Dalibai a Katsina Sun Tada Jijiyar Wuya Bayan ’Yan Sanda Sun Kashe Dan’uwansu Haka Siddan
- Dalibai a jami’ar FUDMA da ke Katsina sun bayyana bacin ransu bayan kashe dalibi abokin karatunsu a cikin jihar
- Wannan ya faru ne a daidai lokacin da jihohin Arewa masu Yammacin Najeriya ke fuskantar kalubalen tsaro a yanzu
- Rahoto ya bayyana yadda aka kai ga hallaka dalibin har dalibai suka fara zanga-zangar nuna Rashin amincewarsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Jihar Katsina - An tafka zanga-zanga mai zafi a Jami’ar Tarayya da ke Dutsin-Ma (FUDMA), Jihar Katsina, bayan kashe wani ɗalibi da ake zargin ƴan sa-kai na yankin ne suka yi.
A ranar Juma’a, ɗaruruwan dalibai sun fita tituna domin nuna fushinsu, inda suka tare babbar hanyar Dutsin-Ma zuwa Katsina, tare da kunna tayoyi da hana ababen hawa wucewa.

Asali: Twitter
Yadda lamarin ya faru
Ɗalibin da aka kashe an bayyana sunansa da Sa’id Abdulkadir, dalibi ne a ajin ƙarshe a Tsangayar Noma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai har yanzu ba a tabbatar da gaskiyar dalilin kisan nasa ba, yayin da rahotanni daban-daban ke fitowa.

Kara karanta wannan
Ni ba Ba-Yarbe bane: IBB ya fadi gaskiyar karin sunan 'Babangida' a cikin sunansa
Wasu bayanai sun nuna cewa an zargi Abdulkadir da kasancewa mai ba da bayanai ga ‘yan bindiga, yayin da wasu ke cewa an harbe shi ne bisa kuskure yayin da yake tafiya akan babur na haya.
An harbi Abdulkadir da mai babur
Majiyoyi sun bayyana cewa jami’an tsaro sun yi ƙoƙarin tsayar da babur ɗin da ke ɗauke da Abdulkadir da wani mutum.
Sai dai matukin babur ɗin bai tsaya ba, lamarin da ya sa jami’an tsaro suka buɗe wuta, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar Abdulkadir nan take.
An kuma ruwaito cewa, matukin babur ɗin ya ji raunuka, inda aka garzaya da shi asibiti domin jinya a jihar.

Asali: Twitter
Dalibai sun fusata matuka
Bayan jin labarin kisan, ɗaliban jami’ar sun fito kwansu da kwarkwatarsu suna neman adalci. Sun yi kira ga mahukunta da su tabbatar da cewa an hukunta waɗanda suka aikata wannan danyen aikin.
Masu zanga-zangar sun nuna fushinsu ta hanyar toshe tituna, hana zirga-zirgar ababen hawa, tare da kunna tayoyi a kan hanya.
Wani daga cikin masu zanga-zangar ya ce:
"Ba za mu amince da irin wannan rashin adalci ba! Dole ne a binciki wannan lamari kuma a hukunta waɗanda suka aikata wannan laifi."
Jami’an tsaro sun shiga tsaka mai wuya
Yayin da zanga-zangar ke ƙaruwa, an tura jami’an tsaro, ciki har da sojoji da ‘yan sanda, domin kwantar da tarzomar.
Sun yi ƙoƙarin lallashin daliban da su janye daga tituna, amma lamarin ya yi ƙamari, inda aka samu tashin hankali tsakaninsu da masu zanga-zangar.
Matakin da jami’a da gwamnati ke shirin dauka
A halin yanzu, ba a sami cikakken martani daga mahukuntan jami’ar ba, amma ana sa ran za a gudanar da cikakken bincike kan wannan lamari domin gano gaskiyar abin da ya faru.
Zanga-zangar dai na nuna yadda ɗalibai ke matukar damuwa da rashin tsaro, musamman yadda matasa ke yawan rasa rayukansu a dalilin farmakin jami’an tsaro ko ‘yan sa-kai.
Ana sa ran hukumomi za su dauki matakan da suka dace domin tabbatar da cewa irin wannan abu ba zai sake faruwa ba.
Asali: Legit.ng