Bashi: Obasanjo da Tsofaffin Shugabanni Kasashe 7 Sun Roka wa Afrika Yafiya
- Tsohon shugaban Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya jagoranci wasu tsofaffin shugabannin Afrika wajen nema wa nahiyar mafita a kan tarin bashi da ta karbo
- Wannan na zuwa ne a lokacin da basussuka suka yi wa manyan kasashen da ke shiyyar katutu, lamarin da Obasanjo da takwarorinsa ke ganin akwai matsala
- Obasanjo, wanda shi ne shugaban kungiyar tsofaffin shugabannin kasashen Afrika masu nema wa nahiyar afuwa ya ce akwai bukatar a tallafa wa shiyyar
- Ya ce yawan bashin da ake bin kasashen suna takure su, tare da zama barazana ga ci gaban tattalin arzikin nahiyar, hadi da jawo koma baya ga manyan ayyuka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Cape Town, South Africa - Tsofaffin shugabanni takwas na kasashen Afrika sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya da aka kira Cape Town Declaration.
Yarjejeniyar ta na yin kira ga kasashe masu karfin tattalin arziki da su yafe wa kasashen da suka yi karbo tulin bashi afuwa.

Asali: Facebook
Reuters ta wallafa cewa har ila yau, shugabannin sun yi tarayya wajen yin kira da a rage tsadar rance kudade ga duk kasashen da ke bukatar karbo bashin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsofaffin hugabannin Afrika masu neman a yafe bashi
The Guardian ta ruwaito cewa sanya hannu kan wannan yarjejeniya ne yayin ƙaddamar da shirin shugabannin Afrika na nema wa nahiyar afuwa.
Shugabannin sun bayyana cewa an yi hakan ne da nufin kawo sauyi a fannin ragewa kasashe nauyin bashi da ke dabaibaye tattalin arzikinsu.
Obasanjo da shugabannin Afrika da ke jagorantar nemo afuwa
Daga cikin shugabannin da ke cikin wannan yunƙuri akwai tsohon Shugaban Najeriya kuma shugaban ƙungiyar, Olusegun Obasanjo, da tsohuwar Shugabar Malawi, Joyce Banda.
Sauran sun haɗa da tsohon Shugaban Tanzania, Jakaya Mrisho Kikwete, da tsohuwar Shugabar Mauritius, Dr Ameenah Gurib-Fakim, tare da wasu shugabanni daga ƙasashen Afrika daban-daban.
Jagororin Afrika na son ci gaban nahiyar
Shugabannin da suka sa hannu a yarjejeniyar sun yi kira da a ƙara ƙaimi wajen haɗin gwiwar ƙasashen duniya don magance matsalar bashi da ke addabar Afrika.
Sun kuma jaddada buƙatar yin garambawul a tsarin hada-hadar kuɗi na duniya domin bai wa kasashe masu tasowa damar samun ingantaccen tallafi.

Asali: Twitter
Shugaban kungiyar, Olusegun Obasanjo, ya ce:
“Afrika na fuskantar nauyin bashi da ba za a iya jurewa ba. Yana da matuƙar muhimmanci mu haɗa kai domin nemo mafita ga wannan matsala.
Makomar Afrika a hade take da makomar duniya, kuma dole ne mu nemi mafita ga matsalar bashi domin haɓaka ci gaban tattalin arziƙi mai ɗorewa a nahiyar.
“Kudirin da Afirka ta Kudu ta ɗauka na bai wa rage bashi muhimmanci da yin aiki tare da sauran ƙasashe don magance tushen matsalar bashin da ke da tsada yana da matuƙar kyau.”

Kara karanta wannan
Tsohon shugaba Buhari, El-Rufa'i da sauran jagororin APC sun ki halartar taron APC
Wata kasar Afrika ta tono mai
A baya, kun samu labarin cewa kasar Rwanda ta sanar da cewa ta gano danyen mai a karon a tafkin Kivu, tare da rijiyoyi 13 a yankin da ke iyaka da Kongo, wanda zai kara bunkasa tallalin arzikinta.
Francis Kamanzi, shugaban hukumar ma'adinai, fetur da gas na kasar ta Rwanda, ya tabbatar da wannan ci gaba, yana mai cewa abu ne mai kyau cewa ƙasar yanzu tana da mai na kashin kanta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng