Dakaru Sun Yi Dirar Mikiya a kan 'Yan Ta'adda ana tsaka da Karbar Kudin Fansa

Dakaru Sun Yi Dirar Mikiya a kan 'Yan Ta'adda ana tsaka da Karbar Kudin Fansa

  • Wasu 'yan bindiga sun gamu da gamonsu suna tsaka da kokarin karbar kudin fansar wani bawan Allah da suka sace a jihar Zamfara
  • Dakarun hadin gwiwa sun dakile dira a wurin musayar kudin a kusa da dajin Ganuwa, Karamar Hukumar Tsafe na jihar
  • Lamarin ya firgita miyagun mutanen, wanda ya sa suka bude wa jami'an tsaro wuta, aka yi masu dabara har suka karar da alburusai

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Zamfara - Jami’an tsaro na hadin gwiwa (JTF) a Zamfara sun samu nasarar hana wani shirin karbar kudin fansa da ‘yan bindiga suka shirya.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an hallaka wasu daga cikin ‘yan ta’adda yayin da suka fito daga maboyarsu a dajin Ganuwa, Karamar Hukumar Tsafe, domin karbar kudin fansa.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun ritsa 'yan bindiga a maboyarsu, an kama 'yan ta'adda 20

SOJOJI
Dakaru sun fatattaki masu karbar kudin fansa Hoto: Nigerian Army HQ
Asali: Facebook

Zagazola Makama ya ruwaito cewa lamarin ya faru ne a ranar Laraba, bayan da jami’an tsaro suka samu bayanan sirri kan wani yunkuri na kai wa ‘yan ta’adda kudin fansa don sakin wani wanda aka sace.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda dakaru suka hallaka ‘yan ta’adda

Bayan samun rahoton sirri, dakarun sun tsara dabarun hana biyan kudin fansa tare da kaddamar da farmaki a kan ‘yan ta’addan.

A cewar majiyoyi, miyagun sun fito daga maboyarsu da niyyar karbar kudin fansa, amma suka fada hannun jami’an tsaro da suka yi shiri na musamman don dakile shirin.

A lokacin da suka yi ido biyu, sai ‘yan ta’addan suka fahimci cewa jami’an tsaro sun yi shirin dakile yunkurinsu, sai suka bude wuta.

Wannan ya haddasa musayar wuta mai tsanani tsakanin bangarorin biyu, har dakarun sojojin Najeriya suka samu gagarumar nasarar dakile shirin karbar fansar.

Dakaru sun ragargaza ‘yan ta’adda

Dakarun hadin guiwa sun taka rawar gani ta hanyar amfani da dabaru don tabbatar da cewa ‘yan ta’addan sun yi amfani da yawancin harsasansu kafin su kai musu farmaki.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun ɓullo da sabuwar dabara, mataimakin ciyaman ya faɗa tarko a Zamfara

Wannan dabara ta sa jami’an tsaro suka samu nasarar hallaka wasu daga cikin miyagun, yayin da sauran suka tsere da raunuka.

Bayan artabu, dakarun sun kwato babura guda biyu da makamai da suka fito daga hannun ‘yan ta’addan.

Ta'addanci: Jami'an tsaro sun ceto wanda aka sace

Bayan nasarar fatattakar ‘yan ta’addan, jami’an tsaro sun samu nasarar kubutar da mutumin da aka sace ba tare da wani rauni ba.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa an mayar da wanda aka ceto ga iyalansa cikin koshin lafiya, bayan an tabbatar da cewa bai samu wata illa ba.

Sojoji
Dakaru sun hallaka 'yan ta'adda Hoto: Nigerian Army HQ
Asali: Facebook

Nasarar da aka samu ta kara fito da nuna kokarin da hukumomin tsaro ke yi na dakile ayyukan ‘yan ta’adda a jihar Zamfara da ma yankin Arewa maso Yamma gaba daya.

A halin da ake ciki, jami’an tsaro sun sha alwashin ci gaba da gudanar da atisayen farmakan ‘yan ta’adda domin tabbatar da cewa an kawo karshen ayyukan ta’addanci a Arewa.

Kara karanta wannan

Mutanen gari sun kama 'yan bindiga hannu da hannu, sun kashe su har lahira

'Yan ta'adda sun sace mataimakin ciyaman

A wani labarin, kun ji cewa ‘yan bindiga sun sace mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Bukkuyum a jihar Zamfara, Bala Muhammad, tare da wasu fasinjoji a kan babban titi.

Baya ga yin amfani da babura, rahotanni sun nuna cewa maharan sun bullo da wata sabuwar dabara ta yin garkuwa da mutane ta hanyar amfani da motar bas, lamarin da ya firgita jama'a.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.