NAFDAC ta rufe kamfanonin hada magungunan jabu a Kano

NAFDAC ta rufe kamfanonin hada magungunan jabu a Kano

- Jami'an hukumar NAFDAC reshen jihar Kano sun kai sumame wasu kamfanonin yin magungunan dabobi a Bichi da ke jihar

- Hukumar ta NAFDAC ta kama mai kamfanonin magungunan bisa zarginsa da yin magunguna marasa inganci da sayar da su a kasuwanni dauke da lambar NAFDAC na bogi

- Hukumar ta ce ta shafe watanni shida tana bincike a kan magungunan da kamfanonin bayan ta lura ana samun karuwar magungunan jabu a kasuwanin Kano

DUBA WANNAN: Gwamnati, 'yan sanda da kungiyar kwadago sun bukaci mutanen Katsina su kare kansu daga 'yan bindiga

NAFDAC ta rufe kamfanonin hada magungunan jabu a Kano
NAFDAC ta rufe kamfanonin hada magungunan jabu a Kano. Hoto @daily_nigerian
Source: Twitter

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna, NAFDAC, ta rufe kamfanonin kera magungunan dabobi na jabu a karamar hukumar Bichi na jihar Kano.

Shugaban hukumar na jihar, Shaba Muhammad ne ya bayyana hakan yayin wata sumame da jami'an hukumar suka kai Laraba a Bichi kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Mista Muhammad ya ce an kai sumamen ne bayan gano magungunan dabobi na jabu masu yawa na yawo a kaswuwan Sabon Gari da wasu manyan kasuwanni a Kano.

Ya ce hukumar ta kwashe watanni shida tana bincike a kan masu sarrafa magungunan jabun.

Shugaban ya ce jami'an hukumar sun kai sumame kamfanonin a Bichi a ranar Talata sun kuma kwato magunguna na kimanin Naira miliyan 10.

KU KARANTA: Fitar da bidiyon lalata na budurwa ya saka ango ya fasa aurenta a Sokoto

Muhammad ya ce kamfanonin na kera magungunan dabobi na jabu sannan su saka musu lambar NAFDAC na jabu suna yaudarar mutane suna sayar musu.

Ya kara da cewa hukumar ta kama wani mutum daya da ake zargi mai suna Jamilu Muhammad Sani wanda shine mai kamfanonin.

Mista Muhammad ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu da zarar an kammala bincike.

"Muna karbar samfurin magunguna da allurai daga kamfanoni mu tafi dakin gwaje-gwaje don tabbatar da ingancinsu,' in ji shi.

A bangarensa, Muhammad Sani ya yi ikirarin cewa yana da lasisi na aiki a matsayin kwararre a fanin kula da dabobi kuma ya kwashe kimanin shekara guda yana yin magungunan.

A wani labarin daban, Tsohon Sarkin Kano, Sanusi Lamido-Sanusi, a ranar Talata ya ce 'yan Najeriya suna korafi a kan karij kudin lantarki da aka yi a baya bayan nan ne saboda ba su da tabbacin za su more kudinsu.

Da ya ke jawabi a wurin taron masu saka hannun jari karo na 5 da aka yi a Kaduna, Sanusi ya yi bayanin cewa 'yan Najeriya da dama har da masu treda a shirye suke su biya kudin idan har za a sika samun wutar yadda ya dace domin su inganta sana'ar su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel