'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Kai Hari a Borno, Sun Sace Babban Farfesa da Fasinjoji

'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Kai Hari a Borno, Sun Sace Babban Farfesa da Fasinjoji

  • Wasu ƴan ta'adda da ake zargin na ƙungiyoyin Boko Haram/ISWAP ne sun yi ta'asa a Borno a ranar Lahadi, 2 ga watan Maris 2025
  • Ƴan ta'addan sun yi awon gaba da Farfesa Abubakar Eljuma na jami'ar sojojin Najeriya da ke Biu (NAUB) tare da wasu fasinjoji
  • An sace babban malamin jami'ar ne tare da fasinjojin a kan titin hanyar Maiduguri-Damaturu a kusa da ƙauyen Kamuya
  • Majiyoyi sun bayyana cewa Farfesa wanda masani ne a harkar injiniyanci na cikin masu neman kujerar shugaban jami'ar NAUB

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Wasu ƴan ta’adda da ake zargin ƴan ƙungiyar Boko Haram/ISWAP ne Farfesa Abubakar Eljuma a jihar Borno.

Ƴan ta'addan sun sace Farfesan ne na jami’ar sojojin Najeriya da ke Biu (NAUB) tare da wasu fasinjoji a ranar Lahadi, 2 ga watan Maris 2025.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya amince da kafa sababbin Jami'o'i 11 a Najeriya, an jero sunayensu

'Yan Boko Haram/ISWAP sun sace Farfesa a Borno
'Yan Boko Haram sun sace Farfesa a jami'ar NAUB Hoto: @ProZulum
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa lamarin ya faru ne a kan titin Damaturu-Biu, wanda ke fama da matsalar tsaro, kusa da garin Kamuya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan Boko Haram/ISWAP sun sace Farfesa a Borno

Majiyoyi sun bayyana cewa Farfesa Eljuma, wanda shi ne shugaban tsangayar aikin Injiniya, na daga cikin manyan ƴan takarar da ke neman kujerar shugaban jami’ar, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.

Garin Kamuya yana da nisan kusan kilomita 10 daga Buratai, garin tsohon babban hafsan sojojin ƙasan Najeriya, Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai (mai ritaya).

Wannan ba shi ne karo na farko da irin wannan lamari ya faru ba, domin an sha samun sace mutane, fashewar bama-bamai da kuma kashe-kashe a wannan yanki a tsawon shekaru 10 da suka gabata.

"A ranar 2/3/2025, wasu da ake zargin ƴan ta'addan Boko Haram/ISWAP ne sun sace matafiya masu yawa daga motoci biyu ƙirar Golf da wata motar haya ta Borno Express a kan titin Damaturu-Biu."

Kara karanta wannan

Sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda, sun kashe babban kwamandan Boko Haram

“Rahotanni sun nuna cewa dukkan matan da ke cikin motocin an sako su, amma maza ne kawai suka rage a hannun ƴan ta'addan."
"Haka kuma, an tabbatar da cewa Farfesa Abubakar Eljuma na ɗaya daga cikin waɗanda aka sace, wanda ke cikin masu neman kujerar shugaban jami’ar NAUB."
“Muna bukatar addu’arku a cikin wannan wata mai alfarma na Ramadan don kubutar da su cikin gaggawa."

- Wata majiya

Mahukunta jami'ar NAUB sun shiga taro

Wani ma’aikacin jami’ar NAUB, wanda ba shi da izinin magana da manema labarai, ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Litinin.

Ya kuma bayyana cewa:

"Hukumar gudanarwar jami’ar na gudanar da wata muhimmiyar tattaunawa kan batun sace Farfesan."

Sojoji sun kashe kwamandan Boko Haram

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya masu aikin samar da tsaro a jihar Borno, sun samu nasara kan ƴan ta'addan Boko Haram.

Sojojin sun hallaka wani babban kwamandan ƴan ta'addan bayan sun kai farmaki a wani sansaninsu da ke ƙaramar hukumar Gwoza.

Kara karanta wannan

Ramadan: Ganduje ya tuna da musulman Najeriya, ya ba da shawara

Jami'an tsaro sun kuma hallaka ƴan ta'adda masu yawa tare da ƙwato tarin makamai a yayin artabun.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel