Daga Karshe, an Ji Ta Bakin Shugaban Majaliss kan Zargin Neman Lalata da Sanata Natasha
- Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godwill Akpabio ya bayyana cewa tun da ya taso a rayuwarsa, bai taɓa cin zarafin mace ba
- Akpabio ya musanta zargin neman lalata da Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, ya ce mahaifiyarsa ta ɗora shi a tarbiyya mai kyau
- Ya yi wannan bayani ne a zaman Majalisa na yau Laraba da Natasha Akpoti-Uduaghan ta miƙa korafi kan zargin da take yi masa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya musanta zargin cin zarafi ko neman lalata da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi masa.
Sanata Akpabio ya yi wannan bayani ne a zaman Majalisar na yau Laraba, 5 ga watan Maris, 2025 a Abuja bayan dawowa daga hutun sati guda.

Asali: Twitter
Akpabio ya bayyana cewa babu a wani lokaci ba ya taɓa cin zarafin wata mace ko ya nemi lalata da ita, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan
Waiwaye: Sanata ya tono sirri a baya da Natasha ke zargin tsohon gwamna da cin zarafi
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban Majalisar Dattawa ya yi bayani
Da yake watsi da zargin da sanata take yi masa, Godswill Akpabio ya ce:
"Ban taɓa cin zarafin mace ba, na taso kan tarbiyya ta gari wacce mahaifiya ta ɗora ni a kai, ita kaɗai ta raineni, ta koya mani girmama mata.
"A dalilin haka ne ma aka ba ni lambar yabo a matsayin gwamnan da ya fi goyon bayan mata a Najeriya."
Shugaban Majalisar ya bayyana cewa tun ranar 25 ga Fabrairu ya fara karɓar kira daga mutane da dama dangane da zargin da aka yi masa, kuma yana sane da yadda lamarin ke yaduwa a kafafen sada zumunta.
Sai dai ya bukaci ‘yan Najeriya da kafafen yada labarai da su guji yanke hukunci gabanin kotu ta saurari ƙorafin.
Sanata Natasha ta mika takardar ƙorafi
Bayan jawabin Akpabio, Sanata Akpoti-Uduaghan ta gabatar da ƙorafi bisa dokar Majalisa ta 40, tana zargin Shugaban Majalisar da cin zarafinta ta hanyar neman kwanciya da ita.

Kara karanta wannan
Zargin 'neman lalata' ya ƙara girma, Sanata Natasha ta gabatar da takarda a Majalisa
Ta ce Akpabio yana amfani da ofishinsa wajen muzanta mata, sannan ta nemi izinin tashi zuwa gaba domin miƙa ƙorafin a gaban majalisar wanda kuma aka ba ta dama.
Wannan batu ya samo asali ne tun a watan Fabrairu, lokacin da wata matsala ta taso dangane da canza wurin zama a majalisa.
Lamarin dai ya haddasa musayar yawu mai zafi tsakanin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da Akpabio, rahoton Daily Trust.
Batun ya ƙara tsananta har ya kai ga Sanatar mai wakiltar Kogi ta Tsakiya ta yi ikirarin Akpabio ya nemi lalata da ita.

Asali: Original
Abin da ya faru a zaman Majalisar dattawa
A yayin zaman majalisar na ranar Laraba, Sanata Akpoti-Uduaghan ta iso zauren majalisar tare da mijinta, lamarin da ya janyo hankulan mutane.
A gaban jama’a, ta sumbaci mijinta gabanin shiga zauren majalisa don ta zauna a sabon kujerarta.
Sai dai abin da ya fi jan hankali shi ne yadda ta ƙi tashi tsaye lokacin da Shugaban Majalisar, Akpabio, ya shigo don fara zaman majalisar wanda ya saba da al’ada.
Bayan ya zauna, Sanata Akpabio ya musanta zargin neman Natasha da lalata, ya ce ba haka tarbiyyar gidansu take ba.
Ƴan Arewa sun nemi Akpabio ya yi murabus
A wani labarin, kun ji cewa ƙungiyar 'yan siyasar Arewa (LND) ta yi magana kan dambarwar da ke faruwa game da zargin lalata da ake yi wa Godswill Akpabio.
LND ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan Kano, Mallam Ibrahim Shekarau ta nemi shugaban Majalissr Dattawa ya yi murabus.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng