Yan Bindiga Sun Lallaba cikin Babban Asibitin Kano, Sun Sace Dattijuwa Mai Shekaru 60
- Wasu da ake zargi da garkuwa da mutane sun sace wata mata mai shekaru 60, Talatu Ali, a Asibitin Dawanau da ke jihar Kano da ke Arewacin Najeriya
- An tabbatar da cewa maharan sun dauke matar ce yayin da take layi a asibitin domin jiran ganin likita saboda rashin lafiyar da ke damunta
- Ɗanta da kuma dan uwanta ne suka kai ta asibiti daga Yar Gaya, amma daga baya suka gano cewa ta bace ba tare da sanin inda take ba inda suka kai rahoto
- Majiya ta ce a ranar 21 ga Fabrairu, wani mutumi da ba a sani ba ya kira yana cewa Talatu na hannun su, yayin da 'yan sanda suka tabbatar da sace ta
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Rahotanni sun tabbatar da cewa masu da ake zargin da garkuwa da mutane sun sace wata dattijuwa a asibiti da ke jihar Kano.

Kara karanta wannan
Yan bindiga sun kutsa da karfin tsiya cikin gida, sun sace malaman addini 2 a Adamawa
An ce ana zargi masu garkuwa sun sace matar mai shekaru 60, Talatu Ali, daga Asibitin Dawanau a Karamar Hukumar Dawakin Tofa, Jihar Kano.

Source: Facebook
An dauke wata dattijuwa a asibitin Kano
Rahoton Zagazola Makama ya tabbatar da cewa an sace matar ne yayin da take layi domin jiran ganawa da likita a asibitin Dawanau da ke jihar.
An ce yaronta mai suna Nasiru Aliyu, da dan uwanta, Aliyu Garba, sun kawo ta daga Yar Gaya a karamar hukumar Dawakin Kudu a ranar 19 ga Fabrairu, 2025, da misalin karfe 8:30 na safe.
Yayin da take cikin layin jiran likita, ba zato ba tsammani sai suka gano cewa ta bace inda aka neme ta sama ko kasa amma babu labarinta.
Duk kokarin da aka yi don gano ta a cikin asibitin bai yi nasara ba, lamarin da ya sa suka kai rahoto ofishin 'yan sanda na Dawanau.

Source: Facebook
Yan bindiga sun kira waya kan sace dattijuwar
A ranar 21 ga Fabrairu, 2025, da misalin karfe 7:00 na safe, Aliyu ya samu kira daga lamba da ba a sani ba, inda mai kiran ya tabbatar musu cewa Talatu na hannun su.
Hukumomi sun ce masu garkuwa da mutane na iya yin niyyar kai farmaki asibitin ne saboda rashin tsaron da ke ba su damar sace mutane ba tare da matsala ba.
Rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce an sace dattijuwar a asibiti mai suna Talatu Ali.
Yan bindiga sun sace malaman coci a Adamawa
Mun ba ku labarin cewa an tabbatar da cewa wasu mahara sun sace manyan fastoci guda biyu, Rabaran Mathew David Dusami da abokinsa, Rabaran Fr. Abraham Samman daga Taraba.
Yan bindigar sun sace Fasto Samman na Jalingo da Fasto Dusami na Yola a Gwaida Malam, Numan da ke jihar Adamawa da ke Arewa maso Gabas a Najeriya.
Kwamishinan 'yan sanda, CP Dankombo Morris, ya bukaci jama’a su taimaka da bayanai, yana mai cewa doka za ta hukunta masu hannu a sacewar.
Asali: Legit.ng
