Sukar Tinubu da Ribadu: APC Ta Kasa Hakura, Ta Yi Wa El Rufai Martani Mai Zafi

Sukar Tinubu da Ribadu: APC Ta Kasa Hakura, Ta Yi Wa El Rufai Martani Mai Zafi

  • Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ba ta ji daɗin kalaman da Nasir Ahmed El-Rufai ya yi ba a kan Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
  • Mataimakin shugaban APC na ƙasa ya caccaki tsohon gwamnan na Kaduna kan sukar da ya yi wa shugaban ƙasan da Malam Nuhu Ribadu
  • APC ta bayyana cewa El-Rufai yana jin haushi ne saboda bai samu biyan buƙatarsa ta son zuciya ba da ya nema a gwamnatin Tinubu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Jam’iyyar APC ta yi martani kan sukar da Nasir El-Rufai ya yi wa shugaba Bola Tinubu da Malam Nuhu Ribadu.

Jam'iyyar APC ta caccaki tsohon gwamnan na jihar Kaduna kan maganganun da ya yi a kan shugaba Tinubu da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu.

Kara karanta wannan

2027: Jigon APC a Kudu maso Kudu ya fadi lokacin hadaka da El Rufa'i

APC ta caccaki El-Rufai
APC ta caccaki El-Rufai kan sukar Tinubu da Ribadu Hoto: @elrufai, @NuhuRibadu, @DOlusegun
Asali: Facebook

Mataimakin shugaban APC na ƙasa (Yankin Kudu Maso Gabas), Dr. Ijeoma Arodiogbu, ne ya caccaki El-Rufai a wata hira da jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ijeoma Arodiogbu ya bayyana sukar da El-Rufai ya yi wa shugaba Tinubu da Ribadu matsayin abin takaici.

El-Rufai ya caccaki Tinubu da Ribadu

A cikin hirar, El-Rufai ya soki sauye-sauyen tattalin arziƙin da Tinubu ke aiwatarwa, yana mai cewa tsarin yadda ake aiwatar da su bai dace ba.

Hakazalika, Malam El-Rufai ya soki naɗin da aka yi wa Ribadu a matsayin mashawarci a kan tsaro, yana mai cewa bai cancanci wannan muƙamin ba.

El-Rufai ya kuma zargi Ribadu da jagorantar wani shiri na ɓata masa suna saboda burinsa na tsayawa takarar shugaban ƙasa a shekarar 2031.

Wane martani APC ta yi wa El-Rufai

Amma yayin da yake mayar da martani kan waɗannan maganganu, Arodiogbu ya bayyana tsohon gwamnan a matsayin mutum mai baƙar zuciya wanda bai samu cikar burinsa na son kai ba a gwamnatin Tinubu.

Kara karanta wannan

2027: El Rufa'i ya fadi kalubalen da za a fuskanta wajen tallar Tinubu a Arewa

"El-Rufai mutum ne mai baƙar zuciya. Ina ganin abubuwan da ya so samu daga gwamnati bai same su ba, shi ya sa yake jin haushi. Ba abin mamaki ba ne."
"Hakan ya bayyana abin da yake nufi da cewa jam’iyyar ce ta bar shi, ba wai shi ne ya bar jam’iyyar ba.”

- Ijeoma Arodiogbu

APC ba ta fargabar rasa El-Rufai

Da aka tambaye shi ko APC tana damuwa da yiwuwar rasa babban ɗan siyasa irin El-Rufai zuwa wata jam’iyyar adawa, mataimakin shugaban na APC ya ce tsohon gwamnan ba barazana ba ne ga jam'iyyar.

“Ba barazana ba ne kwata-kwata. A cikin makonni kaɗan da suka gabata, kusan duk wani sanannen ɗan siyasa, sanatoci, ƴan majalisar wakilai, tsofaffin ƴan takarar LP da PDP suna shigowa APC."
“Don haka, idan dukkan fitattun ƴan siyasa a jihohi suna komawa APC, me kake tsammani? Saboda haka, goyon bayan El-Rufai bai da wani tasiri."

Kara karanta wannan

'Don Allah ka bar ni': Ribadu ya yi martani ga El-Rufai bayan kalamansa kan zaben 2031

- Ijeoma Arodiogbu

El-Rufai ya faɗi wanda ya hana shi minista

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi magana kan rashin samun muƙamin da ya yi a gwamnatin Bola Tinubu.

El-Rufai ya bayyana cewa Bola Tinubu ne ya canza shawara kan ba shi minista, saɓanin tunanin da ake yi na cewa majalisar tarayya ce ta ƙi amincewa ya zama minista.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel