Yadda Gwamnonin Kano da Wasu Jihohin Arewa ke Ciyar da Masu Azumin Ramadan
Wasu gwamnoni a Arewacin Najeriya sun dauki matakin ciyar da masu azumi domin rage radadin rayuwa ga al'ummominsu.
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Gwamnonin da dama a Arewacin Najeriya sun dauki matakin karya farashin abinci da ciyar da talakawa a watan Ramadan.
Gwamnonin sun bayyana cewa sun dauki matakin ne domin saukakawa talakawa da rage musu radadin rayuwa yayin da suke azumi.

Source: Facebook
A wannan rahoton, mun tattaro muku jerin gwamnonin da suka dauki matakin ciyar da mutane a watan Ramadan da yadda ake ciyar da al'umma.
1. Ana ciyar da masu azumi a jihar Kano
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa a bana, gwamnatin Abba Kabir za ta ciyar da mutane 91,000 da ke cikin mawuyacin hali a fadin jihar Kano.
Gwamnatin Kano ta ce shirin ciyarwar azumi wani bangare ne na kokarinta na rage wahalhalun da al’ummar da ke azumi ke fuskanta.

Source: Facebook
Yayin kaddamar da shirin, Mataimakin Gwamnan Kano, Aminu Abdussalam, ya bayyana cewa:
“Wannan shiri na shekara-shekara na daga cikin shirye-shiryen jin kai da gwamnatin jihar ke aiwatarwa domin rage wahalhalun da masu azumi ke fuskanta.”
Gwamnatin Jihar Kano ta tabbatar da cewa shirin ciyar da azumi na bana zai raba abinci ga mutane 91,000 a kullum, tsawon kwanaki 27 a cibiyoyi 91 da aka tanada a fadin jihar.
Domin tabbatar da nasarar shirin, gwamnati ta ce an dauki kamfanonin dafa abinci don samar da kwanon abinci 91,000 da za a rika kai wa cibiyoyin da aka tanada.
Mataimakin Gwamnan Kano da ke jagorantar shirin ya bayyana gamsuwa da yadda aka fara aiwatar da shirin cikin nasara.

Source: Facebook
A karkashin haka ya bukaci kamfanonin da ke aikin da su tabbatar da gama abinci a kan lokaci domin cimma manufar shirin.
2. Yadda ake ciyar da mutane a jihar Jigawa
Gwamnatin Jihar Jigawa ta kaddamar da shirin ciyar da al’umma a watan Ramadan, inda aka ware Naira biliyan 4 domin rabon kayan abinci ga masu bukata.
An ruwaito cewa shirin ba wai ciyarwa kawai ya tsaya ba, har ila yau an tsara shi ne ta yadda kudin akin zai zagaya a cikin al’ummar jihar domin bunkasa tattalin arziki.
Garba Muhammad ya wallafa a Facebook cewa gwamnan jihar ya bukaci masu gudanar da shirin da su yi aiki cikin gaskiya da rikon amana.
Shirin ciyar da al’umma a Ramadan ya hada da sayen kaya daga ‘yan kasuwa, jigilar kayan abinci, da samar da ayyukan yi ga masu dafa abinci da sauran masu ruwa da tsaki.

Source: Facebook
Masu sayar da kayan masarufi, itace, ruwa, kayan miya, da sauran kayan bukatu suma za su amfana da kudin da aka ware.
Ana hasashen cewa shiri zai karfafa tattalin arziki, inda kowane rukuni daga ‘yan kwangila, ‘yan kasuwa, da ma’aikatan rabon kayan za su samu riba.
3. Ana ciyar da talakawa a jihar sokoto

Kara karanta wannan
Ramadan: Tinubu ya tura sako ga Musulmi, ya yi albashir kan farashin abinci da fetur
Gwamnatin Jihar Sokoto ta kaddamar da shirin ciyar da al’umma a watan Ramadan, inda ta ware sama da Naira miliyan 998 domin rabon abinci ga masu azumi.
Rahoton VON ya nuna cewa gwamnan jihar, Ahmed Aliyu, ya bayyana cewa shirin yana daga cikin kudirin gwamnatinsa na tallafa wa al’umma a lokacin azumi.
A shekarar da ta gabata, gwamnatin jihar ta samar da kaji, naman shanu da ‘ya’yan itatuwa ga cibiyoyin ciyarwa 130 a fadin jihar.

Source: Facebook
Gwamna Ahmed Aliyu ya sanar da cewa, a bana, an fadada shirin tare da kara yawan cibiyoyin ciyarwa daga 130 zuwa 155.
Ya ce wannan karin zai taimaka wajen rage cunkoso a wuraren rabon abinci, domin saukaka wa masu azumi samun abinci cikin sauki.
Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa na kokarin ganin cewa kowa ya amfana da shirin, musamman marasa galihu da masu bukata ta musamman.
Ya kuma bukaci ma’aikatan da ke kula da rabon abinci da su gudanar da aikinsu da gaskiya domin tabbatar da cewa duk wanda ya cancanta ya samu abinci.
An karya kayan abinci a jihar Kano
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta hada kai da 'yan kasuwa domin karya farashin abinci a jihar Kano.
Rahotanni sun nuna cewa a karya farashin kayan masarufi da suka kai nau'uka 17 kuma sun hada da shinkafa, wake, man gyada da sauransu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


