Bayan Dakatarwa, Majalisa Ta Dauki Wasu Matakan Ladabtarwa 5 kan Sanata Natasha
- Majalisar dattawa ta nemi sanatar mazabar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan ta rubuta takardar neman afuwa saboda raina majalisa
- Kwamitin ladabtarwa na majalisar ya samu Natasha da laifin karya dokokin majalisar da kuma yi wa Sanata Godswill Akpabio rashin kunya
- A zaman majalisar na yau, kwamitin ya zayyana matakan ladabtarwa da za a dauka kan sanatar, ciki har da dakatar da ita na watanni shida
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Majalisar dattawan Najeriya ta bukaci Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta rubuta takardar neman afuwa kan zargin da ta yi wa shugaban majalisar, Godswill Akpabio.
Shugaban kwamitin da’a da korafe-korafe na majalisar, Sanata Neda Imasuen, ne ya bayyana hakan yayin zaman majalisar a ranar Alhamis.

Asali: Twitter
Majalisa ta dauki matakan ladabtar da Natasha
Majalisar ta kuma yi watsi da ikirarin Akpoti-Uduaghan cewa ana hana ta yin magana a zauren majalisa, inda ta kira zargin da 'marar tushe' inji rahoton The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A yayin zaman majalisar na yau Alhamis, 6 ga watan Maris, 2025, majalisar ta dauki matakan labadartawa 6 a kan Sanata Natasha, kamar haka:
1. An dakatar da Natasha na watanni 6
Kwamitin majalisar ya bada shawarar dakatar da Sanata Natasha daga dukkan harkokin majalisa na tsawon watanni shida daga ranar 6 ga Maris, 2025.
2. An rufe ofishin Natasha da kwace kadarori
Haka nan, majalisar ta bukaci a kulle ofishin Sanata Natasha tare da kwace duk wasu kayayyakin majalisa da ke hannunta har sai bayan karewar wa'adin dakatarwar.
3. An hana Natasha zuwa kusa da majalisa
A cikin lokacin dakatarwar, ba a yarda Sanata Natasha ko ma’aikatanta su shiga harabar majalisar tarayya ko gabatowa kusa da ita ba.
4. An dakatar da alawus da albashin Natasha
Kwamitin ya kuma ba da shawarar dakatar da albashin Sanata Natasha da duk wasu alawus da na hadimanta har na tsawon watanni shida.
5. An janye jami'an tsaron Sanatar
Hakazalika, majalisar ta bukaci a janye dukkanin wasu jami'an tsaron da ke gadin 'yar majalisar dattawan, har zuwa lokacin da dakatarwar zai kare.
6. An hana Natasha wakiltar majalisa a ko ina
An kuma haramtawa Sanata Natasha gabatar da kanta a matsayin wakiliyar majalisar dattawa a cikin gida Najeriya ko a ƙetare har sai bayan wa’adin dakatarwar.
Me ya jawo majalisa ta dauki matakan?
Rahoton Punch ya nuna cewa an dauki wannan mataki ne bayan wata takaddama da ta barke tsakanin Natasha da Akpabio kan sauya mata wurin zama a zauren majalisa.
Sanatar ta zo zaman majalisar ne a makon da ya gabata, sai ta tarar da an cire sunanta daga wurin da take zama ba tare da sanarwa ba.
Bayan hakan, Sanata Natasha ta yi zargin cewa Akpabio ya yi korin cin zarafinta ta hanyar hana ta yin magana da kuma sauya mata wurin zama.
Wasa wasa dai har sai dai rikicin ya kai matsayin da Natasha ta zargi Akpabio da nemanta da lalata a lokuta mabanbanta, zargin da shugaban majalisar dattawan ya karyata.
Majalisa ta yi watsi da korafin Sanata Natasha
A wani labarin, mun ruwaito cewa, kwamitin ladabtarwa na majalisar dattawa ya ki karbar bukatar Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan na watsa zaman tuhumarta kai tsaye a talabijin.
Shugaban kwamitin, Sanata Neda Imasuen, ya ce majalisar ba za ta watsa tuhumar kai tsaye ba domin gudun hayaniya amma za a ba 'yar majalisar damar kare kanta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng