Waiwaye: Sanata Ya Tono Sirri a Baya da Natasha Ke Zargin Tsohon Gwamna da Cin Zarafi
- Sanata da ke wakiltar Ekiti ta Arewa ya bankado abin da Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi wa tsohon gwamnan jiharsa, Kayode Fayemi
- Bayan ta shigar da korafi kan Shugaban Majalisa, Godswill Akpabio, Sanata Cyril Fasuyi ya ce Natasha ta taba zargin Fayemi da cin zarafi
- Fasuyi ya ce tsohon ministan ma zai shigar da nasa korafin a majalisa, yayin da bidiyon zarge-zargen Akpoti-Uduaghan ya kara tayar da kura
- Rikicin ya haddasa hatsaniya a majalisa, yayin da sanatocin adawa suka yi kokarin dakatar da Fasuyi, sai dai Akpabio ya bar shi ya ci gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Sanata Cyril Fasuyi, mai wakiltar Ekiti ta Arewa, ya tono wani sirri da ya shafi Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.
Sanata Fasuyi ya ce Natasha ta taba zargin tsohon gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi da cin zarafi.

Asali: Facebook
Wane zargi Natasha ke yi wa Akpabio?
Fasuyi ya yi wannan ikirari ne jim kadan bayan Akpoti-Uduaghan ta shigar da korafi kan Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, cewar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rikicin ya biyo bayan wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, inda Akpoti-Uduaghan ta zargi Akpabio da cin zarafi.
Natasha ta ci gaba da cewa kin amincewa da ta yi ga bukatun Akpabio ya kara jefa ta cikin matsala saboda rashin ba kudurorinta dama a majalisar.
Sai dai Akpabio ya musanta wannan zargi da Natasha ke yi masa, ya ce mahaifiyarsa ta ba shi tarbiyya tun yana karamin yaro.
Shugaban majalisar ya bayyana haka ne a yau Laraba 5 ga watan Maris, 2025 yayin da Natasha ke gabatar da korafi a gaban majalisar.

Asali: Twitter
Yadda aka bankado Natasha ta zargi tsohon gwamna
Fayemi, tsohon gwamnan Jihar Ekiti, ya rike mukamin Ministan Ma’adanai a zangon mulkin farko na tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan
Daga ƙarshe, an ji ta bakin shugaban Majalisa kan zargin neman lalata da Sanata Natasha
Fasuyi ya yi wannan magana ne yayin da sanatocin APC ke kokarin hana Akpoti-Uduaghan shigar da korafi, suna kafa hujja da wata doka ta majalisa.
Ya kuma ce Fayemi zai shigar da nasa korafin a gaban majalisa domin kare kansa daga zargin da aka yi masa.
A yayin jawabinsa, sanatocin PDP sun yi kokarin dakile Fasuyi daga magana, amma hakan bai hana ci gaba da zaman ba.
Akpoti-Uduaghan, a fusace, ta mike tana cewa:
"Ana yanke mani hukunci ba tare da adalci ba."
Zaman majalisar ya kaure da hayaniya na dan lokaci, kafin Akpabio ya yanke hukunci cewa za a ci gaba da sauraron korafin Akpoti-Uduaghan.
Kotu ta dakile shirin majalisa kan Natasha
A baya, kun ji cewa Kotu ta shiga dambarwar da ke faruwa tsakanin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da Godswill Akpabio.
Kotun ta dakatar da Kwamitin Majalisar Dattawa daga bincikar Natasha Akpoti-Uduaghan kan batun daukar mataki kanta.
Wannan hukunci ya hana kwamitin ci gaba da shirin dakatar da Sanatar har sai an sake duba shari'ar da ke gabanta, ta nemi binciken da za a yi mata ya kasance a bude.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng