Gwamnati za ta rika tatsar haraji daga gidajen haya da takardun filaye

Gwamnati za ta rika tatsar haraji daga gidajen haya da takardun filaye

Mutane za su fara biyan kudin haraji a kan gidaje haya da kuma takardun filaye na CofO a Najeriya. Wannan ya na cikin wani sabon tsari da hukumar FIRS ta shigo da shi a kasar.

Hukumar FIRS mai karbar haraji a Najeriya ta ce za a rika tatsar kudin shiga daga hannun masu gidajen da takardun filaye. Jaridar Daily Trust ta fitar da wannan rahoto.

Mai magana da yawun bakin hikumar FIRS, Abdullahi Ahmad, ya bayyana wannan a wani jawabi da ya fitar a ranar Alhamis, 2 ga watan Yuli, 2020.

FIRS ta bukaci mutane su ajiye takardun yarjejeniyar karbar hayar gidaje ko ofisoshi da shagunansu da kuma na mallakar filaye domin a rika karbar harajin hatimi a kansu.

Abdullahi Ahmad ya yi wannan jawabi ne jiya a babban birnin tarayya Abuja a madadin hukumar.

KU KARANTA: NYSC ta ba Gwamna Obaseki sabuwar takardar shaida

Gwamnati za ta rika tatsar haraji daga gidajen haya da takardun filaye
Ofishin hukumar FIRS
Asali: UGC

Kakakin hukumar harajin kasar ya ce gwamnati za ta soma cire wannan haraji na hatimi har daga cikin sauran kasuwancin da mutane su ke yi na yau da kullum.

Daga yanzu gwamnati za ta rika samun kudin shiga da takardun filaye watau C of O, da takardar yarjejeniya ta MoU, JVA, da takardun jingina kamar yadda jami’in hukumar ya bayyana.

A cewar hukumar, gwamnatin tarayya ce ta shigo da wannan tsari. Bisa dukkan alamu wannan ya na cikin dabarun gwamnatin Najeriya na samun kudin shiga domin aiwatar da ayyuka.

Jaridar Premium Times ta ce gwamnati ta samu Naira biliyan 66 a cikin watanni biyar da bullo da wannan tsari. Kawo yanzu hukumar ba ta bayyana yadda za a rika karbar wannan haraji ba.

A sabuwar dokar tattalin arziki na 2019 wanda aka yi wa garambawul, akwai na’uka biyu na harajin hatimi da hukumar FIRS za ta rika karba a madadin gwamnatin Najeriya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel