Bayan Kwanaki 49, Kakakin Majalisa da Aka Taru Aka Tsige Ya Dawo kan Kujerarsa
- Mudashiru Obasa ya sake darewa kujerar shugaban majalisar dokokin jihar Legas bayan murabus din Mojisola Meranda a ranar Litinin
- Har yanzu ba a bayyana dalilan da suka sa Meranda ta sauka daga mukamin ba, sai dai ana zargin shugabannin APC da matsa mata lamba
- Bayan murabus dinta, an rantsar da Meranda a matsayin mataimakiyar kakakin majalisa, a wani mataki na kawo karshen rikicin majalisar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Mudashiru Obasa ya sake darewa kujerar kakakin majalisar dokokin jihar Legas bayan murabus din Mojisola Meranda daga mukamin.
Murabus din Meranda ya biyo bayan matsin lamba daga manyan jagororin siyasa, lamarin da ya bai wa Obasa damar komawa kan mukaminsa.

Source: Twitter
Obasa ya sake zama shugaban majalisar Legas
Har yanzu ba a bayyana cikakkun dalilan da suka sa Mojisola Meranda ta ajiye mukamin ba, kamar yadda rahoton ThisDay ya nuna.
Mudashiru Obasa, wanda ya riga ya taba shugabantar majalisar, ya kasance jigo a harkokin dokoki na jihar Legas.
Sake komawarsa ya jawo cece-kuce a tsakanin masu lura da siyasar jihar, yayin da ake hasashen tasirin hakan kan shugabancin majalisar.
Amma dai, wani rahoto na jaridar Daily Trust ya nuna cewa, akwai yiwuwar Obasa shi ma zai yi murabus daga mukamin a kashin kansa a nan gaba kadan.
Merinda ta zama mataimakiyar Obasa bayan murabus
Meranda ta karɓi mukamin mataimakiyar kakakin majalisa jim kadan bayan da aka matsa mata lamba ta yi murabus daga shugabancin majalisar.
Ta sanar da murabus dinta ne a zaman majalisar na ranar Litinin, inda ake zargin cewa shugabannin APC, da suka hada da Shugaba Bola Tinubu da Cornelius Ojelabi suka matsa lamba ta sauka.
“Daga yau na ajiye mukamina a matsayin kakakin majalisa,” inji Meranda a wani jawabi da aka watsa kai tsaye daga zauren majalisar.

Kara karanta wannan
'Yan sanda, DSS sun mamaye zauren majalisa, kakakin majalisa ta shirya yin murabus
Murabus din nata ya zo ne bayan wata ganawa ta sirri da aka yi tsakanin Obasa da wasu manyan ‘yan siyasa na jam'iyyar APC.
Duk da adawar wasu ‘yan majalisa, APC ta dage cewa dole ne a dawo da Obasa, inda ta yi watsi da matsayar majalisar, inji rahoton SaharaReporters.
Rikicin da ya faru bayan tsige kakakin majalisa
Tun farko, an tsige Obasa a ranar 13 ga watan Janairu bisa zarge-zargen karkatar da kudi da nuna danniya a shugabanci.
A lokacin, yawancin ‘yan majalisa sun goyi bayan tsige shi, suna masu cewa hakan zai taimaka wajen tabbatar da gaskiya da adalci.
Sai dai a ranar 27 ga Fabrairu, Obasa ya kutsa kai majalisar tare da wasu ‘yan majalisa hudu, inda ya jagoranci wani zama da ya jawo suka.
Dawowarsa ta kara rura rikicin shugabanci a majalisar, wanda ya jawo ‘yan majalisa suka rabu kashi biyu, amma dai murabus din Meranda ya kawo karshen takaddamar.
Jami'an tsaro sun mamaye zauren majalisar Legas
Tun da fari, mun ruwaito cewa, jami'an tsaro da suka hada da 'yan sanda, DSS da jami'an tsaron Legas sun mamaye zauren majalisar jihar a ranar Litinin.
Wata majiya ta shaida cewa jami'an tsaron sun hana hatta 'yan jarida shiga zauren majalisar yayin da 'yan majalisar ke shirin yin gagarumin zama a ranar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng

