Ana Batun Cin Zarafin Sanata, Remi Tinubu Ta Bukaci Karin Wakilcin Mata a Majalisa
- Sanata Oluremi Tinubu ta jaddada muhimmancin ware kujeru na musamman ga mata a majalisar dokoki da mukaman zartarwa
- Ta ce mata na taka muhimmiyar rawa a ci gaban kasa, don haka yana da muhimmanci a ba su karin dama a siyasa da shugabanci
- Uwargidan shugaban kasar ta fadi haka ne don nuna goyon baya ga kudirin da zai ware 35% na kujerun majalisun jihohi da tarayya ga mata
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Uwargidan Shugaban Kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta bayyana goyon bayanta ga kudirin dokar da ke neman ware kujeru na musamman ga mata a majalisar dokoki.
Kudirin, wanda Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Benjamin Okezie Kalu, ya dauki nauyin gabatarwa, yana kan matakin nazari a halin yanzu.

Kara karanta wannan
Zargin lalata: Sanata Natasha na tsaka mai wuya, Hadimin Osinbajo ya tona shirin majalisa

Asali: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa an gabatar da irin wannan kudiri a Majalisar Tarayya ta Tara ta hannun tsohuwar ‘yar majalisa, Nkeiruka Onyejeocha, amma bai samu nasarar wucewa ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Oluremi Tinubu, wacce ta jaddada muhimmancin kudirin ta kuma kara da yin kira ga Majalisar Tarayya da ta gaggauta amincewa da shi.
"A kara yawan mata a majalisa," Remi Tinubu
The Nation ta ruwaito cewa Uwargidan Shugaban Kasa, wacce Hajiya Fatima Tajudeen Abbas, matar Kakakin Majalisar Wakilai, ta wakilta ta nanata goyon bayanta ga kudirin a wani taro a Abuja.
Ta ce:
"Ya na da matukar muhimmanci a mai da hankali kan bukatar karin wakilcin mata a matsayi na jagoranci da yanke shawarwari a kan abinda ya shafi jama'arsu.
Mata na da matukar muhimmanci a ci gaban kasarmu, amma har yanzu an takaita wakilcin jama'arsu da suke yi a wani mataki.”
Uwargidan shugaban kasar ta sake tabbatar da goyon bayanta ga kudirin, wanda ke bukatar a ware akalla 35% na kujerun majalisa da mukaman zartarwa ga mata.
Remi Tinubu: "Mata na da muhimmanci"
Sanata Remi Tinubu ta ce mata suna da matukar muhimmanci a wajen zartar da manufofin da suka shafi kasa, saboda haka bai kamata a dakile su ba.

Asali: Facebook
Ta ce:
"Saboda haka, ina goyon bayan kudirin da ke bukatar a ware akalla 35% na kujerun majalisa da mukaman zartarwa ga mata.
Ina kuma kira ga Majalisar Tarayya da ta gaggauta amincewa da wannan kudiri. Ni a shirye nake na mara baya ga duk wata manufa da za ta inganta wakilcin mata da gina kasa.”
An yi takaicin karancin mata a shugabanci
A nasa bangaren, Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu, wanda ke jagorantar kudirin, ya nuna damuwa kan yadda mata ke fuskantar karancin wakilci a shugabanci.
Kudirin na da nufin gyara kundin tsarin mulkin 1999 domin ware kujeru na musamman ga mata a majalisun dokokin jihohi da na kasa baki daya.
Ministar Harkokin Mata, Hajiya Imman Suleiman, tare da wasu manyan baki, sun bayyana cikakken goyon bayansu ga wannan kudiri tare da bukatar a amince da shi cikin gaggawa.
Remi Tinubu ta yi rabon kudi a Arewa
A wani labarin, kun ji cewa Uwargidan Shugaban Kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta kaddamar da rabon tallafin Naira miliyan 50 ga tsofaffi 250 daga jihohin Nasarawa da Gombe.
A jihar Nasarawa, an gudanar da taron rabon tallafin a birnin Lafia, inda aka kara yawan kudin tallafin daga N100,000 zuwa N200,000 domin kara rage radadin matsin tattalin arziki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng