Gidauniya Za Ta Dauki Nauyin Karatun Yaran Talakawa, Ta Raba Fom na JAMB 300
- Gidauniyar Ibrahim Ali Usman ta raba fom na JAMB guda 300 ga dalibai da aka zaba daga yankin Bauchi ta Kudu
- Daliban sun fito daga kananan hukumomi bakwai, kuma an bi ka’ida wurin tantance wadanda suka fi cancanta
- An tabbatar da wanda ya ci jarabawar JAMB, Gidauniya za ta dauki nauyin karatunsa har zuwa jami’a ko kwalejin ilimi
- Daraktan yada labaran Gidauniyar, Nuruddeen Haske, ya ce manufarsu ita ce tallafa wa dalibai masu hazaka domin samun ilimi mai inganci
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Bauchi - Gidauniyar Ibrahim Ali Usman a jihar Bauchi ta sake yin abin alheri ga wasu zababbun dalibai.
Gidauniyar ta raba fom na JAMB guda 300 ga wasu dalibai da aka zaba da suka yi fice a yankin Bauchi ta Kudu.

Source: Facebook
Bauchi: Gidauniya ta nemo hanyar inganta ilimi
Daraktan yada labaran Gidauniyar, Nuruddeen Yakubu Haske shi ya tabbatar da haka ga wakilin Legit Hausa a ranar Juma'a 28 ga watan Faburairun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idan ba ku manta ba, Legit Hausa ta ruwaito muku cewa Gidauniyar ta tallafawa ɗalibai da littattafai domin inganta harkokin ilimi a jihar Bauchi da ke Arewacin Najeriya.
Gidauniyar ta ƙaddamar da tallafin litattafai akalla 1,050,000 domin tallafa wa ɗaliban Bauchi ta Kudu a wani babban taro a watan Janairun 2025.
Albashir da Gidauniya ta yi wa zababbun dalibai
Nurudden Haske ya ce Gidauniyar ta biyawa dalibai akalla 300 da suka fito daga kananan hukumomi bakwai da ke yankin Bauchi ta Kudu kudin jarrabawar.
Ya ce an bi dukkan tsarin da ya dace wurin zaben yaran da suke da kokari da ke shirin rubuta jarabawar JAMB domin zuwa makarantun gaba da sakandare.
Daga bisani, ya ce duk dalibin da ya samu nasara, Gidauniya za ta dauki nauyin karatunsu har zuwa jami'o'i ko kuma kwalejin ilimi da sauransu.

Source: Facebook
Hanyar da Gidauniya ta bi wurin zakulo ɗaliban
Nuruddeen Yakubu Haske ya ce:
"Abin da ya faru shi ne Gidauniya ce ta dauki mutum 300 daga cikin talakawa da suka fito daga shiyyar Bauchi ta Kudu a kananan hukumomi bakwai.
"An zabo yaran ne da suke da kokari wadanda za su rubuta jarabawar JAMB wanda daga bisani duk wanda ya yi nasara, Gidauniya za ta dauki nauyin karatunsa.
"Za ta dauki nauyin karatun tun daga farko har karewa a jami'a ko kwaleji, kenan duk wadanda suka dace za a dauke su da daukar nauyin karatunsu.
"Kamar yadda na fada tun farko an dauki daliban ko in ce yara daga kananan hukumomi bakwai da suka fito daga shiyyar Kudancin Bauchi."
Gidauniya ta ba mata dankareren gida a Bauchi
A baya, kun ji cewa Gidauniyar Ibrahim Ali Usman ta tallafa wa wata mata mai suna Barakatu, ta gina mata gida bayan rushewar inda take zaune a ciki.
Barakatu ta nuna godiyarta ga Hon. Ibrahim Ali Usman ta hanyar ba shi Alkur'ani mai girma tare da yin addu'oi na musamman gare shi da iyalansa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng


