Yanzu-yanzu: Kotu ta bada umurnin a duba lafiyar kwakwalwa da kunnen Sheikh Abduljabbar
- Kotun Musulunci dake Kofar Kudu ta ce a duba lafiyar kwakwalwar Abduljabbar a kotu
- Lauyoyinsa sun bukaci kotu ta basu takardun shari'ar su duba
- Gwamnatin jihar Kano ta shigar da Abduljabbar Kotu bayan muhawarar da yayi da Malaman Kano
Kano - Kotun Shari'ar Musulunci dake shari'a kan kara da gwamnatin jihar Kano ta shigar da Sheik AbdulJabbar Kabara ya bada umurnin aje a duba lafiyar kwakwalwar Malamin.
Kotun dake zaune a Kofar Kudu ta bada wannan umurni ne a zaman da aka yi ranar Alhamis, 2 ga watan Satumba 2021, rahoton BBC.
A cewar kotun, akwai bukatar gwada kwakwalwa da kunnuwan Malam Abduljabbar a asibitin Dawanau da na Murtala saboda rashin maganar da yayi lokacin da aka karanto masa tuhume-tuhume 4 da ake masa.
A riwayar Alheri Rediyo, Lauyoyin Abduljabbar sun bukaci kotun ta basu takardun shari'ar domin su duba kuma su daukaka kara.
A karshe, Alkalin kotun Musuluncin, Ibrahim Sarki Yola, ya ce a cigaba da tsare AbdulJabbar zuwa ranar 16 ga Satumba, 2021.
Gwamna Ganduje ya na mana shisshigi a shari’ar Abduljabbar Kabara inji Lauyoyinsa
A baya, Lauyoyin da suka tsaya wa babban malamin nan, Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, suna zargin gwamnati da tsoma kanta a cikin shari’ar da ake yi.
Jaridar Daily Trust ta rahoto lauyoyin shehin suna cewa Mai girma gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya na shisshigi a shari’ar da ake yi da malamin.
Lauyoyin sun yi kira ga masu ruwa da tsaki a wannan kara da ke kotu, da su sa wa gwamnatin Kano idanu sosai domin tabbatar da cewa gaskiya ta yi aiki.
Rahoton ya ce lauyoyin sun yi wannan jawabi ne yayin da su ka kira wani taron manema labarai a garin Kano, a yammacin Lahadi, 25 ga watan Yuli, 2021.
Saleh M. Bakaro ya ke cewa Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya fito ya na yin maganganun da za su iya jawo matsala a wannan shari’ar da ke gaban Alkali.
Asali: Legit.ng