'Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 10, Sun Sace Ɗaliban Jami'a 4 a Wasu Jihohin Arewa

'Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 10, Sun Sace Ɗaliban Jami'a 4 a Wasu Jihohin Arewa

  • Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai farmaki a Paris Quarters da ke bayan jami’ar tarayya ta Dutsinma, inda suka sace dalibai hudu
  • Rahoto ya nuna cewa ‘yan bindigar sun mamaye yankin da misalin karfe 2:20 na dare, inda suka sace daliban kafin jami'an tsaro su kai dauki
  • Kasa da mako daya bayan satar daliban, ‘yan bindiga sun kai hari a wurin hakar ma’adinai a Karaga, jihar Neja, inda suka kashe mutane 10

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Katsina - Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun sace dalibai hudu daga unguwar Paris Quarters, dake bayan jami’ar tarayya ta Dutsinma, a Katsina.

Wannan mummunan lamari ya faru ne da misalin karfe 2:20 na dare a ranar Lahadi, inda mahara masu yawa suka afka yankin dauke da makamai.

Kara karanta wannan

Ana neman Turji, wani ɗan bindiga da yaransa sun ba da mamaki, sun mika wuya

'Yan bindiga sun sace daliban jami'ar tarayya ta Dutsinma da ke Katsina
'Yan bindiga sun farmaki Katsina, sun sace daliban jami'ar tarayya ta Dutsinma. Hoto: @ZagazOlaMakama
Asali: Twitter

'Yan bindiga sun sace dalibai 4 a Katsina

Mai sharhi kan harkokin tsaro a Arewa maso Gabacin Najeriya da kuma yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama ne ya sanar da hakan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu majiyoyin tsaro sun tabbatar da sacewa 'yan bindigar sun sace Wali Kayode, Fahad Muhammad, Emmanuel (ba a san sunansa na iyali ba), da wani mutum daya.

Bayan samun labarin harin, an ce jami’an tsaro sun garzaya wurin, amma ‘yan bindigan sun tsere kafin su isa.

Rahoton ya nuna cewa ana ci gaba da kokarin bin sahun masu garkuwa da mutanen domin ceto daliban FUDMA da aka sace cikin koshin lafiya.

'Yan ta'adda sun farmaki mutane a Neja

Harin na zuwa ne kasa da mako daya bayan wani farmaki da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 10 a wani wurin hakar ma’adanai a Karaga, jihar Neja.

Kara karanta wannan

Neja: 'Yan bindiga sun farmaki Musulmai ana shirin fara azumi, an rasa rayuka

Bisa bayanan sirri, harin ya faru ne a ranar 26 ga Fabrairu, inda ‘yan ta’adda da yawa suka kai farmaki kan ma’aikatan hakar ma’adanai.

A sabon rahoton da ya fitar a shafinsa na X, Makama ya ce maharan sun isa wurin akan babura, inda suka budewa ma’aikata da mazauna yankin wuta.

Sunayen mutane 10 da aka kashe a Neja

'Yan bindiga sun kashe mutane 10 da suka kai farmaki jihar Neja
'Yan bindiga sun kai farmaki jihar Neja, sun kashe akalla mutane 10. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

An gano sunayen wadanda suka mutu kamar haka: Lurwsnu Saidu, Zubairu Ibrahim, Tasiu Danlami, Zanaidu Ibrahim, Haliru Ibrahim, da Abbas Abdulhamid.

Sauran wadanda aka kashe sun hada da: Uzairu Ibrahim, Umaru Aliyu, Dahiru Fadama, da Alheri Gambo (wacce ita kadai ce mace a cikin wadanda aka kashe).

Wani mutum, Sabiu Yakubu (25), ya samu rauni a hannunsa na dama sakamakon harbin bindiga, kuma yana samun kulawa a asibitin Erena.

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa ‘yan bindigan suna daga cikin wata kungiyar ‘yan ta’adda da ke addabar yankin Shiroro, wadanda ke kai hare-hare kan wuraren hakar ma’adanai da kauyuka.

Kara karanta wannan

Dakaru sun yi dirar mikiya a kan 'yan ta'adda ana tsaka da karbar kudin fansa

A cikin ‘yan watannin nan, ‘yan bindigar suna ci gaba da kai hare-hare a Shiroro, inda suke kashe mutane da kara haddasa barazanar tsaro a yankin.

Duba rahotannin biyu a kasa:

'Yan bindiga sun kashe manoma 9 a Karara

A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun farmaki yankin Karaga da ke jihar Neja, inda suka kashe manoma tara, sannan suka sace mutane shida da shanu.

Mazauna yankin Bassa, sun bayyana cewa an yiwa mutanen kisan gilla, yayin da 'yan sa-kai ke ci gaba da nemo sauran gawarwaki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.