"Ku Shirya": Hukumar NSCDC Za Ta Dauki Sababbin Ma'aikata, Ta Sa Lokaci

"Ku Shirya": Hukumar NSCDC Za Ta Dauki Sababbin Ma'aikata, Ta Sa Lokaci

  • Hukumar tsaro ta NSCDC ta shirya ɗaukar sababbin ma'aikata domin ƙara bunƙasa ayyukanta na tsaron gida
  • Shugaban hukumar na ƙasa, Ahmed Audi, ya bayyana cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince a ɗauki sababbin ma'aikatan
  • Ahmed Audi ya nuna cewa za a ɗauki ƴan Najeriya masu halaye na gari domin su yi aiki a hukumar tsaron da aka kafa a 2003
  • Shugaban na NSCDC ya bayyana cewa nan ba da daɗewa ba za a sanar da lokacin da za a fara aikin ɗaukar sababbin ma'aikatan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban NSCDC, Ahmed Audi OFR, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta ɗauki sababbin ma'aikata da za su yi aiki a hukumar.

Shugaban na NSCDC ya bayyana cewa za a ɗauki ƴan Najeriya da suka cancanta domin aiki a hukumar nan ba da daɗewa ba.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban hukumar NIS ya mutu a dakin otel, budurwar da suke tare ta tsere

NSCDC za ta dauki sababbin ma'aikata
Hukumar NSCDC za ta dauki ma'aikata Hoto: @OfficialNSCDC
Asali: Twitter

Ya bayyana hakan ne yayin buɗe ofishin NSCDC na ƙaramar hukumar Bwari a ranar Laraba a Abuja, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya amince a ɗauki ma'aikata a NSCDC

Ahmed Audi ya ce hukumar ta samu amincewar fara ɗaukar ma’aikata, amma za a sanar da ranar fara aikin ɗaukar ma’aikatan a lokacin da ya dace.

“Muna shirin fara ɗaukar ma’aikata a hukumance, muna godiya ga shugaban ƙasa saboda amincewa a ɗauki ƴan Najeriya masu halayya ta gari aiki a cikin hukumar."

- Ahmed Audi

NSCDC ta yabawa shugaban ƙaramar hukuma

Ya yabawa majalisar ƙaramar hukumar Bwari bisa gina ofishin reshen hukumar, yana mai cewa ofishin zai taimaka wajen samar da tsaro a yankin.

A nasa jawabin, kwamandan NSCDC na babban birnin tarayya Abuja, Olusola Odumosu, ya godewa shugaban ƙaramar hukumar Bwari, Dr. John Gabaya, bisa ƙoƙarinsa na gina ofishin don jami’an hukumar.

Ya ƙara da cewa ɗaya daga cikin matsalolin da jami’an yankin ke fuskanta shi ne kula da motocin aikinsu da kuma batun man fetur, don haka ya buƙaci ƙarin tallafi.

Kara karanta wannan

Shugaban NAHCON ya sha sabon alwashi kan aikin Hajjin 2025

"Ina so na tabbatar muku cewa yanzu da muka samu wannan ofishin mai inganci don gudanar da ayyuka, za mu ƙara tura jami’ai da kayan aiki."
“Tun daga hawana ofis mun ƙirƙiri ƙarin ofisoshi guda biyu, mun ƙara wasu manyan rundunoni guda biyu, tare da kafa wuraren sa-ido da dama."
“Waɗannan matakai ne da za su taimaka wajen kusantar da mu ga al’umma, domin samun cikakkiyar fahimta kan matsalolin tsaro a matakin yankuna, tare da tsara ayyukan tsaro cikin inganci."

- Olusola Odumosu

Hukumar NSCDC ta koro jami'inta

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar tsaro ta NSCDC ta ɗauki matakin ladabtarwa kan jami'inta da aka samu da aikata ba daidai ba a jihar Zamfara.

Hukumar NSCDC ta kori jami'in ne wanda aka kama da laifin safarar makamai da miyagun ƙwayoyi ga ƴan bindiga zuwa cikin daji.

Kwamandan NSCDC na jihar Zamfara, Sani Mustapha ya yi Allah wadai da mummunar ɗabi'ar da jami'in ya nuna.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng