Tinubu Ya Shiga Wani Hali da Tsohuwar Minista Ta Rasu a Najeriya, Ya Tura Sako
- Shugaba Tinubu ya jajanta wa iyalan Adenike Ebunoluwa Oyagbola, tsohuwar Ministar Tsare-Tsare ta Kasa, wadda ta rasu tana da shekara 94 a duniya
- Tinubu ya yaba da irin gudunmuwarta wajen bunkasa Najeriya, musamman a matsayin ta na mace ta farko da ta zama minista mai cikakken matsayi
- Tinubu ya ce marigayiyar ta bar gagarumin tarihi, musamman wajen inganta matasa, al'adu da kuma ci gaban tattalin arzikin kasa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan Adenike Ebunoluwa Oyagbola wacce ta riga mu gidan gaskiya.
Marigayiyar, Adenike Ebunoluwa Oyagbola wacce ta rike muƙamin tsohuwar minista kuma jakadiya ta rasu tana da shekara 94.

Source: Facebook
Tinubu ya jajanta bayan rasuwar basarake
Hakan na kunshe a cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ya fitar, cewar Punch.

Kara karanta wannan
Zamfara: 'Yan bindiga sun sace shugabannin APC a kan hanyarsu ta zuwa gidan Sanata
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Makwanni biyu da suka wuce, Legit Hausa ta ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya jajantawa mutanen Remo da Gwamnatin Ogun bisa rasuwar Oba Idowu Basibo, wanda ya shafe shekaru 22 yana mulkin Iperu.
Tinubu ya yaba wa Oba Basibo kan jagoranci na adalci da hakuri, yana mai cewa girmansa da hikimarsa za su kasance abin tunawa da ba za a manta da su ba.
Shugaban ya yi addu’a ga marigayin, yana fatan za a ci gaba da girmama bayansa, tare da dorawa kan kyawawan ayyukansa na al’umma.
Tinubu ya kadu da samun labarin mutuwar Oyagbola
Tinubu ya jajanta wa iyalan marigayiyar da kuma al'ummar jihar Ogun bisa wannan babban rashi da suka yi.
A wani gagarumin yabo da ya yi mata, Tinubu ya siffanta marigayiyar a matsayin jagora da abin koyi ga mata a Najeriya.
Tinubu ya ce:
“A matsayin Minista ta farko da ta samu cikakken matsayi, ta karya shingaye tare da buda kofa ga mata da dama su samu mukamai.

Kara karanta wannan
Najeriya ta yi rashi: Tsohuwar Minista da ta kafa tarihi ta riga mu gidan gaskiya
“Gudunmuwarta wajen cigaban matasa da bunkasa al’adu ya bar tarihi mai kyau a bangaren kirkire-kirkire, tasirinta yana nan daram.”

Source: Facebook
Tinubu ya jero gudunmawar marigayiya, Oyagbola
Shugaban ya jaddada irin rawar da marigayiyar ta taka wajen cigaban kasa, musamman lokacin da take minista daga 1979 zuwa 1983.
Tinubu ya ce Najeriya za ta yi kewarta kan tsafta da gaskiya a shugabanci, tare da gode wa irin gudunmuwar da ta bayar.
Ya yi addu'a Allah ya jikanta, sannan ya bukaci iyalanta su dauki dangana da irin kyakkyawan tarihin da ta bari, Tribune ta ruwaito.
Gwamna ya jajanta da tsohuwar minista ta rasu
Kun ji cewa Gwamna Dapo Abiodun ya nuna alhinin rasuwar Cif Adenike Ebun Oyagbola, mace ta farko da ta zama minista mai matsayi a majalisar tarayya a Najeriya.
Gwamna Abiodun na jihar Ogun ya ce marigayiyar ta zama abin koyi ga mata a Afrika, tana da kwazo, jajircewa da kishin kasa, tare da neman daidaito a siyasa.
Abiodun ya yi addu’a Allah ya jikanta, ya kuma ba iyalanta hakurin jure wannan babban rashi da ya girgiza jihar Ogun da Najeriya baki daya.
Asali: Legit.ng