Wadanda suka ce sun ga wata jiya karya sukayi, ko a yau ba za'a gani ma: Masani Simwal

Wadanda suka ce sun ga wata jiya karya sukayi, ko a yau ba za'a gani ma: Masani Simwal

- Wadanda suka sabawa umurnin shugaba sun yi kuskure babba, Simwal

- Wasu jagororin addini sun yi Sallar Idi ranar Laraba duk da kasancewar ba'a ga wata ba

Daya daga cikin mambobin kwamitin duba wata na majalisar koli ta shari'ar Musulunci a Najeriya, Simwal Usman Jibril, ya bayyana cewa wadanda sukayi ikirarin sun ga wata jiya kuskure suka yi.

Simwal ya yi bayanin cewa ko a yau 30 ga watan Ramadana ba zai yiwu a ga watan ba saboda wasu dalilai.

Ya bayyana hakan a shafinsa a Facebook da Tuwita.

A cewarsa, hasali ya kamata jama'a suga wata ranar 30 ga wata cikin sauki amma tunda awanni jinjirin watan bai wuce 22 ba, ba za'a gani cikin sauki ba.

Ga bayaninsa: "Hasali a ranar 30 ga watan akan ga jinjirin wata cikin sauki kuma babba. Watan na fadi ne akalla waw guda daya bayan faduwar ranar idan jinjirin wata ya bayyana a jiya."

"Amma saboda sai bayan karfe 8 na daren jiya jinjirin wata ya bayyana, Insha Allah da yamman nan awanni jinjirin watan 22 kuma zai fadi bayan mintuna 42 da faduwar rana Insha Allah amma ba za'a iya gani cikin sauki ba."

KU KARANTA: Hotunan Zulum da Oshiomole Na Yakin Neman Shugaban Kasa a 2023 Sun Bazu a Gombe

Wadanda suka ce sun ga wata jiya karya sukayi, ko a yau ba za'a gani ma: Masani Simwal
Wadanda suka ce sun ga wata jiya karya sukayi, ko a yau ba za'a gani ma: Masani Simwal Hoto: Simwal Usman Jibril
Asali: Facebook

DUBA NAN: Hoton Hadiza Bala Usman Da El-Rufai a Fadar Sarkin Zazzau Ya Janyo Maganganu

"Yanzu na gama tabbatar daga kwamitin duban wata da fadar mai martana Sarkin Musulmi cewa babu inda aka ga wata a yau a Najeriya. Ko wadanda suka ce sun gani jiya sun ce basu gani yau ba," Ya kara

"Mun bayyana karara cewa da kamar wuya a ga watan yau saboda awanni jinjirin watan 22 da yan kai. Ko wadanda suka yi ikirarin gani jiya sun gaza gani yau. Hakan na tabbatar da cewa kuskure sukayi jiya."

A bangare guda, Sarkin Musulmi, Sultan Alhaji Sa'ad Abubakar III ya kalubalanci shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnoni da su kawo karshen rashin tsaro a kasar nan, Jaridar The Nation ta wallafa.

Sarkin Musulmin wanda shine shugaban majalisar koli ta al'amuran addinin Musulunci a Najeriya, yayi wannan jawabin ne a Sokoto bayan sallar idin karamar sallah da aka yi a ranar Alhamis da ta gabata.

Ya ce: "Muna kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da dukkan gwamnonin jihohi da su gaggauta kawo karshen rashin tsaro da ya addabi kasar nan."

Asali: Legit.ng

Online view pixel