'Yan Sanda Sun Yi Bayanin Yadda Bindigogi kusan 4,000 Suka Bace a karkashin Kulawarta

'Yan Sanda Sun Yi Bayanin Yadda Bindigogi kusan 4,000 Suka Bace a karkashin Kulawarta

  • Rundunar 'yan sandan kasar nan ta bayyana takaicin yadda bindigu akalla 3,907 suka yi layar zana daga karkashin kulawar jami'anta
  • Wannan ya biyo bayan yadda majalisar kasar nan ta sako rundunar a gaba bisa makaman da har yanzu, ba a kai ga sanin inda suke ba
  • Rundunar ta aika sako mai kunshe da gargadin gaggawa ga manyan ma'aikatanta dake rassanta a kasar nan da su shiga taitayinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta bayyana cewa bindigu akalla 3,907 sun ɓace daga hannun jami’anta, lamarin da ya janyo damuwa ga hukumomin kasar nan.

Wannan na zuwa ne bayan tambayoyin da Kwamitin Majalisar Tarayya mai kula da Kayan Gwamnati ya yi wa Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun, kan ɓacewar makaman.

Kara karanta wannan

Dalibai sun fusata kan rufe makarantu a Arewa, NANS ta shirya zanga-zanga

Yan sanda
Rundunar 'yan sanda ta ce manyan jami'anta ne suka yi sakaci har bindigu suka bace Hoto: @FCT_PoliceNG, @NGRSenate
Asali: Twitter

A labarin da ya kebanta ga jaridar Aminiya, rundunar ta bayyana cewa matsalar tana da nasaba da sakacin wasu daga cikin jami’anta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ga laifin wasu daga cikin manyan jami'anta, wanda a cewarta, su ne suka mika bindigun ga ’yan sanda da ba su da cikakkiyar kwarewa.

Rundunar ’yan sanda ta yi nadama

Rundunar ’yan sandan Najeriya ta nuna takaicinta a cikin wata takardar sirri daga ofishinta na Abuja a kan rahoton ɓacewar makaman da gwamnati ta samar masu.

A cikin rahoton, Babban Mai Binciken Kuɗin Gwamnati na Tarayya, an bayyana cewa manyan bindigu 3,907 sun ɓace ba tare da cikakken bayani kan inda suke ba.

"Bata-gari sun sace makamai," 'Yan sanda

Kakakin rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya bayyana cewa bata-gari ne suka yi awon gaba da bindigun da ake zargin sun ɓace.

Sai dai ya ce akwai yiyuwar an yi aringizon adadin makaman da suka ɓace a rahoton Babban Mai Binciken Kuɗi, wanda ke nufin an kara yawansu.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kaduna ya yi gargadi kan siyasantar da tsaro bayan kalaman El-Rufa'i

Rundunar ’yan sanda ta gargadi jami’anta

Rundunar ’yan sanda ta gargaɗi manyan jami’anta da cewa za su fuskanci hukunci idan irin wannan lamari ya sake faruwa a ƙarƙashin jagorancinsu.

Yan sanda
Rundunar 'yan sanda ta gargadi manyan jami'anta Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Twitter

A cikin saƙon da aka aika wa rassan rundunar, an umarci manyan jami’ai da su riƙa bayar da rahoto kan dukkan makaman da ke ƙarƙashin kulawarsu kafin ko a ranar 23 ga kowane wata.

Jihohin da rundunar ’yan sanda ta aika gargadi

Rundunar ta aika saƙon gaggawa ga rassanta da ke Kano, Maiduguri, Legas, Fatakwal, Abuja, Aba, Warri, da Damaturu, tare da gargaɗin manyan jami’anta kan adana bindigun dake hannunsu.

Sauran jihohin sun haɗa da Bauchi, Enugu, Jos, Minna, Yola, Ibadan, Owerri, Makurdi, Lokoja, Gusau, Gombe, Lafia, Ilorin, Yenagoa, Uyo, Okija, Kaduna, da Uburu, domin kare makaman Najeriya.

Bindigogin rundunar 'yan sanda sun bace

A baya, mun ruwaito cewa majalisar kasar nan ta bayyana damuwa a kan yadda aka nemi bindigu kusan 4,000 suka bace daga hannun jami'an rundunar 'yan sandan kasar nan.

Kara karanta wannan

Fitinannen dan ta'addan da ya addabi Zamfara, Nabamamu ya fada tarkon sojoji

Binciken ya biyo bayan rahoton binciken 2019 na akanta janar na tarayya, Shaakaa Kanyitor Chira, wanda ya bayyana cewa mafi yawancin bindigun da suka bace kirar AK-47 ne.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labari

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.