'Yan Bindiga Sun Saki Tsohon Shugaban NYSC, Janar Maharazu Tsiga? An Gano Gaskiya
- Wasu rahotanni sun fita a daren ranar 28 ga watan Fabrairun 2025 kan sakin tsohon shugaban hukumar kula da masu yi wa ƙasa hidima (NYSC)
- A cikin rahotannin an bayyana cewa ƴan bindiga sun saki Birgediya Janar Maharazu Tsiga ne bayan shafe kwanaki 23 a hannunsu
- Sai dai, wata majiya da ke kusa da iyalan Maharazu Tsiga ta bayyana saɓanin hakan lokacin da Legit Hausa ta tuntuɓeta
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - An fitar da wasu rahotanni masu cewa tsohon Darakta-Janar na hukumar kula da masu yi wa ƙasa hidima (NYSC), Birgediya Janar Maharazu Tsiga, ya samu ƴanci daga hannun ƴan bindiga.
Rahotannin sun ce Birgediya Janar Maharazu Tsiga ya samu ƴanci daga hannun masu garkuwa da shi ne a ranar Juma’a, bayan ya shafe kwanaki 22 a hannunsu.

Asali: Facebook
Tashar Channels tv ta ce wata majiya ta tabbatar mata da sakin Maharazu Tsiga a daren Juma’a, 28 ga watan Fabrairun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyar ta bayyana cewa Birgediya Janar Maharazu Tsiga yana samun kulawar likitoci a wani asibiti da ba a bayyana ba, saboda dalilai na tsaro.
Shin da gaske an saki Maharazu Tsiga?
Legit Hausa ta tuntuɓi wani makusancin iyalan tsohon shugaban na NYSC, Rabo Tsiga, kan labarin sakin Maharazu Tsiga.
Rabo Tsiga ya bayyana cewa ko kaɗan babu ƙamshin gaskiya dangane da sakin tsohon shugaban na hukumar NYSC.
Ya bayyana cewa ko a lokacin da aka buga labarin sakin Maharazu Tsiga, ba su daɗe da yin magana da shi ba a hannun ƴan bindigan da suka tsare shi.
"Gaskiya labaran cewa an saki Janar ba gaskiya ba ne. Ban san a inda suka samu hakan ba domin har yanzu yana tsare a hannunsu."
"Har yanzu muna ci gaba da lallaɓawa domin mu samu a sako shi daga hannunsu."
- Rabo Tsiga
Ƴan sanda ba su da masaniya
Legit Hausa ta sake tuntuɓar kakakin rundunar ƴan sandan jihar Katsina, Abubakar Sadiq Aliyu, wanda ya bayyana cewa bai da tabbaci kan sakin Maharazu Tsiga.
"Gaskiya ba ni da tabbaci kan labarin amma ina ƙoƙarin bincikawa domin tabbatarwa."
- Abubakar Sadiq Aliyu
Maharazu Tsiga ya shafe kwanaki a hannun ƴan bindiga
An sace Janar Maharazu Tsiga ne a ranar 6 ga watan Fabrairu, 2025, a gidansa da ke ƙauyen Tsiga, cikin karamar hukumar Bakori ta Jihar Katsina.
A lokacin harin, mutane biyu sun samu raunuka daban-daban sakamakon harbin bindiga.
Haka nan kuma, wani daga cikin ƴan bindigar da suka kai harin ya gamu da ajalinsa, bayan wani daga cikin ƴan tawagarsu harbe shi ba da gangan ba.
Masu garkuwa da mutanen da suka yi awon gaba da shi, ƙarƙashin jagorancin wani hatsabibin ɗan bindiga mai suna Babaro, sun nemi a biya su Naira miliyan 250 kafin su sake shi

Kara karanta wannan
A gaban Tinubu da manyan jiga jigai, Ganduje ya bankado abubuwan da ya tarar a APC
Sace Janar Tsiga ya jefa mutane cikin firgici
A wani labarin kuma, kun ji cewa sace tsohon shugaban hukumar NYSC, Birgediya Janar Maharazu Tsiga da 'yan bindiga suka yi, ya jefa mutane cikin firgici.
Wasu mutanen ƙauyen Tsiga da ke ƙaramar hukumar Bakori a jihar Katsina sun yi ƙaura daga gidajensu sakamakon sace tsohon shugaban na NYSC.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng