"Ku Bi a Hankali," Omokri Ya Bukaci CAN Ta Guji Shari’a da Jihohi kan Hutun Ramadan
- Tsohon hadimin shugaban ƙasa, Reno Omokri, ya maida martani kan barazanar da CAN ta yi wa jihohin Arewa saboda hutun makarantu
- Fasto Omokri ya ce babu dalilin tayar da hankali kan batun, duba da yadda Musulmi ke hakuri da hutun da ke fifita Kiristoci a ƙasar nan
- Ya shawarci CAN kan hanyoyin da ya dace ta bi, matuƙar dole ne ta yi korafi game da hutun da aka bayar a wasu jihohi saboda azumi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Tsohon hadimin shugaban ƙasa, Reno Omokri, ya bukaci Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) da kada ta nemi fara shari’a kan rufe makarantu na ɗan lokaci a wasu jihohin Arewacin Najeriya.
CAN ta soki matakin da jihohin Kano, Katsina, Kebbi da Bauchi suka ɗauka na rufe makarantu har na tsawon makonni biyar domin bai wa dalibai damar gudanar da azumin Ramadana a gida.

Kara karanta wannan
Bola Tinubu ya ware sama da Naira biliyan 700 a watan azumi, za a yi muhimman ayyuka

Asali: Twitter
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Mista Omokri ya ce hakan na iya janyo ramuwar gayya daga ƙungiyoyin Musulmi a nan gaba idan aka rufe makarantu saboda bukukuwan Kiristoci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Reno Omokri ya jero hutun makarantun Najeriya
Tsohon mai ba da shawara na shugaban ƙasa ya bayyana cewa makarantu a Najeriya suna hutun Kirsimeti, hutun Easter, da hutun sabuwar shekara, wanda duk ya fi alaka da Kiristanci.
Ya ce tsarin shekarar karatu a Najeriya yana daidaita ne da irin tsarin addinin Kiristanci na Birtaniya, amma Musulmi suna hakuri da hakan ba tare da korafi ba.
Ya ce:
"A Najeriya, daga Litinin zuwa Juma’a rana ce ta aiki da karatu, abin da ke amfanar addinin Kiristanci, amma Musulmi suna bin wannan tsari.
A duk faɗin duniya ta Musulunci, Juma’a rana ce ta hutu daga aiki da karatu, yayin da Lahadi rana ce ta aiki da karatu. Amma a Najeriya, akasin hakan ne ke faruwa."
"Wannan ba shi da wata alaƙa da al’adar Najeriya kafin zuwan Turawa. Wannan tsarin addinin Kiristanci irin na Turawan Yamma ne, wanda ‘yan’uwanmu Musulmi suka yarda da shi a matsayin sadaukarwa domin zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya."
Omokri ya shawarci kungiyar CAN
Reno Omokri ya ce zai fi dacewa Kiristoci su sassauta matsayarsu a kan wannan batu, domin jihohin Arewacin Najeriya da su ka bayar da hutun na da rinjayen Musulmi.

Asali: Twitter
Ya ba da shawarar a sake tsara jadawalin makarantu domin ya dace da al’ada da al’ummomin yankuna daban-daban na kasar nan.
Ya ce:
"Ko da za a ce Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) dole ne ta shiga cikin lamarin, to ya fi dacewa ta yi hakan ta hanyar lallashi, ba tare da barazanar ɗaukar matakin doka ba. Barazana irin wannan halayya ce da ta fi dacewa da kungiyar MURIC."
"Ina mai tunatar da mu cewa waɗannan jihohi suna da ‘yancin doka a kan hakan, domin ilimi na firamare, sakandare, da manyan makarantu yana cikin jerin lamuran da doka ta ba jihohi da tarayya damar gudanarwa a kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da aka yi wa gyara."
"Kuma, me muka yi a matsayinmu na Kiristoci a lokacin da aka rufe makarantun firamare, sakandare da jami’o’i a wasu yankuna na ƙasar har na ranakun Litinin 54 a kowace shekara?"
Hutun Ramadan: Kungiyar CAN ta dauki zafi
A wani labarin, mun wallafa cewa Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta bai wa gwamnatocin jihohin Bauchi, Katsina, Kano da Kebbi wa’adin janye matakin rufe makarantu da Ramadan.
Shugaban CAN, Daniel Okoh, ya soki matakin yana mai cewa hakan zai ƙara dagula matsalar ilimi, musamman a jihohin da ke fama da yawan yara da ba sa zuwa makaranta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng