Bayan Fara Binciken Zabtare Albashi: Abba Ya Dakatar da Shugaban Ma'aikatan Kano
- Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya dakatar da mukaddashin shugaban ma’aikatan gwamnati, kan zargin taba albashin ma’aikata
- An nada Malam Umar Muhammad Jalo a matsayin sabon mukaddashin shugaban ma’aikatan gwamnati yayin da ake gudanar da bincike
- Gwamnatin Kano ta kafa kwamitin bincike karkashin jagorancin Abdulkadir Abdussalam, tare da ba shi kwanaki bakwai a gano gaskiya
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sha alwashin cewa babu wanda za a dagawa kafa idan aka same shi da zabtare albashin ma'aikatan Kano
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya dakatar da mukaddashin shugaban ma’aikatan jihar, Salisu Mustapha.
Gwamna Abba Yusuf ya dauki matakin dakatar da Salisu Mustapha ne bisa zargin rashin biya da kuma cire kudi daga albashin ma'aikatan Kano ba bisa ka’ida ba.

Asali: Facebook
Abba ya dakatar da shugaban ma'aikatan Kano
Bayanin hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta kuma ce an umarci Salisu Mustapha da ya sauka daga matsayin babban sakatare na sashen tsare-tsare, a ofishin HoS, domin bada damar bincike.
Domin tabbatar da cigaba a harkokin mulki, gwamna Yusuf ya nada Malam Umar Muhammad Jalo a matsayin sabon mukaddashin shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar.
Kafin nadinsa, Malam Umar Muhammad Jalo yana rike da mukamin babban sakatare a ma’aikatar REPA, kuma zai ci gaba da aiki har sai an kammala bincike.
Gwamna ya gargadi masu hannu a zabtare albashi
Gwamna Abba Yusuf ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta yarda da wata badakala ba, tare da gargadin cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci.
A jiya Alhamis din ne aka kafa kwamitin bincike kan badaƙalar, karkashin jagorancin Abdulkadir Abdussalam, kuma an ba shi kwanaki bakwai domin gano gaskiyar lamarin.
Ana sa ran kwamitin zai binciko musabbabin matsalar biyan albashi da cire kudi daga albashin ma'aikatan Kano ba bisa ka’ida ba.

Asali: Twitter
Gwamnatin Kano ta nada Salisu Mustapha a matsayin mukaddashin shugaban ma’aikata ne bayan an bai wa Abdullahi Musa hutun jinya a kasar Indiya.
Gwamnatin Kano ta ce za ta dauki matakan da suka dace domin tabbatar da gaskiya da adalci a lamarin.
'Lallai ayi wa ma'aikata adalci' - El-Bash
Wani matashi a Kano, Bashir Abdullahi El-Bash da muka ji ta bakinsa game da lamarin, ya ce matakin da Abba ya dauka ya dace.
El-Bash ya ce akwai bukatar kwamitin da aka kafa ya yi aiki cikin gaskiya domin ganin an bi kadin ma'aikatan da aka tauyewa hakkokinsu.
"Gwamnati ta yi kokari da ta fara daukar mataki irin wannan, ko ba komai, mutane za su gamsu cewa za a yi bincike tsakani da Allah.
"Lallai a yi wa ma'aikatan Kano adalci, a dawo da kudin ma'aikatan da aka cire mana, sannan a hukunta wadanda suka aikata wannan danyen aiki, ni shawarata kenan."

Kara karanta wannan
El Rufa'i ya fadi yadda aikin Ribadu ke taimaka wa 'yan ta'adda da miyagun makamai
Abba bai ji dadin yankewa ma'aikata albashi ba
Tuni da fari, mun ruwaito cewa, gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi tsokaci mai zafi kan rage albashi da rashin biyan wasu ma’aikata haƙƙoƙinsu yadda ya kamata.
Ya bayyana lamarin a matsayin cin amanar jama’a da take haƙƙin ma’aikata, wanda gwamnatinsa ba za ta lamunta da shi ba.
Gwamnan ya nuna rashin jin daɗinsa kan rahotannin da ke cewa wasu ma’aikata sun kwashe watanni ba tare da an biya su ba, yayin da wasu ake rage musu albashi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng