Abba Ya Zama Gwamnan Gwamnonin Afrika, An Gwangwaje Shi a Kasar Waje

Abba Ya Zama Gwamnan Gwamnonin Afrika, An Gwangwaje Shi a Kasar Waje

  • Mujallar African Leadership Magazine (ALM) ta karrama Gwamna Abba Kabir Yusuf a matsayin Gwamnan Afrika na shekarar 2025
  • Mujallar ta jero bangarori da dama da ya yi zarra idan aka kwatanta shi da takwarorinsa, inda ta ce wannan babban abin koyi ne
  • A lokacin da ya karbi lambar yabon, gwamna Abba Kabir Yusuf ya sadaukar da ita ga mutanen Kano, wanda ya ce su ne ginshikin ci gaban

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar KanoGwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya samu lambar yabo ta Gwamnan Afrika na Shekarar 2025 kan Kyakkyawan tsarin gudanar da mulki.

Mujallar African Leadership Magazine (ALM) ce ta karrama gwamnan a karon da ta gudanar karo na 14, wanda aka yi a Casablanca, da ke kasar Maroko.

Kara karanta wannan

An bankado umarnin Tinubu da zai illata Arewa, NARTO ta gargadi gwamnati

Gwamna
An ba gwamnan Kano lambar yabo Hoto: Sanusi Bature D– Tofa
Asali: Facebook

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya fitar da sanarwar a madadin mashawarta da jami’an hulda da jama’a na wasu shugabannin Afrika da suka halarci taron a Otal ɗin Marriot da ke Casablanca.

Dalilin karrama gwamnan jihar Kano

Sanarwar ta ce karramawa na nuni da jagoranci na kwarai da Gwamna Yusuf ke yi wajen tabbatar da gaskiya, rikon amana, da mulkin ba tare da nuna wariya ba.

Ta kara da cewa sauye-sauyen da gwamnatin Gwamna Abba ke aiwatarwa a fannonin ilimi, gine-gine, kiwon lafiya, da bunƙasa tattalin arziki ya a zama abin misali.

Gwamnan Kano ya sadaukar da lambar yabo

Da yake wakiltar gwamnan a taron, Mai ba da shawara na musamman kan harkokin jiha, Alhaji Usman Bala, ya ce gwamnan ya sadaukar da lambar yabo ga al’ummar Kano.

Gwamna
Lambar yabon da aka ba gwamna Abba Kabir Yusuf Hoto: Sanusi Bature D–Tofa
Asali: Facebook

Ya jaddada cewa jama'ar da suka zabe shi, su ne ginshikin ci gaban da wannan gwamnati ke samu da har duniya take gani a yanzu.

Kara karanta wannan

Ministan tsaro ya yi albashir ga Arewa kan matsalar ta'addanci, ya tabo alaka da Nijar

Mujallar African Leadership ta yabi gwamnan Kano

A cewar mujallar African Leadership, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Yusuf, Kano ta cimma manyan nasarori, ciki har da ware fiye da 31% na kasafin kuɗin jihar ga ilimi.

Haka kuma ta yabi yadda yake daukar nauyin ɗaliban digiri na biyu a ƙasashen waje, da aiwatar da tsarin tafiyar da mulki ta hanyar fasahar zamani.

Sanarwar ta ce:

“Gwamna Yusuf ya himmatu matuƙa wajen kyautata mulki, lamarin da ya sa ya samu lambobin yabo na ƙasa da na duniya, ciki har da Gwamnan Shekara a Fannin Ilimi daga jaridar New Telegraph, Gwamnan da Ya Fi Kula da Fansho daga Ƙungiyar Ƙwadago ta Masu Fansho ta Najeriya, da Gwamnan da Ya Fi Kula da Malamai daga Ƙungiyar Malaman Najeriya, da sauransu.”

Kwamitin editoci na mujallar ALM ya yaba da ƙoƙarinsa, yana mai cewa, gwamna Yusuf kyakkyawan misali ne na sauyin shugabanci a Afrika.

Kara karanta wannan

El-Rufai ya sake dagula siyasa, ya gana da shugabannin PDP, an yada hotunan ganawar

Shugabannin da aka karrama bayan na Kano

Baya ga Gwamnan Kano, wasu fitattun shugabanni da aka karrama a taron sun haɗa da Shugaba Andry Rajoelina na Madagascar, Firaminista Robinah Nabbanja ta Uganda.

Haka kuma an karrama tsohon shugaban Tanzania, Dr. Jakaya Kikwete, Lefoko Maxwell Moagi, tsohon Ministan Ma’adinai da Makamashi na Botswana da dai sauransu.

Abdullahi Abbas na kwadayin kujerar gwamnan Kano

A baya, mun wallafa cewa shugaban APC reshen jihar Kano, Abdullahi Abbas ya bayyana cewa muradinsa ya wuce ya sake koma wa kujerar shugabancin jam'iyyar, sai dai ya zama gwamna.

Wannan na zuwa ne a matsayin martani ga kalaman karamin Ministan gidaje da raya karkara, Yusuf Ata, inda ya zargi Abdullahi Abbas na kokarin komawa kujerarsa karo na hudu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.