwon lafiya
- Ta ce gwamnatocin jihohi na da cikakken iko kan jadawalin makarantu, tana sukar masu adawa da matakin, ciki har da kungiyoyin Kiristoci
- Ta yi kira ga duk masu ruwa da tsaki su mutunta wannan hukunci, tana mai yabawa gwamnatocin da suka fifita jin dadin dalibai fiye da sauran batutuwa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Majalisar Shari’a ta Najeriya (SCSN) ta kare matakin wasu gwamnatocin jihohi a Arewa na rufe makarantu saboda azumin watan Ramadan.
Majalisar ta ce hakan zai kare lafiyar dalibai daga zafin rana da ake fama da shi musamman a Arewacin Najeriya.

Asali: Facebook
Rufe makarantu: Majalisar shari'a ta shawarci jihohi
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakatare-Janar na majalisar, Nafiu Baba-Ahmad, ya sanya wa hannu, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majalisar ta bukaci jihohin Zamfara, Sokoto da Jigawa su ɗauki wannan mataki saboda tsananin zafin rana a yankunansu.
SCSN ta yi watsi da korafin Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) da wasu NGOs, tana mai cewa gwamnatocin jihohi na da cikakken iko kan jadawalin makarantu.
Sanarwar ta ce:
“Wannan mataki yana tabbatar da ci gaba da karatu ba tare da dalibai sun kasance a banza ba, an duba shi sosai tare da karɓuwar iyaye."
“Abin mamaki ne yadda CAN ta yi shiru lokacin da yajin aikin ASUU ya hana karatu na tsawon lokaci, amma yanzu tana adawa da wannan canjin kwanaki 25 kacal."

Kara karanta wannan
Ana batun cin zarafin Sanata, Remi Tinubu ta bukaci karin wakilcin mata a majalisa

Asali: Twitter
Majalisar shari'a ta caccaki kungiyar CAN a Najeriya
Majalisar ta soki barazanar daukar matakin shari’a ko yajin aiki kan rufe makarantu, tana mai cewa hakan raini ne ga ikon gwamnatocin jihohi.
Ta ambato dokar ilimi ta 1 ga Janairu, 1964, tana mai cewa gwamnoni na da ikon yanke lokacin hutu, sai dai a jihar Kogi inda dokar ba ta aiki.
SCSN ta ce CAN ba ta da rawar takawa a tsarin ilimi na jihohin Arewa, tana mai cewa babu wata gwamnati da ke bukatar neman amincewa kafin daukar matakin makarantu.
Majalisar ta jinjinawa gwamnatocin da suka aiwatar da matakin, tana mai kira ga sauran jihohin Arewa su dauki irin wannan mataki don amfanin dalibai.
Ta bukaci kowa ya mutunta hukuncin gwamnatocin jihohi, tare da guje wa tsoma baki a dokoki da suka shafi dalibai da iyalansu kai tsaye, The Nation ta ruwaito.
Gwamnoni sun yi wa CAN martanin rufe makarantu

Kara karanta wannan
Zargin lalata: Sanata Natasha na tsaka mai wuya, Hadimin Osinbajo ya tona shirin majalisa
Kun ji cewa Gwamnatocin Kebbi, Bauchi da Kano da suka rufe makarantu saboda Ramadan sun yi martani kan ce-ce-ku-ce da ake yi.
Gwamnatocin sun bayyana cewa ba za su sauya matsayar rufe makarantu a watan Ramadan ba kamar yadda ake bukata.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng