Yadda Ma’aikatan FUDMA su ka bar harabar Makaranta saboda gujewa harin Miyagu

Yadda Ma’aikatan FUDMA su ka bar harabar Makaranta saboda gujewa harin Miyagu

Bayanai sun fito a game da dalilin da ya sa mutane su ka fito su ka tare hanyar Katsina zuwa Marabar Kankara su na zanga-zanga a ranar Alhamis.

Jaridar Vanguard ta ce hare-haren da ‘yan bindiga su ka kai a jihar Katsina, da kuma barazanar shigowa yankin jami’ar FUDMA ta Dutsinma ya jawo zanga-zangar jiya.

Sakamakon rade-radin da aka ji cewa ‘yan bindiga za su kawo hari a jami’ar tarayyar, mutanen Turare su ka sa ma’aikatan jami’ar su ka tsere domin su kubuta.

Rahoton ya ce ma’aikata da malaman jami’ar FUDMA sun tsere daga makarantar ne da sassafe. Dole ma'aikatan su ka yi tawage su ka bar ofis bayan sun zo aiki.

Wani babban jami’in jami’ar da ya yi magana da jaridar, ya ce da ya ke tafiyar kilomita 22 ne tsakanin Dutsinma da kauyen Turare, dole su ka yi zagaye ta garin Sayaya.

Ma’aikata da sauran malaman jami’ar sun yi dogon yanke ta Sayaya da ke karamar hukumar Matazu, su ka shiga Kafin Soli a Kankia, daga nan su ka isa garin Dutsinma.

KU KARANTA: Malaman UNIMAID sun yi wata da watanni babu albashi

Yadda Ma’aikata Jami’a su ka bar harabar Makaranta saboda gujewa harin Miyagu
Wasu masu gudun hijira a Katsina
Asali: Twitter

Ma’aikacin jami’ar da ya bukaci a boye sunansa, ya ce sun yi zagayen kusan kilomita 100 ne saboda tsoron cewa ‘Yan bindiga za su iya kawo masu hari a ko da yaushe.

Ya ce: “Mu na cikin aiki a ofis da kimanin karfe 10: 00 na safe, sai mu ka fara jin labari cewa ‘Yan bindiga sun shiga kauyukan da ke makwabtaka da jami’ar a daren da ya gabata."

Ma’aikacin ya ce miyagun sun yi barna a inda su ka shiga, sun sace dabbobi, sun kashe mutane.

“A dalilin haka, shugaban jami’a ya bada umarni mu fice daga makarantar, mu shiga wajen jami’a ta cikin gari,, nan ta ke mu ka yi maza-maza mu ka yi tawaga zuwa Dutsinma”

“A kan hanya mu ka ji labari an yi wa kauyukan da ke kan titi barazanar za a kawo masu hari, sannan mutane sun shigo domin su samu wurin fakewa da dabbobinsu.”

Bugu da kari mutane sun fito su na zanga-zanga a kan halin da su ke ciki. Wannan ya sa ma’aikatan jami’ar su ka canza hanya, su ka yi zagaye domin su isa cikin gari.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng