Da Gaske Kotun Koli Ta Tsige Gwamnan PDP da Ke Fada da Wike? Gwamnati Ta Magantu

Da Gaske Kotun Koli Ta Tsige Gwamnan PDP da Ke Fada da Wike? Gwamnati Ta Magantu

  • Gwamnatin tarayya ta dakatar da ba da kudin jihar Ribas har sai Gwamna Simi Fubara ya mika kasafin kudin ga ‘yan majalisa
  • Kotun Koli ta soke zaben kananan hukumomin da aka gudanar a Ribas a shekarar 2023, wanda mutanen Simi Fubara suka lashe
  • Gwamnatin jihar Ribas ta musanta jita-jitar cewa an tsige gwamna, tana mai cewa yana kan karagar mulki ne bisa doka

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ribas - Ana ta rade radin cewa kotun koli ta kwace kujerar gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara a hukuncin da ta yanke ranar Juma'a.

A hukuncin kotun kolin na ranar Juma’a, ta umarci gwamnatin tarayya da ta dakatar da ba da kudaden jihar Ribas har sai Fubara ya mika kasafin kudin jihar ga ‘yan majalisar da ke karkashin jagorancin Martins Amaewhule.

Kara karanta wannan

Gwamna ya shiga matsala, Majalisar Dokoki ta ba shi sa'o'i 48 ya bayyana a gabanta

Gwamna Fubara ya yi magana da ake jita jitar kotun koli ta tsige shi
Gwamnan Ribas ya ce ba ya tsoron tsige da ake jita-jitar kotun koli ta sauke shi. Hoto: @SimFubaraKSC
Asali: Facebook

Hukuncin kotun da ya ba 'yan majalisa karfi

Kotun ta kuma soke zaben kananan hukumomi da aka gudanar a jihar a bara, wanda hukumar RSIEC ta shirya, inji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan hukunci ya bai wa Wike da ‘yan majalisar da ke tare da shi karfi a rikicin siyasar Ribas da ya barke tun watan Oktoba, 2023.

A kololuwar rikicin, Majalisar Dokokin Jihar Ribas ta kasu gida biyu, inda ‘yan majalisa 27 suka mara wa Wike baya, yayin da guda hudu suka tsaya tare da Fubara.

Sakamakon wannan hukunci ne, ake yada jita-jitar cewa yanzu Fubara ya rasa kujerarsa ta gwamnan jihar Ribas.

Sai dai, gwamnan Ribas, Fubara ya bayyana cewa ko kadan hukuncin kotun koli bai tsige shi ba, hasalima, shi ba ya tsoron tsigewa.

Matsalar da Fubara ya fuskanta bayan hukuncin kotu

A watan Oktoba 2023, ‘yan majalisar da ke goyon bayan Wike suka fara yunkurin tsige Fubara, wanda hakan ya haddasa kai hari da bam a ginin majalisar.

Kara karanta wannan

Daga fara Ramadan, ana barazanar rufe Najeriya kirif da zanga zanga ga Tinubu

Gwamna Fubara ya yi watsi da ‘yan majalisar 27, yana masu kallon cewa sun rasa kujerunsu tun bayan sauya shekarsu daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

A kan wannan dalili ne Fubara ya mika kasafin kudin shekarun 2024 da 2025 ga ‘yan majalisar hudu da ke goyon bayansa.

Amma Kotun Koli ta bayyana hakan a matsayin laifi, tana mai umartar Fubara da ya mika kasafin kudin ga ‘yan majalisar da ke goyon bayan Wike.

Gwamnati ta karyata zargin tsige Fubara

Gwamna Fubara ya jaddada cewa yana kan kujerarsa bisa doron doka
Fubara ya yi magana da aka ce kotun koli ta tsige shi, ya ce ba ya tsoron tsigewa. Hoto: @SimFubaraKSC
Asali: Twitter

Yayin da ake jita-jitar tsige Fubara, gwamnatin jihar Ribas ta ce babu wata barazana ta tsige gwamnan, domin yana kan karagar mulki ne bisa doka.

Kwamishinan yada labarai na jihar Ribas, Joseph Johnson, ya ce babu abin da zai hana gwamna gudanar da ayyukansa kamar yadda doka ta tanada.

A wata hira da manema labarai, Johnson ya ce:

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya amince da hukuncin kotun koli, ya kori dukkanin ciyamomin jiharsa

“Meyasa za mu ji tsoron tsigewa? Gwamnan yana kan aikinsa kuma yana da goyon bayan al’ummar Ribas.”

Ya kara da cewa:

“Za mu fara kaddamar da ayyuka daga ranar Litinin, kuma cikin kwanaki goma za a ci gaba da kaddamar da wasu.”

Johnson ya jaddada cewa hukuncin kotun koli bai tsige gwamna ba, illa dai ya dakatar da kudaden da jihar ke samu daga gwamnatin tarayya.

Fubara ya sauke ciyamomin jihar Ribas

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamna Siminalayi Fubara ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta aiwatar da hukuncin Kotun Koli bayan samun takardar hukuncin (CTC).

Kotun Koli ta soke zaben kananan hukumomi 23 na jihar Ribas, inda gwamnan ya umarci shugabannin gudanarwa (HLGAs) su dauki ragamar shugabanci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

iiq_pixel