'Akwai Matsala': Direbobi Sun Yi Abu 1 da Zai Jawo Karancin Man Fetur a Najeriya

'Akwai Matsala': Direbobi Sun Yi Abu 1 da Zai Jawo Karancin Man Fetur a Najeriya

  • Direbobin tankunan mai sun dakatar da ɗaukar fetur a Legas da wasu jihohi saboda zargin cin zarafi daga jami’an gwamnatin jiha da tarayya
  • Kamfanonin sadarwa sun bayyana damuwa kan yiwuwar katsewar hanyoyin sadarwa idan an kasa samar da dizal ga injinoninsu a kasar
  • Shugaban NARTO, Yusuf Othman, ya ce jami’an tsaro na kwace motocin direbobin, lamarin da ke hana su ɗaukar man fetur a kwanakin nan
  • Yusuf Othman ya ba gwamnatin Legas da ta tarayya shawara yayin da yake fargabar ci gaba da kin dakon fetur a cikin satin da muka shiga

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Ana fargabar yiwuwar ƙarancin man fetur a Legas da wasu sassa na Najeriya bayan direbobin tankar mai sun dakatar da ɗaukar kaya.

Direbobin sun dakatar da aiki ne bisa zargin cin zarafi daga jami’an gwamnatin jihar Legas da ma’aikatar sufuri ta tarayya.

Kara karanta wannan

An bankado umarnin Tinubu da zai illata Arewa, NARTO ta gargadi gwamnati

Direbobin tanka sun magantu da suka daina dakon man fetur a Najeriya
Direbobi sun dauki matakin daina dakon man fetur sakamakon cin zarafi daga gwamnati. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Direbobi sun daina dakon man fetur

Haka kuma, kamfanonin sadarwa sun nuna damuwa kan yiwuwar katsewar hanyoyin sadarwa sakamakon matsalar isar da dizal, inji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun nuna cewa tankuna ba su ɗauki man fetur a ranakun Asabar da Lahadi ba, lamarin da ke haddasa fargabar matsalar man fetur.

Sai dai gwamnatin jihar Lagos ta ce tana aiwatar da tsarin e-call-up domin sarrafa zirga-zirgar manyan motocin jigila a yankin Lekki-Epe.

An ji abin da ya jawo matakin direbobin

Shugaban ƙungiyar direbobin tankar mai (NARTO), Yusuf Othman, ya ce jami’an gwamnati na cin zarafin mambobinsu ba tare da wani dalili ba.

Ya bayyana cewa jami’an tsaro na kwace motocin su da kuma cin zarafin direbobi, lamarin da ke hana su dakon man fetur.

Yusuf Othman ya ce har yanzu ba a san ko za a iya dakon man fetur a yau Litinin ba, bisa ga yadda ake cigaba da takaddamar.

Kara karanta wannan

Dalibai a Katsina sun tada jijiyar wuya bayan 'yan sanda sun kashe dan'uwansu haka siddan

Ya ce matakin na gwamnatin Lagos yana iya janyo matsalar karancin man fetur, matuƙar ba a samo mafita ba cikin gaggawa.

NARTO ta ba gwamnati mafita kan matsalar

Direbobin tankar mai sun fadi dalilin daina dakon man fetur a Najeriya
Tankokin NNPC yayin da suke layin jigilar man fetur daga matatar man Dangote a Legas. Hoto: @nnpclimited
Asali: Twitter

Shugaban NARTO ya yi gargadin cewa ba za a iya tafiyar da matatun mai ko dakon kayayyaki ba tare da motocin ɗaukar mai ba.

Ya bukaci gwamnati da ta kawo mafita domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba da ayyukan sufuri ba tare da cikas ba.

Ya kuma bayyana cewa wannan matsala ba ta da alaƙa da dokar hana manyan motoci 60,000 zirga-zirga da aka sanya a baya.

A cewarsa, matsalar ta samo asali ne daga jami’an gwamnatin jihar Legas da kuma ma’aikatar sufuri ta tarayya.

Karancin man fetur ya mamaye birnin Abuja

A wani labarin, mun ruwaito cewa, a safiyar Litinin, 19 ga Fabrairu, 2024, an tashi da dogayen layuka a gidajen mai na birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Rikicin kabilanci ya barke a Najeriya, an kashe mutane 7 yayin da 6 suka jikkata

Rahoton ya bayyana cewa karancin fetur ya bulla ne a daidai lokacin da ƙungiyar direbobin manyan motoci (NARTO) ta dakatar da jigilar man fetur.

NARTO ta bayyana cewa ta dakatar da ayyukann tankokin dakon mai saboda tsadar abubuwa da ke neman cin ƙarfinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

iiq_pixel