Rikicin Kabilanci Ya Barke a Najeriya, An Kashe Mutane 7 Yayin da 6 Suka Jikkata
- Rikici tsakanin al'ummomin Gbelemonti da Maidoti a Edo ya yi sanadin mutuwar mutum bakwai, yayin da shida sukekwance a asibiti
- Rundunar ‘yan sanda tare da sojoji da 'yan sa kai sun dakile rikicin, kuma an fara bincike kan musabbabin wannan tashin hankalin
- Kwamishinan ‘yan sanda Betty Otimenyin ta ce za a binciko dalilin rikicin tare da tabbatar da an hukunta masu hannu a tayar da zaune tsaye
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Edo - Rahotanni sun bayyana cewa an kashe mutane bakwai tare da jikkata wasu shida a rikicin kabilanci da ya barke a Jihar Edo.
Rundunar ‘yan sandan jihar Edo ta ce a ranar 21 ga watan Fabrairu, rikici ya barke tsakanin al’ummomin Gbelemonti da Maidoti a karamar hukumar Ovia North-East.

Asali: Twitter
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Moses Yamu, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, inji rahoton Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kashe mutane 7, wasu 6 sun jikkata
Moses Yamu ya ce jami’an ‘yan sanda daga sashen Iguobazuwa, tare da hadin gwiwar sojoji da 'yan bijilanti, sun garzaya yankin domin dakile rikicin.
“Mun samu nasarar kwashe wasu daga cikin wadanda suka jikkata zuwa asibiti, inda aka tabbatar da mutuwar mutane bakwai, yayin da wasu shida ke karbar magani,” in ji Yamu.
Ya kara da cewa, an shawo kan rikicin, kuma an dawo da doka da oda a yankin, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da sintiri don tabbatar da zaman lafiya.
Edo: 'Yan sanda sun soma bincike
A cewarsa, rundunar ‘yan sanda ta fara bincike domin gano musabbabin rikicin da kuma hukunta wadanda ke da hannu a lamarin.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Betty Otimenyin, ta tabbatar da cewa babu wani abu da zai kawo cikas wajen gano gaskiyar lamarin da kuma daukar matakin da ya dace ba.

Kara karanta wannan
'Yan sanda sun dakile shirin masu garkuwa da mutane, sun cafke miyagun masu laifi
Kwamishinan ta bayyana rikicin a matsayin abin da za a iya kaucewa, inda ta gargadi jama’a da su rika kai korafi ga jami'an tsaro maimakon daukar doka a hannunsu.

Asali: Twitter
Cikakkiyar sanarwar da 'yan sanda suka fitar
A cewar sanarwar rundunar:
“A ranar 21 ga watan Fabrairu, 2025, misalin karfe 10 na safe, rundunar ta samu labarin rikicin da ya barke tsakanin al’ummomin Gbelemonti da Maidoti a karamar hukumar Ovia ta Arewa maso Gabas.
“Jami’an ‘yan sanda daga sashen Iguobazuwa, tare da sojoji da kungiyar 'yan sa kai, sun hanzarta zuwa wurin don dakile rikicin.
“Mun samu nasarar kwashe wadanda suka jikkata zuwa asibiti, inda aka tabbatar da mutuwar mutane bakwai, yayin da wasu shida ke ci gaba da karbar magani.
“An shawo kan rikicin, kuma an tabbatar da zaman lafiya a yankin yayin da bincike ke ci gaba don gano musabbabin lamarin.
“Kwamishinan ‘yan sanda, CP Betty Enekpen Isokpan Otimenyin, ta bayyana cewa rundunar za ta yi aiki tukuru wajen tabbatar da adalci.
“Ta kuma gargadi jama’a da su guji daukar doka a hannunsu tare da shawartar su da su rika kai koke ga hukumomi maimakon tayar da fitina.”
Jigawa: Mutane 11 sun mutu a fadin kabilanci
A wani labarin, mun ruwaito cewa, an kashe akalla mutane 11 tare da kona gidaje 31 a yankin Gululu da ke Jahun da Miga, Jihar Jigawa a rikicin kabilanci.
Wani dattijo Bafulatani, Sulaiman Abubakar Jahun, ya ce ya rasa 'ya'yansa biyar a rikicin da ya haddasa asarar rayuka da dukiyoyi.
Hukumar SEMA ta raba tallafi ga wadanda suka jikkata da masu asara, ciki har da shinkafa da kudi, tare da alkawarin tabbatar da zaman lafiya.
Asali: Legit.ng