Ramadan: Yadda Kayan Abinci Suka Yi Sauki a Arewa ana Shirin Azumi
- Rahotanni sun nuna cewa farashin kayayyakin abinci kamar shinkafa, masara, gero, dawa da wake sun fadi a jihohin da ake samar da su
- Masana sun danganta hakan da karancin sayen hatsi daga manoman kaji da masu sarrafa shinkafa bayan Kirsimeti da sabuwar shekara
- Wasu kuma sun ce shigowar kayayyakin amfanin gona daga kasashen waje na daga cikin dalilan da suka haddasa saukar farashin a kasuwanni
- Wani mai sayar da kayan abinci a jihar Gombe, Ibrahim Sa'id ya yi wa Legit karin haske kan yadda saukar farashin ke shafar harkokinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Arewa - A yayin da azumin Ramadan ke karatowa, rahotanni sun tabbatar da cewa farashin kayayyakin abinci da suka hada da hatsi da sauran nau'ikan amfanin gona ya fara sauka.
Rahoto ya nuna cewa dalilan da suka haddasa saukar farashin sun hada da karancin sayayya daga masu nika shinkafa da manoman kaji, tare da shigowar kayayyakin abinci daga ketare.

Asali: Facebook
Wani bincike da jaridar Daily Trust ta yi ya nuna cewa an samu saukin farashin masara, shinkafa, gero, dawa da wake musamman a jihohin da ake samar da su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Raguwar farashin hatsi a kasuwanni
A kasuwannin Kaduna, an samu gagarumin saukar farashin kayayyakin abinci. A kasuwar Saminaka, buhun masara da aka sayar kan N70,000 zuwa N75,000 yanzu ya sauka zuwa N47,000.
A kasuwar Giwa kuwa, buhun gero da dawa ana sayar da su tsakanin N50,000 da N51,000, yayin da wake fari ya sauka daga N150,000 zuwa N100,000.
A jihar Taraba, farashin buhun shinkafa ya ragu daga N50,000 zuwa N45,000, yayin da buhun masara ya sauka daga N57,000 zuwa tsakanin N40,000 da N45,000.

Kara karanta wannan
Soyayya ta ƙare: Wani ɗan Najeriya ya lakaɗawa budurwarsa dukan tsiya har ta mutu
Farashi ya sauka a jihohin Benue da Kano
A Makurdi, babban birnin jihar Benue, farashin shinkafa ya ragu sosai. A kasuwar Wadata, ana sayar da buhun shinkafa tsakanin N26,000 zuwa N29,000, sabanin N45,000 zuwa N55,000 a baya.
A kasuwar Zamani ta jihar Benue kuwa, farashin mudu daya na shinkafa ya fadi daga N2,700 zuwa N1,800.
A jihar Kano, kasuwar Danhassan ta sami ragin farashi inda mudu daya na wake ya sauka zuwa N2,500 daga N3,500, yayin da farashin mudun gero ya ragu daga N2,700 zuwa N1,200.
A kasuwar Dawanau, ana sayar da mudu daya na masara tsakanin N1,200 da N1,300, yayin da mudun wake ke tsakanin N2,000 da N2,200.
Farashin kayan abinci a kasuwannin Niger
A jihar Neja, kasuwar Manigi da ke Mashegu ta nuna raguwar farashi sosai. Buhun wake ya sauka daga N200,000 zuwa N90,000, yayin da wake fari ya fadi daga N160,000 zuwa N90,000.
Buhun masara da dawa kuwa yanzu ana sayar da su a kan N40,000, sabanin N85,000 da ake sayarwa kafin girbi.

Asali: Getty Images
A kasuwar Lemu, ana sayar da buhun shinkafa a kan N108,000, yayin da buhun masara, dawa da gero ke kan farashin N42,000 kowanne.
Legit ta tattauna da mai sayar da abinci
Wani mai sayar da kayan abinci a Gombe ya shaida cewa an samu saukar farashin kayan abinci, amma duk da haka ya ce akwai dalilan da suka sanya farashi bai sauka a kananan shaguna ba.
"Sauki yana zuwa ne a hankali, dole ne a kara hakuri. Da sannu kowa zai shaida saukin cikin kankanin lokaci.
"Masu shaguna suna da tsohon kaya, da sun gama sayar da shi za su fara sayar da wanda suka saya da araha, sauki zai game ko ina"
- Ibrahim Sa'id
Ganduje ya yabi Tinubu kan saukar farashi
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya yabawa Bola Tinubu kan saukar farashin kayan abinci.
Abdullahi Ganduje ya ce tsare tsaren Bola Tinubu suna aiki yadda ya kamata kuma a cewarsa, hakan ne ya sanya fara samun saukin rayuwa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng