An Janye Masu Gadin Shugabar Majalisa, An Koma Takawa Tsohon Shugaba baya

An Janye Masu Gadin Shugabar Majalisa, An Koma Takawa Tsohon Shugaba baya

  • Rikicin majalisar dokokin jihar Legas ta sake salo, bayan an ga tsohon shugaban majalisar ya kutsa kai cikin ofis da rakiyar jami'an tsaro
  • Matakin na zuwa ne a lokacin da aka sanar da janye jami'an tsaron dake ba shugabar ta yanzu, Mojisola Meranda kariya a safiyar Alhamis
  • Lamarin ya kara dagula rikicin majalisar da ya jawo aka tsige Mudashiru Obasa bisa zarge-zarge da dama, wanda suka hada da kama-karya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos - Tsohon shugaban majalisar dokokin Jihar Legas, Mudashiru Obasa, ya mamaye harabar majalisar dokokin jihar duk da maye gurbinsa da aka yi.

An samu labarin cewa Obasa, tare da rakiyar wasu jami’an tsaro, ya shiga ofishin Shugaban Majalisa da misalin karfe 12 na rana a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

"Karya kake yi," Ƴan Majalisa 36 sun ƙara yi wa kakaki bore, sun tabbatar da tsige shi

Obasa
Obasa ya kutsa ofishin shugaban majalisa duk da tsige shi daga ofis Hoto: @nigerianoise/@abbeygovernor1
Asali: Twitter

Jaridar Punch ta wallafa cewa Obasa ya bayyana a ofishin kakakin majalisa ne bayan janye jami’an tsaron da ke gadin sabuwar Shugabar Majalisar, Mojisola Meranda.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mudashiru Obasa ya kutsa kai ofishin majalisa

A cewar The Cable, Sakataren Yada Labaran na Meranda, Segun Ajiboye, ya tabbatar da lamarin a wani takaitaccen sako da ya fitar a ranar Alhamis.

Ya yi zargin cewa Obasa da mukarrabansa sun afka wa ofishin shugaban majalisar ba tare da izini ba, wanda hakan ya saba doka.

Majalisa
Obasa ya samu rakiyar jami'ian tsaro zuwa majalisa Hoto: @lshaofficial
Asali: Twitter

Wata majiya daga bangaren tsohon kakakin, ta tabbatar da cewa yanzu haka sun shiga ofishin, a lokacin da dambarwar majalisar ke ci gaba da ruruwa.

Yadda aka samu sabani a majalisar Legas

Tun bayan sauke Obasa daga shugabancin majalisa, aka kuma zabi Meranda a matsayin sabuwar shugaba, rikici ya mamaye majalisar dokokin Legas.

Fiye da 90% na ‘yan majalisar sun zargi Obasa da irin salon mulkin karfa-karfa, yawan latti wajen halartar zaman majalisa, danniya, da rashin girmama sauran ‘yan majalisa.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: An janye dukkanin jami'an tsaron da ke gadin kakakin majalisa

Baya ga haka, an kuma zarge shi da cin zarafin ofis, tauye hakkin ‘yan majalisa, wawure kudade, da wasu zarge-zarge masu yawa.

An nemi Tinubu ya tsoma baki a rikicin Legas

Manyan APC, ciki kamar tsofaffin gwamnonin Osun, Ogun da Legas, watau Cif Bisi Akande, Segun Osoba, da Akinwunmi Ambode, sun shiga tsakani domin kawo sasanci a lamarin.

Haka kuma sun bukaci shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da sauran manyan 'yan siaysa a Legas da su gaggauta shiga tsakani domin yayyafa wa matsalar ruwa.

Wani jigo a kwamitin shawarwari na gwamnonin Legas, Cif Muraina Taiwo, ya ce akwai yiwuwar a sake duba cikin ‘yan majalisa bakwai daga yankin Legas ta Yamma dan zaben sabon shugaba.

Ya na ganin akwai bukatar Meranda da Obasa su hakura da mukamin domin a tabbatar da zaman lafiya da sasanci a tsakaninsu.

An janye dakarun tsaron shugabar majalisar Legas

A baya, kun ji cewa shugabar majalisar Legas, Mojisola Meranda, ta fada a mawuyacin hali bayan an janye dukkanin jami'an tsaron da ke gadinta, yayin da rikicin majalisa ke kamari.

Kara karanta wannan

IBB: 'Dalilan kitsa harin rashin imani da ya kashe tsohon shugaban kasa, Murtala'

A safiyar Alhamis, hadiman shugabar majalisar sun wayi gari da labarin cewa an cire dukkan jami'an tsaron da suka hada da 'yan sanda da DSS daga ofishinta ba tare da dalili ba.

Wani hadimi mai kusanci da Mojisola Meranda ya bayyana cewa wannan mataki daidai yake da jefa rayuwar shugabar a cikin mawuyacin hali da kuma barazanar tsaro ta kowace fuska.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.