Gwamnan PDP Ya Amince da Hukuncin Kotun Koli, Ya Kori Dukkanin Ciyamomin Jiharsa
- Gwamna Siminalayi Fubara ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta aiwatar da hukuncin Kotun Koli bayan samun cikakken kwafin hukuncin (CTC)
- Kotun Koli ta soke zaben kananan hukumomi 23 na jihar Ribas, inda gwamna ya umarci shugabannin gudanarwa (HLGAs) su karbi ragamar mulki
- Har ila yau, kotun ta hana Babban Bankin Najeriya da Akanta Janar na Tarayya fitar da kudaden gwamnati ga jihar Ribas har sai an bi umarninta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ribas - Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta aiwatar da hukuncin Kotun Koli bayan nazarin cikakken kwafin hukuncin.
A ranar Juma’a, Kotun Koli ta soke zaben kananan hukumomin da aka gudanar a jihar a ranar 5 ga Oktoba, 2024, saboda an yisa ba bisa ka’ida ba.

Asali: Twitter
Gwamnan Ribas ya saduda da hukuncin kotun koli
A cikin wani jawabin da ya yi a gidan talabijin na jihar a ranar Lahadi, Gwamna Fubara ya ce za su yi biyayya da hukuncin kotu a yanzu, inji rahoton Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fubara ya bayyana cewa ya gana da tawagar lauyoyinsa, kuma ana sa ran samun cikakken kwafin hukuncin (CTC) zuwa ranar 7 ga Maris, 2025.
Ya jaddada cewa gwamnatinsa tana mutunta doka kuma za ta yi aiki da kundin tsarin mulki kamar yadda doka ta tanada wajen aiwatar da umarnin Kotun Kolin.
Fubara ya umarci ciyamomi su mika mulki
Biyo bayan hukuncin Kotun Koli, gwamnan ya bada umarnin cewa shugabannin gudanarwa na kananan hukumomi (HLGAs) su karbi ragamar shugabanci a dukkanin kananan hukumomi 23 na jihar.
Ya ce wadannan jami’an gwamnati za su ci gaba da tafiyar da ayyukan kananan hukumomin har zuwa lokacin da za a gudanar da sabon zabe.
Hakazalika, ya umarci shugabannin kananan hukumomin da ke barin gado da su mika mulki ga HLGAs kafin ranar Litinin (gobe).
Yayin da ake ci gaba da samun rashin tabbas a siyasar jihar, Gwamna Fubara ya bukaci jama’a su kwantar da hankalinsu tare da tabbatar masu da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da gudanar da mulki bisa doka.
Kotun Koli ta hana Ribas samun kudin gwamnati

Asali: Facebook
A wani hukunci na daban, Kotun Koli ta hana Babban Bankin Najeriya (CBN), Akanta Janar na Tarayya da sauran hukumomi fitar da kudaden gwamnati ga jihar Ribas har sai an bi umarnin kotu.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Emmanuel Akomaye, ya jagoranci kwamitin alkalai biyar da suka yanke hukuncin, inda suka kori karar da Fubara ya shigar.
Gwamnan na Ribas ya shigar da kara yana kalubalantar halaccin majalisar dokokin jihar karkashin shugabancin Martin Amaewhule.
Kotun ta yanke hukunci cewa Martin Amaewhule ya koma kujerarsa tare da sauran ‘yan majalisa da aka zaba domin ci gaba da ayyukansu na majalisa nan take.
Fubara zai rantsar da zababbun ciyamomin Ribas
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamna Siminalayi Fubara na Ribas zai rantsar da shugabannin kananan hukumomi 23 da suka lashe zaben aka gudanar a jihar.
A wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar Dr Tammy Wenike Danagogo, an bayyana cewa za a rantsar da ciyamomin da yammacin Ladadi, 6 ga Oktobar 2024.
Asali: Legit.ng