Dakarun Sojoji Sun Yi Dirar Mikiya kan 'Yan Ta'adda, Sun Kashe Miyagu 2, An Kama 3

Dakarun Sojoji Sun Yi Dirar Mikiya kan 'Yan Ta'adda, Sun Kashe Miyagu 2, An Kama 3

  • Sojojin runduna ta 3 da na Operation Safe Haven sun kashe ‘yan bindiga biyu tare da ceto wata mata da ‘yarta a Gindiri, jihar Filato
  • A wani farmaki na daban, sojojin sun kama fitattun masu garkuwa biyu a Barkin Ladi, bayan samun bayanan sirri daga wani da aka kama
  • An samu bayanai daga wadanda aka kama, masu taimakawa sojoji wajen gano maboyar sauran ‘yan bindiga da ke addabar Filato

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Filato - Sojojin runduna ta uku da na Operation Safe Haven sun kashe ‘yan bindiga biyu tare da ceto wata mata da ‘yarta a Gindiri, karamar hukumar mangu ta jihar Filato.

Bayanan sirri sun tabbatar da cewa wannan farmaki ya faru ne a ranar 23 ga Fabrairu, misalin karfe 8:30 na dare, bayan da aka samu rahoton sace mutanen a garin Gindiri.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi tabargaza a Abuja kusa da barikin sojoji, sun sace mutane

Sojoji sun yi nasara kan 'yan bindiga a Filato, sun kashe miyagu 2
Sojoji sun kashe masu garkuwa da mutane a Filato, sun ceto wadanda aka sace. Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Sojoji sun kashe 'yan bindiga a Filato

Mai sharhi kan lamuran tsaro a yankin Arewa maso Gabas da Tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya sanar da hakan a shafinsa na X a safiyar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya ce sojoji sun yi gaggawar kaddamar da farmaki bayan samun rahoto, inda suka bi sawun ‘yan bindigar har zuwa wajen gari.

Bayan sun yi dauki ba dadi, sojojin sun samu nasarar kashe ‘yan bindiga biyu yayin da suka kama wani da raunukan harbin bindiga.

"An ceto matar da ‘yarta ba tare da sun samu rauni ba, sannan an kai su asibitin koyarwa na jami’ar Jos (reshen Gindiri) domin duba lafiyarsu, kafin daga bisani a mikasu ga iyalansu."

- Zagazola Makama

Bayan wannan nasara, sojoji sun kara kaimi wajen sintiri a yankin domin inganta tsaro da tabbatar da zaman lafiya.

Kama hatsabiban masu garkuwa a Filato

Kara karanta wannan

Mutanen gari sun kama 'yan bindiga hannu da hannu, sun kashe su har lahira

Sojoji sun saki hoton daya daga cikin 'yan bindigar da suka kama a jihar Filato
An ga hoton daya daga cikin 'yan bindigar da sojoji suka kama a jihar Filato. Hoto: @ZagazOlaMakama
Asali: Twitter

A wani farmakin na daban, sojojin runduna ta 3 da na Operation Safe Haven sun kama wasu fitattun masu garkuwa da mutane biyu a karamar hukumar Barkin Ladi, jihar Filato.

Rahotanni daga majiyoyin sirri sun bayyana cewa an kaddamar da wannan farmaki, mai suna Operation Golden Peace, a ranar 24 ga Fabrairu, misalin karfe 2:20 na rana a Lugere Sho, Barkin Ladi.

Wannan harin ya biyo bayan bayanan sirri da aka samu daga wani da aka kama a ranar 22 ga Fabrairu.

A yayin farmakin, sojoji sun sake cafke wani fitaccen dan fashi da mai garkuwa da mutane a kauyen Kwok, wanda ke cikin karamar hukumar Barkin Ladi.

An gano maboyar wasu masu garkuwa

Wanda ake zargin, da ke hannun hukuma a halin yanzu, yana bayar da bayani kan aikata laifuffukan da suka hada da garkuwa da mutane a jihohin Filato da Nasarawa.

Kara karanta wannan

Matakin da sojoji suka dauka da Bello Turji ya sanya N25m ga kauyukan Sokoto

Rahotannin sirri na soji sun nuna cewa daya daga cikin wadanda aka kama ya amsa cewa ya taba samun raunukan harbin bindiga a wata fafatawa da sojoji.

Haka kuma, wadanda ake zargin sun bayyana sunayen wasu abokan aikinsu da maboyarsu a yankunan Barkin Ladi.

A halin yanzu, sojoji na ci gaba da gudanar da samame domin kama ragowar ‘yan kungiyar masu garkuwa da mutane.

Filato: Sojoji sun kashe hatsabibin dan bindiga

A wani labarin, mun ruwaito cewa, sojoji sun kashe ‘yan bindiga biyar, ciki har da shugabansu, Kachalla Saleh, a Wase, Jihar Filato.

Kashe Kachalla Saleh ya faru kasa da mako guda bayan wata artabu tsakanin ‘yan bindiga da ’yan banga a yankin, kamar yadda rahoto ya nuna.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.