'Ana Barazanar Kashe Shugabar Hukumar NAFDAC,' Yarbawa Sun Aika Sako ga Tinubu

'Ana Barazanar Kashe Shugabar Hukumar NAFDAC,' Yarbawa Sun Aika Sako ga Tinubu

  • Kungiyar Yarbawa taAfenifere ta bukaci shugaba Bola Tinubu ya kara tsaurara tsaro ga Farfesa Mojisola Adeyeye da jami’an NAFDAC
  • Farfesa Adeyeye ta bayyana cewa an yi yunkurin kashe ta, an kuma sace yaron wani ma’aikacin NAFDAC saboda ayyukan da suke yi
  • Afenifere ta bukaci gwamnati ta dauki matakin gaggawa don kare jami’an gwamnati daga ’yan ta’adda da ke barazana ga rayuwarsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kungiyar Afenifere ta bukaci shugaba Bola Tinubu ya kara tsaurara matakan tsaro ga shugabar hukumar NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye, da sauran jami’an gwamnati.

A ranar Laraba, Farfesa Adeyeye ta bayyana cewa ana barazana ga rayuwarta da ma wasu ma’aikatan NAFDAC saboda ayyukan da suke yi.

Shugabar hukumar NAFDAC ta yi ikirarin yana barazana ga rayuwarta
Shugabar NAFDAC, Mojisola Adeyeye ta ce ana barazana ga rayuwarta da ta ma'aikatanta. Hoto: @NafdacAgency
Asali: Twitter

'Ana barazanar kashe ni' - Shugabar NAFDAC

Ta bukaci mahukunta su kare su, tana mai cewa rayuwarta da ta wasu jami’an NAFDAC na cikin tsari yayin da suke aiwatar da ayyukansu, inji rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

APC ta fadi abin da zai mayar da Tinubu kujerarsa bayan zaben 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farfesa Adeyeye ta bayyana cewa, an yi yunkurin kashe ta a watanni shida da suka gubata, lamarin da ya nuna karara irin barazanar da take fuskanta.

A cewarta, an sace yaron daya daga cikin ma’aikatan NAFDAC a Kano, saboda mahaifinsa yana aiki kamar yadda doka ta tanada.

Sai dai, an samu nasarar ceto yaron daga hannun wadanda suka sace shi, kamar yadda ta bayyana a cikin sanarwar gaggawa da ta aikawa jami'an tsaro.

Yarbawa sun ce gwamnati ta kare shugabar NAFDAC

Kungiyar Afenifere ta mayar da martani, tana mai cewa wannan barazana ga rayuwarta da jami’anta ba abin a yi wasa da ita ba ne.

A cewar kungiyar Yarbawan, duk wani yunkuri na hallaka Farfesa Adeyeye, to yunkurin farmakar lafiyar al’umma, tsaron kasa da kuma tsarin doka da oda ne.

Kungiyar ta ce Farfesa Adeyeye na kan gaba wajen yaki da kwayoyi da magungunan da abinci na jabu da ke barazana ga lafiyar ’yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Bayan kusoshin APC sun kaurace wa taron jam'iyya, Tinubu ya dora wa Ganduje aiki

Afeniferi ta nemi Tinubu ya kare jami'an hukumar NAFDAC daga 'yan ta'adda
Kungiyar Yarbawa ta aika sako ga Tinubu da aka fara barazana ga rayuwar ma'aikatan NAFDAC. Hoto: @NafdacAgency
Asali: Twitter

Afenifere ta ce Najeriya bai kamata Najerita ta yi sakaci da wadanda ke sadaukar da rayuwarsu don amfanin al’umma ba.

Ta bukaci gwamnati ta samar da ingantattun matakan tsaro ga shugabannin hukumomin yaki da miyagun kwayoyi da ma na cin hanci da rashawa.

Afenifere ta gargadi gwamnati da sakaci da jami'anta

A cewar kungiyar Yarbawan, akwai bukatar a kare manyan jami’an ta hanyar ba su motocin sulke, hada su da jami’an tsaro na musamman, da kuma na’urorin bincike na zamani.

Kungiyar ta bukaci a kare iyalan wadannan jami'ai, a lokacin da suke kan aiki da kuma bayan sun bar mukamansu.

Afenifere ta gargadi cewa idan ’yan ta’adda sun fahimci gwamnati ba za ta iya kare jami’anta ba, to za su ci gaba da aikata manyan laifuka da kai farmakin ramuwar gayya.

Kungiyar ta bukaci Shugaba Tinubu da ya dauki matakin gaggawa don kare Farfesa Adeyeye da sauran jami’anta.

Kara karanta wannan

Shirin babban taron APC ya gama kankama, jagororin jam'iyya sun hallara Abuja

NAFDAC ta kama jabun kayayyaki na N140bn

A wani labarin, mun ruwaito cewa, hukumar NAFDAC ta bayyana cewa ta lalata kayayyaki da aka kama, wanda darajarsu ta haura Naira biliyan 120, tsakanin Yuli da Disamba 2024.

An gudanar da lalata wadannan kayayyaki a shiyyoyi shida na Najeriya da Babban Birnin Tarayya, Abuja, domin kare lafiyar al’umma daga hadurran da za su iya haifarwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.