Ana Fama da Tsadar Rayuwa, Gwamna a Arewa Zai Fara Tatsar Haraji daga Masu Gidaje
- Gwamnatin Kogi ta fara karɓar harajin fili daga masu gidaje da shaguna, ana buƙatar masu filaye su biya harajin don ci gaban jihar
- Shugaban KGIRS, Alhaji Sule Enehe, ya ce harajin zai ƙara kuɗin shiga, inganta tattalin arziki tare da samar da sababbin ayyukan yi a Kogi
- Gwamnati ta ce gine-ginen gwamnati, wuraren ibada, makarantu, asibitoci, da kadarorin sarakuna ba su cikin waɗanda za su biya harajin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kogi - Gwamnatin jihar Kogi ta fara karɓar harajin Ground Rent daga masu gidaje, shaguna da kadarori a matsayin wani ɓangare na haraji da ake tattarawa a jihar.
Legit Hausa ta fahimci cewa Ground Rent, wani haraji da ne da gwamnatocin jihohi ke karba daga wadanda ta ba takardar mallakar fili (CofO).

Asali: Facebook
Masu kadarori a Kogi za su fara biyan haraji
A dokar kasa ta amfani da fili ta 1978 (da aka sabunta), ta nuna cewa gwamnati ce ke da mallakin duk wani fili na jiharta, don haka za ta iya karbar harajin, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Punch ta rahoto cewa shugaban hukumar tattara haraji ta Kogi (KGIRS), Alhaji Sule Enehe, ya sanar da fara karbar harajin a taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki a Lokoja.
Alhaji Sule ya ce dokar amfani da fili ta 2024, a jihar, ta tanadi haɗa duk kuɗin shiga cikin tsari guda don ƙara inganta tattalin arzikin ƙananan hukumomi.
Shugaban KGIRS ya bayyana cewa harajin filin zai inganta tattara bayanai, ƙarfafa cigaban birane, da samar da sababbin ayyukan yi a jihar Kogi.
Gwamnati ta fadi amfanin biyan harajin GR
Alhaji Sule ya ce dokar za ta taimaka wajen sauƙaƙe tsarin haraji, tabbatar da gaskiya, da tabbatar da cewa kowa yana bada gudunmawarsa wajen ci gaban jihar.

Kara karanta wannan
Zamfara: 'Yan bindiga sun sace shugabannin APC a kan hanyarsu ta zuwa gidan Sanata
"Idan aka aiwatar da wannan doka yadda ya kamata, za ta kawo babbar riba ga ƙananan hukumomi da jihar baki ɗaya,"
- in ji Alhaji Sule.
Ya bayyana cewa, tun da farko KGIRS na karbar harajin kadarorin da aka riga aka gina kuma ake amfanid a su (TR), amma ba a tilasta biyan harajin amfani da fili ba sai yanzu.
Shugaban KGIRS ya ce an fara aiwatar da dokar tun bara, amma yanzu za a tabbatar da karbar kudin, yana mai cewa akwai bukatar kowa ya fahimci tsarin kafin masu karɓar haraji su isa ƙananan hukumomi.
Alhaji Sule ya bukaci shugabannin ƙananan hukumomin jihar Kogi su ba da haɗin kai don tabbatar da nasarar aiwatar da dokar a faɗin jihar.
An lissafa wadanda ba za su biya harajin ba

Asali: Twitter
Shugaban kamfanin New Wave Echo System, Mista Femi Williams, ya ce dokar ta dade tana samar da kuɗin shiga a wasu jihohin Najeriya.
Mista Femi ya ce gwamnati ba za ta karbi harajin a kan gine-ginen gwamnati, wuraren ibada, asibitoci, makarantu, da kadarorin da sarakuna ke amfani da su don aiki ba.
Shugabannin ƙananan hukumomin Olamaboro da Lokoja sun tabbatar da cewa dukkan ciyamomin ƙananan hukumomi 21 za su goyi bayan aiwatar da dokar.
Sun bayyana cewa aiwatar da dokar zai taimaka wajen bunƙasa ci gaban ƙananan hukumomi da kuma inganta tattalin arzikin jihar Kogi.
Gwamnati za ta tatsi haraji daga gidajen haya
A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan Najeriya za su fara biyan haraji kan gidajen haya da takardun filaye na CofO, bisa sabon tsari da hukumar FIRS ta kaddamar.
Hukumar FIRS, wacce ke da alhakin karɓar haraji a Najeriya, ta bayyana cewa za a fara tatsar haraji daga masu gidaje da masu takardun filaye don inganta hanyoyin kudin shiga.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng