Tinubu Na Shirin Gudanar da Ƙidaya, An Gano Matsalar da Za Ta Iya Dagula Komai

Tinubu Na Shirin Gudanar da Ƙidaya, An Gano Matsalar da Za Ta Iya Dagula Komai

  • Gwamnatin Najeriya ta shirya gudanar da sabuwar kidayar jama’a da gidaje, inda za a yi amfani da fasahar zamani don tattara bayanai
  • Shugaba Bola Tinubu ya ce za a kafa kwamitin da zai tantance kasafin kidayar tare da la’akari da halin tattalin arzikin ƙasa na yanzu
  • Shugaban NPC, Nasir Kwarra, ya ce an sayo kwamfutoci 760,000 don gudanar da aikin, kuma NPC za ta nemi tallafi daga abokan hulɗa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin Najeriya ta shirya gudanar da kidayar jama’a da gidaje, inda za a yi amfani da fasahar dangwalen yatsa da na'ura mai kwakwalwa.

A wata ganawa da jami’an hukumar kidaya ta kasa (NPC) a fadar gwamnati, Shugaba Bola Tinubu ya ce zai kafa kwamitin da zai daidaita kasafin kudin kidayar da halin tattalin arzikin ƙasa a yanzu.

Kara karanta wannan

EFCC: Kotu ta ƙara takaita tsohon gwamnan CBN, an kwace miliyoyin daloli da kadarori

Shugaba Bola Tinubu ya magantu kan shirye-shiryen gudanar da kidaya a Najeriya
Tinubu ya fadi shirin da ya kamata ayi na gudanar da kidayar jama'a da gidaje a Najeriya. Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga ya fitar, wadda Olusegun Dada ya wallafa a shafinsa na X, an ji cewa kidayar ƙarshe da aka gudanar a Najeriya ita ce ta Nuwambar 2006.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya yi magana kan kidayar jama'a

Sanarwar ta ce Tinubu ya jaddada cewa dole ne hukumar kula da shaidar dan kasa (NIMC) ta kasance cikin duba tsarin kidayar don tabbatar da daukar ingantattun bayanai.

"Dole ne mu san yawan mutanenmu da yadda za mu tsara bayananmu. Ba tare da kidaya mai inganci ba, ba za mu iya tsara ayyukan ci gaba kamar aikin yi, noma da wadatar abinci ba," in ji Shugaba Tinubu.

Ya bayyana cewa sabuwar kidayar za ta ba da ingantattun alkaluma da za a yi amfani da su wajen tsara shirye-shiryen ci gaba da kyautata rayuwar ‘yan Najeriya.

Tinubu ya kara da cewa idan ana da cikakkun bayanai, za a inganta rabon takin zamani da sauran tallafin gwamnati ga manoma.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba zai jiƙa mutanen Kano da ayyukan alheri, ya ware sama da Naira biliyan 30

Ya jaddada bukatar amfani da fasahar dangwalen yatsa da ta daukar fuska da muryar mutum wajen tattara bayanai, don kauce wa kuskure.

Sanarwar ta rahoto Shugaba Tinunu yana cewa:

"Dole mu tsara tsari mai dorewa kafin mu nemi tallafin abokan hulda. Ba zan lamunci tsarin da ake samun kwan gaba kwan baya ba, dole ne sai mun hau kan madaidaiciyar hanya."

Minista ya fadi dalilin gaza yin kidaya

NPC ta fadi shirin da ta yi na gudanar da kidayar mutane da jama'a da zarar an samu kudi
NPC ta ce ta sayo kwamfutoci sama da 700,000, tana jiran a samu kudi ta gudanar da kidaya. Hoto: @natpopcom
Asali: Twitter

Ministan kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, ya ce bayanan kidayar za su kasance tubalin tsara manufofin ci gaba a nan gaba.

"A taron ministoci na 2023, Shugaba Tinubu ya jaddada kudirinsa na gudanar da kidaya. Babban matsalar kawai ita ce rashin isassun kudade," in ji Bagudu.

Ya bayyana cewa a shekarar 2006, kashi 40% na kudin kidayar ya fito ne daga abokan hulda, don haka akwai bukatar hadin gwiwa don samun tallafin da ake bukata.

Bagudu ya kara da cewa NPC, NBS, NIMC, ma’aikatar tattalin arzikin zamani, rijistar masu zabe, da bayanan sadarwa suna tattaunawa da hukumar NASRDA don tantance yawan bayanan da gwamnati ke da su.

Kara karanta wannan

An kashe mutane 10, an lalata dukiyar Naira biliyan 11 a zanga zangar Kano

Shirye-shiryen da NPC ta yi na kidaya

A nasa jawabin, Shugaban NPC, Nasir Isa Kwarra, ya ce shekaru 19 kenan tun bayan kidayar ƙarshe, kuma alkaluman da ake amfani da su sun tsufa.

Nasir Kwarra ya ce lallai akwai bukatar gudanar da sabuwar gidaya ma damar ana so a inganta tsare-tsaren gwamnati da kawo ci gaba a kasa.

Ya bayyana cewa an riga an sayo kwamfutoci 760,000 domin gudanar da kidayar, kuma an ajiye su a hannun CBN.

Ya kuma tabbatar da cewa hukumar NPC za ta tuntubi abokan huldarta domin samun tallafi idan Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da kidayar.

NPC ta sanya lokacin gudanar da kidaya

A baya, Legit Hausa ta ruwaito cewa, shugaban hukumar kidayar jama’a ta kasa, Nasir Isa Kwarra, ya bayyana cewa Najeriya za ta gudanar da kidaya a 2025.

Nasir Isa Kwarra ya ce rashin kidaya tun 2006 ya haifar da kalubale wajen raba albarkatu, inganta kiwon lafiya, da rage mace-macen mata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.