Magana Ta Kare: Masana Taurari Sun Fadi Ranar Ganin Watan Ramadan a Najeriya
- Wani dan kwamitin ganin wata a fadar Mai alfarma Sarkin Musulmi ya yi karin haske kan matakan da suke bi wajen tantance labaran da ake isar musu
- Kwamitin yana amfani da na’ura wajen tantance jinjirin wata, amma ba a fara amfani da ita wajen duba wata kai tsaye ba a Najeriya har yanzu
- Masu ilimin taurari sun bayyyana cewa akwai alamar da ta nuna rana da lokacin da za a ga watan Ramadan na 2025 a Najeriya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Sokoto - 'Dan Kwamitin ganin wata a Najeriya, Simwal Usman Jibril ya bayyana hanyoyin da ake bi don tantance bayyanar jinjirin wata a lokacin azumi da sauran lokutan shekara.
A cewar Malam Simwal Jibril, tun daga 25 ga wata ake fara fadakarwa kan duba wata, saboda yadda aka dauki lamarin da muhimmanci.

Asali: Facebook
Legit ta tattaro bayanan da Simwal Usman Jibril ya yi ne a cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Simwal ya ce ana amfani da na’ura wajen tantance sabon wata don bambance shi da sauran abubuwa masu kama da shi.
Sai dai duk da haka har yanzu ba a fara amfani da ita kai tsaye wajen duba wata a Najeriya ba, sabanin wasu kasashe kamar Saudiyya.
Rage rudani kan ganin wata a Najeriya
Simwal ya ce a baya an samu matsaloli da rudani kan batun ganin wata, musamman idan aka samu sabanin ra’ayi tsakanin mutane daban-daban.
Sai dai dan kwamitin ya bayyana cewa an rage irin wannan rudani ta hanyar hada dukkan masu ruwa da tsaki a kan batun.
Kwamitin ya ce idan aka samu wadanda suka saba da ganin watan da Sarkin Musulmi ke sanarwa, ana kokarin yin aiki tare da su a shekara mai zuwa don dinke sabanin.

Kara karanta wannan
Da gaske Tinubu ya fara korar Amurkawa 700 da hana amfani da wayoyinsu a Najeriya?
Yadda sarkin Musulmi ke tantance ganin wata
Domin tabbatar da sahihancin ikirarin ganin wata, kwamitin ya ce akwai tambayoyi biyar da ake yi wa mutumin da ya ce ya hango jinjirin wata:
1. Shin ka ga faduwar rana? Wannan na taimakawa wajen tabbatar da cewa ba a kalli wani abu daban ba.
2. Ta wane bangaren rana ka ga jinjirin wata? Domin yana canzawa daga lokaci zuwa lokaci, kuma masana sun san a wane bangare yake bayyana a ko da yaushe.
3. Karfe nawa ka hango shi? Wannan yana taimakawa wajen tantance dacewar bayanin da aka bayar.
4. Yaya yanayin kwanciyar wata a lokacin da aka hango shi? Ana bincike don ganin ko ya yi daidai da bayanan falaki.
Wata zai fito ranar Juma'a - Simwal
Simwal Usman Jibril ya bayyana cewa bayanan falaki sun nuna cewa akwai yiwuwar ganin jinjirin watan Ramadan a ranar Juma’a.
Ya bayyana haka ne inda ya ce za a haifi jinjirin watan a ranar Juma'a sai dai kuma idan an samu wasu dalilan da za su hana ganin shi.

Asali: Twitter
Kira ga jama’a kan ganin wata
Dan kwamitin ya bukaci kowa ya fita don neman jinjirin wata idan lokaci ya yi, sannan a sanar da hakimai ko dagatai idan an hango shi.
Haka zalika, an yi kira ga al’ummar Musulmi da su rika bin umarnin Sarkin Musulmi kan batun ganin wata, domin samun hadin kai a cikin al’umma.
An bukaci duba watan Ramadan a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa fadar sarkin Musulmi ta bukaci a duba watan Ramadan a ranar Juma'a, 29 ga Sha'aban 1446.
Kwamitin ganin wata a fadar sarkin Musulmi ya tanadi lambobin waya da za a sanar da shi labarin ganin wata a sassan Najeriya daban daban.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng