Talaka Zai Ci Bulus: Gwamna Ya Bude Shagunan Sayar da Abinci da Araha

Talaka Zai Ci Bulus: Gwamna Ya Bude Shagunan Sayar da Abinci da Araha

  • Gwamnatin Jihar Katsina ta kaddamar da shirin Rumbun Sauki domin rage radadin tsadar kayan abinci da ma’aikata da ‘yan fansho ke fuskanta
  • Gwamna Dikko Umaru Radda ya ce gwamnati ta ware Naira biliyan 4 domin tabbatar da nasarar shirin da kuma bunkasa tsaro da daidaiton tattali
  • Mataimakin gwamnan Katsina, Malam Faruk Lawal Jobe, ya ce shirin zai karfafa kasuwanci, samar da ayyukan yi da kuma bunkasa tattalin arziki

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - A kokarin rage radadin matsin tattalin arziki, gwamnatin jihar Katsina ta kaddamar da wani sabon shiri mai suna Rumbun Sauki.

Gwamna Dikko Umaru Radda ya ce shirin na da nufin saukaka wa ma’aikata, ‘yan fansho da sauran al’ummar jihar damar samun abinci a farashi mai sauki.

Kara karanta wannan

El Rufa'i: Kotu ta umarci ICPC ta kwato sama da N1bn da aka karkatar a Kaduna

Radda
An bude rumbun sauki a Katsina. Hoto: Ibrahim Kaula Mohammed
Asali: Facebook

A cewar sanarwar da mai magana da yawun gwamnan Katsina, Ibrahim Kaula Mohammed, ya wallafa a Facebook, shirin zai bayar da tallafin kashi 10% ga kayayyakin abinci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati ta ware N4bn domin Rumbun Sauki

Gwamna Radda ya bayyana cewa gwamnati ta fitar da Naira biliyan 4 domin tabbatar da nasarar shirin Rumbun Sauki.

Ya ce shirin zai taimakawa ma’aikata na matakin jiha da kananan hukumomi, malaman makaranta, da ‘yan fansho masu shekaru 60 zuwa sama.

Dikko Radda ya ce shirin zai tabbatar da adalci da kaucewa babakere ta hanyar kafa tsari na bin doka da oda wajen raba kayan tallafin.

Za a fara raba tallafin a manyan birane

A cewar gwamnan, za a fara raba kayayyakin tallafin ne a manyan yankunan jihar guda uku, Katsina, Daura da Funtua.

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati na da shirin fadada shirin zuwa dukkan kananan hukumomi 34 na jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Neman lalata: Majalisa ta yi watsi da bukatar Natasha kan zargin Akpabio

Ya bukaci wadanda za su amfana da shirin da su bi ka’idojin da aka shimfida domin dorewar shirin.

“Wannan shiri wani bangare ne na kokarin gwamnati wajen tabbatar da tsaro, samar da wadatar abinci da kuma inganta rayuwar al’umma,”

- Gwamna Dikko Radda

Shirin zai jawo daidaita farashin abinci

Mataimakin gwamnan Katsina, Malam Faruk Lawal Jobe, ya ce shirin ba wai kawai rage radadin matsin tattalin arziki zai yi ba, zai kuma bunkasa harkokin kasuwanci.

Ya bayyana cewa ‘yan kasuwa da ke cikin shirin za su samu damar yin ciniki da kimanin Naira biliyan 30 duk shekara.

Faruk Lawal Jobe ya ce shirin zai taimaka wajen daidaita farashin kayayyakin abinci a kasuwanni domin hana hauhawar farashi.

Haka nan ya yabawa Gwamna Radda kan kokarinsa na ciyar da tattalin arzikin Katsina gaba da samar da manufofin tallafawa jama’a.

Gwamna Radda
Gwamna Radda na ba matasa tallafi. Hoto: Ibrahim Kaulaha Mohammed
Asali: Facebook

Yadda za a rika biyan kudin abinci

Kara karanta wannan

Yadda Biden da Amurka su ka matsawa Najeriya lamba, aka saki jami'in Binance

Mai bai wa gwamnan Katsina shawara kan tattalin arzikin karkara, Yakubu Nuhu Danja, ya ce shirin zai fadada zuwa wadanda ba ma’aikata ba, musamman masu shekaru 60 zuwa sama.

Ya ce ana iya karbar kayan tallafin tare da biyansu kai tsaye ko kuma a rika cire kudin daga albashin mutum ba tare da riba ba.

Danja ya bayyana cewa hakan zai baiwa jama’a damar cin gajiyar shirin ba tare da matsin lamba ba.

Jihohin da ake raba raba abincin azumi

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnoni a jihohi daban daban da suka hada da Kano sun kaddamar da shirin ciyar da masu azumi.

A kullum ana dafa abinci a jihohin domin a rika ba mutane su yi buda baki a kan tsare tsare da aka gindaya domin kaucewa tarzoma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel