'Mun Yi Babban Rashi': Gwamna Ya Girgiza da Mutuwar Sarkin Hausawa, Haruna Maiyasin

'Mun Yi Babban Rashi': Gwamna Ya Girgiza da Mutuwar Sarkin Hausawa, Haruna Maiyasin

  • Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, ya nuna alhinin rasuwar Sarkin Sasa, Alhaji Haruna Maiyasin Katsina, wanda ya rasu yana da shekaru 125
  • Makinde ya bayyana marigayin a matsayin shugaba nagari da ya jagoranci jama’arsa da kishi, tare da ba da goyon baya ga gwamnati
  • Gwamnan ya jajantawa iyalan marigayin da al’ummar Hausa/Fulani, yana mai rokon Allah ya jikansa da rahama ya kuma sanya shi cikin Aljanna

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Oyo - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana jimaminsa kan rasuwar Sarkin Sasa, Alhaji Haruna Maiyasin Katsina, wanda ya rasu ranar Asabar da yamma.

Makinde ya ce rasuwar Sarkin Sasa, wanda shi ne shugaban majalisar sarakunan Hausawa a jihohin Kudu 17, babban rashi ce ga Oyo da jihohin Kudu.

Makinde ya yi alhinin rasuwar Sarkin Sasa
Makinde ya mike sakon ta'aziyyar rasuwar sarkin Sasa, Alhaji Haruna Maiyasin. Hoto: @seyiamakinde
Asali: Twitter

Gwamna ya yi alhinin rasuwar Sarkin Hausawa

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi rashi: Tsohuwar Minista da ta kafa tarihi ta riga mu gidan gaskiya

Ya yi ta'aziyya ga iyalan marigayin da daukacin al’ummar Hausa/Fulani na Oyo da Kudancin Najeriya, yana mai rokon Allah ya jikansa da Rahama, inji rahoton Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Seyi Makinde ya bayyana cewa ya san marigayin tun kafin ya zama gwamnan Oyo, kuma suna da kyakkyawar alaka da juna.

Makinde ya ce:

“A madadin gwamnatin jihar Oyo, ina mika ta’aziyyata ga al’ummar Hausa/Fulani bisa rasuwar Sarkin Sasa.”

Gwamna ya yiwa Maiyasin addu'ar samun Aljanna

Sanarwar gwamnan na Oyo ta kara da cewa, “Rasuwarsa a shekaru 125 alama ce ta ƙarshen wani zamani mai daraja.”

Ya bayyana marigayin a matsayin shugaba nagari da ya jagoranci jama’arsa cikin kishi da kuma ba da cikakken hadin kai ga gwamnati.

Gwamnan jihar na Oyo, Seyi Makinde, ya kammala sanarwar da addu’ar Allah ya jikan Sarkin Sasa, ya sanya shi cikin Aljanna Firdausi.

Takadammar da ta kai ga tsige Maiyasin

Kara karanta wannan

Fitaccen basarake kuma shugaban majalisar sarakunan Hausawa a jihohi 17 ya rasu

Kafin rasuwar Alhaji Haruna Maiyasin, ya fuskanci kalubale masu yawa, ciki har da dakatarwa daga al'ummar Hausawa, bisa jagorancin Sarkin Hausawa na kasar Ibadan, Alhaji Ali Zungeru.

An taba tsige sarkin sasa kafin rasuwarsa
Takaddamar da ta jawo aka taba tsige sarkin Sasa daga mukaminsa. Hoto: @ZagazOlaMakama
Asali: Facebook

Idan ba a manta ba, Legit Hausa ta rahoto cewa, an dakatar da Alhaji Haruna Maiyasin bisa zarginsa da 'zagon kasa' da kuma nuna rashin ladabi ga Olubadan na kasar Ibadan.

An zargi basaraken da nade-naden mukaman sarauta ga mutane ba tare da sahalewar Sarkin Hausawan kasar Ibadan ba.

A jawabin Zungeru bayan kammala taron, ya yi nuni da cewa, ci gaba da zaman Maiyasin a matsayin Sarkin Sasa na iya kunna wata wutar rikici a yankin.

Yace:

"Abun bakin cikin shi ne, Sarkin Sasa yanzu ya fara daukar matakan da ke son rusa zaman lafiyar da ake yi a jihar, ta hanyar yin nade naden sarauta ba tare da sahalewar Sarkin Hausawa na kasar Ibadan ba.

Kara karanta wannan

Ramadan: 'Dan majalisa ya jika limamai da N40m, ya raba buhunan abinci 1,000

"Hakazalika, akwai zargin wani shiri da yake yi na tsige Sarkin Hausawa a Akinyele, Ado Sule da shugaban 'yan tirela, Yaro Abubakar, wadanda Zungeru ne ya nada su, wanda hakan na iya haddasa rikici. A kula, shi kanshi Maiyasin, yana karkashin Zungeru ne, don haka ba shi da ikon tsige wani daga mukaminsa."

Sarkin Sasa, Alhaji Haruna Maiyasin ya rasu

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Allah ya yi wa Sarkin Sasa da ke Ibadan a jihar Oyo, Alhaji Haruna Maiyasin rasuwa bayan ya shafe shekaru da dama kan karagar mulki.

Kafin rasuwar Alhaji Haruna Maiyasin, shi ne ke riƙe da muƙamin Shugaban Majalisar Sarakunan Hausawa a jihohi 17 na Kudancin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.