Ana Murna Farashin Fetur Ya Sauka, Gwamnati Ta Garkame Wasu Gidajen Mai
- Hukumar NMDPRA ta rufe gidajen mai biyar a Katsina saboda matse litar mai da rashin lasisin aiki, don kare hakkin abokan huldarsu
- Jami’in hukumar, Umar Muhammad, shi ya jagoranci binciken da ya gano cewa gidajen man suna amfani da dabara wajen cutar mutane
- Umar Muhammad ya zayyana sunayen gidajen da aka rufe suka hada da A A Rano, Ashafa da wasu uku, ya gargadi masu gidajen mai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Katsina - Hukumar NMDPRA, reshen jihar Katsina, ta rufe gidajen mai biyar saboda karya ka’idoji da kuma cutar da kwastomomi ta hanyar matse litar mai.
Wannan matakin ya biyo bayan binciken da hukumar ke gudanarwa don tabbatar da cewa gidajen mai suna bin ka’idojin aiki da kare hakkin masu sayen mai.

Asali: UGC
NMDPRA ta rufe gidajen mai 5 a jihar Katsina
Jami’in kula da hukumar a jihar, Umar Muhammad ne ya jagoranci binciken, inda aka gano wasu gidajen mai na aiki ba tare da lasisin da aka sabunta ba, inji rahoton Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Binciken ya kuma nuna cewa wasu daga cikin gidajen man sun jima suna sayar da mai kasa da yadda ya kamata, suna matse lita, baya ga rashin kayan tsaro kamar na kashe gobara.
Gidajen man da aka rufe sun hada da gidan man Total, A.A. Rano, Ashafa, Maje Gas, da Gwagware International Ltd.
Hukumar NMDPRA ta gargadi masu matse litar mai
Hukumar ta gargadi gidajen mai da ke matse lita, ta ce duk wanda aka samu yana aikata hakan zai fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada.
Muhammad ya jaddada kudirin hukumar na tabbatar da bin doka da oda a bangaren man fetur, yana mai cewa irin wannan bincike zai ci gaba a fadin jihar don kare hakkin abokan hulda.
A cewarsa:
"Ba za mu amince da duk wani salon da ya saba da ka’idojin aiki ba. Gidajen mai dole su bi dokoki kamar yadda doka ta tanada.”
Hukumar NMDPRA ta kuma dauki matakin dakile irin wannan matsala a wasu jihohin kasar.

Asali: Twitter
NMDPRA ta bude gidajen man da ta rufe a Kogi
A makon da ya gabata, hukumar ta bayyana cewa za ta dauki tsauraran matakai don tabbatar da cewa gidajen mai a jihar Kogi suna sayar da adadin mai da ya dace.
Jami’in hukumar a jihar Kogi, Mr. Ogbe Godwin, ya bayyana hakan ne ga manema labarai a Lokoja, yana mai cewa an rufe gidajen mai bakwai saboda irin wadannan laifuffuka.
Gidajen man da aka rufe sun hada da Solag Resources Ltd. (Ankpa), Hismus Oil and Gas (Obajana), Riyenic Global Ltd. (Oke-Ibukun Kabba), S.O.T Nigeria Ltd. (Omuo Kabba), Marktot Oil and Gas (Kabba), da NIPCO.
Jaridar The Guardian ta rahoto cewa an tuhumi masu gidajen mai da yin algus ta hanyar bata mitocin sayar da mai don matse litar man da suke zubawa abokan huldarsu.
Sai dai an sake bude wadannan gidajen man bayan sun biya tarar da aka ci su, kamar yadda hukumar ta NMDPRA ta sanar.
An gargadi gidajen mai kan matse lita
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin jihar Enugu ta yi barazanar rufe dukkanin gidajen mai da aka kama suna matse lita.
Kwamishinan ayyuka na musamman na jihar, Emeka Ajogwu ya nuna cewa akwai wasu gidajen mai da ake zargi suna matse lita domin zaluntar masu sayen fetur.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng