Badakalar N33.8bn: Shaidan EFCC Ya Kwarewa Ministan Buhari Baya a gaban Kotu

Badakalar N33.8bn: Shaidan EFCC Ya Kwarewa Ministan Buhari Baya a gaban Kotu

  • Hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya, ta ci gaba da gabatar da shaidu a ƙarar da ta shigar da Saleh Mamman
  • Shaidan da hukumar ta gabatar ya bayyana yadda tsohon ministan lantarkin ya siya gidan N200m da daloli a birnin tarayya Abuja
  • Tsohon ministan na gwamnatin Muhammadu Buhari yana fuskantar tuhuma guda 12 kan almundahanar N33.8bn a kotun tarayya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, ta ci gaba da sauraron ƙarar tsohon ministan lantarki a gwamnatin Muhammadu Buhari, Saleh Mamman.

Kotun ta saurari yadda akae zargin Saleh Mamman, ya sayi wata kadarar da ta kai Naira miliyan 200 a Abuja ta hanyar biyan kuɗin da tsabar daloli.

EFCC ta kai karar Saleh Mamman
Shaidan EFCC ya fallasa Saleh Mamman Hoto: EFCC Nigeria
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta ce Saleh Mamman yana fuskantar tuhuma 12 da suka shafi haɗa baki da kuma almundahanar kuɗaɗe da suka kai kimanin Naira biliyan 33.8.

Kara karanta wannan

Yadda Biden da Amurka su ka matsawa Najeriya lamba, aka saki jami'in Binance

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

EFCC ta gabatar da shaida kan ministan Buhari

A ci gaba da shari’ar, shaidan da EFCC ta gabatar na 12, Mr Samson Bitrus, ya shaidawa kotu cewa shi dillalin gidaje ne kuma shi ne ya taimakawa wanda ake tuhuma wajen sayen gidan da ke lamba 12, titin Lungi a Wuse 2, Abuja.

Lauyan masu shigar da ƙara, Mista Rotimi Oyedepo (SAN), ya jagoranci Samson Bitrus wajen bada shaida.

Samson wanda ya bayyana sunan kamfaninsa a matsayin Tekma Grand Advantage Limited, ya ce an gabatar da shi ga wanda ake tuhuma ta hannun wani abokin kasuwancinsa, Alhaji Mustapha Dan Daura.

Ya bayyanawa kotu cewa tsohon ministan ya buƙaci ya nemo masa wani gida tun a shekarar 2019, tare da tabbatar da cewa kadarar ba ta da wata matsala ta doka.

"Bayan bincike, mun haɗu da mai gidan kuma mun kammala ciniki ta hanyar biyan kuɗin siyan gidan. Gidan yana a lamba 12, titin Lungi, Wuse 2."

Kara karanta wannan

"Lambarsa ta fito": Hukumar EFCC ta cafke tsohon gwamna kan badakalar N700bn

"Sunan mai sayar da gidan Jidda. Lokacin da muka je wurinsa, tsohon ministan ya zo tare da abokinsa, wanda ina tunanin sunansa Mohammed Hussein."
“Kuɗin siyan gidan ya kai naira miliyan 200, kuma wanda ake tuhuma ya biya da daloli. Mai gidan ya karbi kudin kuma ya ƙirga don tabbatar da cewa sun cika."

- Samson Bitrus

Me lauyan Saleh Mamman ya ce?

A yayin zaman, lauyan wanda ake tuhuma, Mista Femi Atteh (SAN), ya nemi kotu ta dage shari’ar domin ba shi damar yi wa shaidan tambayoyi sosai.

Tun da farko a zaman shari’ar, wani mai canjin kuɗi, Maina Goje, wanda aka fassara shaidarsa daga Hausa zuwa Turanci, ya bayyana cewa yana kai wa tsohon ministan kuɗi zuwa gidansa da ke Abuja.

Sai dai ya amince cewa wanda ake tuhuma bai taɓa karbar kuɗin kai tsaye daga hannunsa ba, sai dai ta hannun matasan da ke zaune a gidansa.

EFCC ta cafke tsohon gwamnan Akwa Ibom

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ta cafke tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel.

Kara karanta wannan

Ana neman Turji, wani ɗan bindiga da yaransa sun ba da mamaki, sun mika wuya

Hukumar EFCC ta cafke tsohon gwamnan ne kan zargin badaƙalar N700bn bayan an shigar da ƙorafi a kansa a gabanta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng