Akpabio da Shugabanni da Jami’ai 3 da Aka Taba da Tuhuma da Cin Zarafin Mata

Akpabio da Shugabanni da Jami’ai 3 da Aka Taba da Tuhuma da Cin Zarafin Mata

A tsawon shekaru, mata da dama a Najeriya sun fito fili suna zargin jami’an gwamnati da cin zarafinsu ko nemansu da lalata a lokuta mabanbanta.

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Zargi
Mata akalla hudu ne suka fito bainar jama'a wajen zargin manyan jami'ai da cin zarafi a Najeriya Hoto: Godswill Obot Akpabio/Natasha H Akpoti/@Samikon4nass
Source: Facebook

Legit ta yi waiwaye a kan korafe-korafen wasu daga cikin matan dake zargin manyan jami'ai da cin zarafinsu ta cikin wannan rahoto.

1. An zargi 'yan majalisa 3 da cin zarafi

A watan Yuni 2016, jakadan Amurka a Najeriya, James Entwistle, ya zargi 'yan majalisar wakilai, Samuel Ikon, Mohammed Garba Gololo da Mark Terseer Gbillahda yunkurin fyade da cin zarafin wata baiwar Allah.

Majalisa
An zargi tsohon dan majalisa da cin zarafi a shekarar 201 Hoto: House of Representatives
Source: Facebook

Amurka ta zargi 'yan majalisar da neman mata yayin wani taro a kan shugabanci da ya gudana Cleaveland dake Ohio a kasar.

Channels ta wallafa cewa dukkanin 'yan majalisar sun musanta zargin, tare da bayyana cewa an kitsa masu sharri, lamarin da ya kai ga barazanar zuwa kotu.

Kara karanta wannan

Dalibai sun fusata kan rufe makarantu a Arewa, NANS ta shirya zanga-zanga

Bayan bincike, kwamitin ladabtarwa na majalisar wakilai ta Najeriya ya wanke dukkanin 'yan majalisar daga zarge-zargen da aka yi masu saboda rashin isassun hujjoji.

2. Nunieh ta zargi Akpabio ta cin zarafi

A watan Yuli 2020, tsohuwar shugabar rikon kwarya ta hukumar raya yankin Neja-Delta (NDDC), Joy Nunieh, ta zargi ministan harkokin yankin, Godswill Akpabio, da cin zarafi.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Nunieh ta ce sai da ta mari Akpabio a gidansa da ke Abuja bayan ya fara yunkurin lalata da ita.

Sanata
Sanata Akpabio ya karyata zargin cin zarafi da aka yi masa har sau biyu Hoto: Godswill Obot Akpabio
Source: Facebook

Akpabio ya musanta zargin, yana mai cewa Nunieh tana da matsalar kwakwalwa, kuma tana bukatar a duba lafiyarta.

3. Cin zarafi: An zargi jami'in ma'aikatar harkokin waje

A watan Mayu 2024, wata mata mai aiki a ma’aikatar harkokin waje, Simisola Fajemirokun-Ajayi, ta zargi babban sakataren ma’aikatar, Ambasada Ibrahim Lamuwa, da yunkurin lalata da ita.

Wannan ta jawo ta shigar da kara ta hannun lauyanta, Femi Falana (SAN), inda take neman a bi mata hakkinta.

Amma Lamuwa ya musanta zargin, yana mai cewa ana kokarin bata masa suna, ana haka ne wasu mata uku suka fito da makamancin zargin.

Kara karanta wannan

Ana binciken Natasha maimakon Akpabio duk da zargin shugaban majalisa da lalata

4. Soja ta zargi babban jami'i da cin zarafinta

A watan Satumba 2024, rundunar sojin Najeriya ta sallami wata soja mai suna Ruth Ogunleye bayan ta zargi wani babban jami'i, Kanal I.B. Abdulkareem, da cin zarafi da kuma tilasta mata shan magunguna.

Ogunleye ta bayyana cewa Abdulkareem ya yi yunkurin tilasta lalata da ita, sannan ya tura ta asibitin mahaukata bayan ta ki amincewa da bukatarsa.

Bayan bincike, rundunar soji ta ce ba ta samu wata hujja da ke tabbatar da zargin nata ba, sanan an kore ta daga aiki bisa dalilin rashin lafiya tare da ba ta 50% na fanshonta.

5. Sanata Natasha ta zargi Akpabio da cin zarafinta

A 'yan kwanakin nan ne Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan ta bayyana cewa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya neme ta.

Ta ce ya nemi ta ba shi hadin kai a lokacin da ita da mai gidanta suka ziyarci gidansa da ke Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom.

Kara karanta wannan

Ramadan: Gwamna ya rufe dukkanin makarantun jiharsa na tsawon mako 5

Natasha
Natasha ta ce Sanata Akpabio ya yi alkawarin ba ta dama a majalisa matukar za ta ba shi kula wa Hoto: @NGRSenate
Source: Twitter

Natasha ta ce Akpabio ya rike hannunta tare da furta wasu kalaman da suka nuna yana son yin lalata da ita, ko da yake mijinta na tare da ita a lokacin.

Amma mai dakin Sanata Akpabio ta kare shi, tana mai cewa Natasha ta kirkiri labarin don cimma wata manufar kashin kai ne kawai.

Natasha: Majalisa ta yi biris da zargin cin zarafi

A baya, kun samu labarin cewa Majalisar Dattawan Najeriya ta ce ba za ta ɗauki wani mataki kan zargin da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi na cewa shugabanta, Godswill Akpabio, ya nemi ta ba.

Jami’in hulɗa da jama’a na majalisar, Yemi Adaramodu, ne ya bayyana hakan. Sai dai, ya ce za a binciki zargin karya dokar majalisa da ake yi wa Sanata Natasha domin ɗaukar matakin ladabtarwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng