Sojojin Sama Sun Yi Ruwan Wuta kan 'Yan Bindiga, Sun Soye Miyagu Masu Yawa
- Dakarun sojojin saman Najeriya na ci gaba da samun nasara a yaƙin da suke yi da ƴan bindiga a jihar Zamfara da ke yankin Arewa maso Yamma
- Sojojin na rundunar Operation Fansan Yamma sun samu nasarar hallaka ƴan bindiga masu tarin yawa bayan sun samu bayanan sirri a kan ayyukansu
- Majiyoyi sun bayyana cewa sojojin sun hallaka ƴan bindiga 23 tare da ƙwato dabbobi masu yawa waɗanda suka sace
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Dakarun sojojin saman Najeriya na rundunar Operation Fansan Yanma sun samu nasara kan ƴan bindiga a jihar Zamfara.
Dakarun sojojin sun samu nasarar kashe ƴan bindiga da dama a ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.

Asali: Original
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan
Karya ta kare: Sojoji sun gano maboyar Bello Turji, sun fadi lokacin kawar da shi
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojojin sama sun ragargaji ƴan bindiga
Majiyoyi sun bayyana cewa wannan nasarar ta biyo bayan samun bayanan sirri da aka yi kan ƴan bindigan.
Bayanan sun nuna cewa gungun ƴan bindigan da ake zargin ƴan uwan Ado Aleiro ne, tare da wasu mutane da ba a tantance ba, sun bar ƙaramar hukumar Tsafe don satar dabbobi daga ƙauyukan da ke makwabtaka da ita.
Majiyoyin sun ce ƴan bindigan sun yi nasarar satar dabbobi da dama sannan suna ƙoƙarin tserewa lokacin da suka ci karo da jami'an tsaro na yankin.
Jami'an tsaron sun bi sawun masu satar dabbobin kuma suka jira har sai da suka isa wani wuri mai tsaunuka kafin su kewaye su.
Bayan tabbatar da wurin da suke, sun sanar da rundunar sojojin saman Najeriya, wacce da sauri ta tura jiragen yaƙi don kai farmaki kan ƴan bindigan.
Sojoji sun kashe ƴan bindiga masu yawa
Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa an kashe ƴan bindiga da dama a harin duk da cewa ba a faɗi adadin waɗanda aka hallaka ba.
Sai dai, wata majiya ta bayyana cewa an kashe aƙalla ƴan bindiga 23 tare da jikkata wasu da dama.
Majiyoyin sun ce dakarun sun kuma ƙwato adadi mai yawa na dabbobin da ƴan bindigan suka sace.
Wannan farmakin dai yana daga cikin ƙoƙarin da sojoji ke yi na rushe sansanonin ƴan bindiga da kuma daƙile satar dabbobi.
Satar dabbobi dai ta kasance babbar hanyar samun kuɗaɗen shiga ga ƙungiyoyin ƴan bindiga da ke aiki a jihar Zamfara da jihohin da ke makwabtaka da ita.
Sojoji sun ragargaji ƴan bindiga a Sokoto
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Fansan Yamma sun kai farmaki kan ƴan bindiga a jihar Sokoto da ke yankin Arewa maso Yamma.
Sojojin a yayin farmakin wanda suka kai a dajin Sakkarawa da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni, sun hallaka ƴan bindiga masu tarin yawa.
Dakarun sojojin sun kuma raunata ƴan bindiga masu yawa a artabun da suka yi da su a sansanin na su da ke cikin dajin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng