Natasha: 'Yan Sanda Sun Tarwatsa Masu Zanga Zanga, Sun Harba Barkonon Tsohuwa
- ‘Yan sanda sun harba borkonon tsohuwa domin tarwatsa magoya bayan Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan a gaban majalisar tarayya
- Legit Hausa ta rahoto cewa dandazon matasa ne suka yiwa majalisar tarayya kawanya, suna neman Godswill Akpabio ya yi murabus
- Zanga zangar ta biyo bayan zargin da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi na cewa shugaban majalisar dattawa ya neme ta da lalata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - 'Yan sanda sun harba barkonon tsohuwa don hana magoya bayan Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan shiga harabar majalisar dokoki ta ƙasa a ranar Laraba.
Mun rahoto cewa zanga zanga ta ɓarke a majalisar tarayya, biyo bayan zarge-zargen da Natasha ta yi wa shugaban majalisar dattawa.

Asali: Facebook
'Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga
Rahoton The Cable ya nuna cewa masu zanga-zangar sun hallara a kofar majalisar tun da misalin karfe 8:00 na safe yayin da ake shirin fara zaman majalisar.

Kara karanta wannan
Sojoji da ‘yan ta’adda sun gwabza bayan harin ofishin ‘yan sanda, an samu asarar rayuka
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matasan suna rike da kwalaye masu rubuce-rubuce kamar: ‘Dole ne Akpabio ya sauka’, ‘Kare hakkin mata’, da ‘Kare Natasha ko ta halin ƙaƙa’.
Rahotanni sun nuna cewa an jibge jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda, NSCDC da sojoji a wurin domin hana tashin hankali.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa 'yan sanda ba su wani ɓata lokaci ba suka harba hayaƙi mai sanya hawaye domin tarwatsa masu zanga-zangar.
Wakilin jaridar da ya halarci inda ake zanga-zangar ya ruwaito cewa masu zanga-zangar sun tsere daga wurin bayan hayaƙin ya bazu ko ina.
Bayan tarwatsa su, an ce masu zanga-zangar sun koma bangaren Unity Fountain domin ci gaba da nuna adawarsu kan zargin cin zarafin Natasha.
Abin da ya jawo zanga zanga a majalisar tarayya

Asali: Twitter
Idan ba a manta ba, Sanata Natasha, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, ta samu sabani da shugaban majalisa, Godswill Akpabio, kan wurin zama a ranar 20 ga Fabrairu.

Kara karanta wannan
Daga ƙarshe, an ji ta bakin shugaban Majalisa kan zargin neman lalata da Sanata Natasha
Sanata Natasha ta bijirewa umarnin Akpabio na canja wurin zamanta, inda a nan take ta zarge shi da nuna mata wariya a cikin majalisar.
Maganganun da ta yi, ya sa majalisar ta mika lamarinta ga kwamitin ladabtarwa, inda ita kuma ta shigar da kara kan Akpabio, tana neman diyyar N100bn.
Rigimar ta ɗauki zafi ne yayin da a ranar Juma’ar da ta gabata, Natasha ta shiga gidan talabijin, ta zargi Akpabio da nemanta da lalata, wanda taki amincewa.
Natasha da matar Akpabio sun yi cacar-baki
Sai dai Akpabio ya fito ya musanta zargin ta ta hannun mai magana da yawunsa, Kenny Okulogbo.
Hakazalika, matar shugaban majalisar, Ekaette Akpabio, ta fito ta gargadi Natasha akan ta fita daga harkar mijinta, "domin shi ba mutumin banza ba ne."
Ita ma Sanata Natasha, ta yi wa matar Akpabio martani, ta gargade ta a kan shiga abin da bai shafe ta ba, kamar yadda muka ruwaito.

Kara karanta wannan
Zargin 'neman lalata' ya ƙara girma, Sanata Natasha ta gabatar da takarda a Majalisa
A yanzu haka dai, ana jiran Sanata Akpoti-Uduaghan ta gurfanar gaban kwamitin ladabtarwa na majalisar da karfe 2 na yammacin yau domin kare kanta.
Kotu ta hana a tuhumi Sanata Natasha
A wani labarin, mun ruwaito cewa, kotu ta dakatar da kwamitin majalisar dattawa daga bincikar Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, har sai an gama shari'arta.
Yayin da ake jiran matakin da majalisa za ta dauka kan hukuncin kotun, Sanata Natasha ta bukaci a gudanar da binciken a bude, ta yadda 'yan Najeriya za su ga abin da ke faruwa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng