‘Wallahi na Kusa Mutuwa’: Kalaman Tsohon Sanata Kenan Makwanni Kafin Mutuwarsa

‘Wallahi na Kusa Mutuwa’: Kalaman Tsohon Sanata Kenan Makwanni Kafin Mutuwarsa

  • Wani bidiyo da ya bayyana yana dauke da kalaman marigayi Sanata Lawal Yahaya Gumau ya girgiza mutane, inda ya ce ya kusa mutuwa
  • A bidiyon, Sanata Gumau ya bayyana bukatar samun wanda zai ci gaba da ayyukan alherin da suka fara a siyasa
  • Marigayin ya ce da gaske yake kan maganarsa, yana mai cewa jama’a su guji yaudarar ‘yan siyasa masu alkawuran bogi
  • An ce marigayin ya yi maganar makwanni kafin rasuwarsa wanda mutane da dama suke mamakin irin baiwar da Allah ya yi masa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Bauchi - Wani faifan bidiyo da aka rika yadawa kan kalaman marigayi Sanata Lawal Yahaya Gumau ya girgiza mutane.

A cikin bidiyon wanda aka ce Sanata Gumau ya yi kalaman ne makwanni da suka wuce ya bayyana cewa ya kusa mutuwa.

Kara karanta wannan

Rai ya yi halinsa: Tsohon sanatan Bauchi ya rasu a Abuja, an shirya jana'izarsa

Bidiyon marigayi sanata da yake fadin ya kusa mutuwa
An yada bidiyon marigayi Sanata Lawal Yahaya Gumau da yake cewa wallahi ya kusa mutuwa. Hoto: @BauchiVsion.
Asali: Facebook

Bidiyon marigayi Sanata da ya ba mutane mamaki

Wani mai amfani da kafofin sadarwa, @LadanSalihu1 shi ya wallafa faifan bidiyon a shafinsa na X a daren jiya Asabar 22 ga watan Faburairun 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A bidiyon an gano sanata Gumau na cewa yana neman magajinsa wanda zai ci gaba da ayyukan alheri da suka yi.

Har ila yau ya ce wallahi ya kusa mutuwa inda ya tabbatar da cewa da gaske yake yi ba wasa ba.

"Sanata Lawal Gumau ya ba wa taron siyasa mamaki makwanni da suka wuce lokacin da ya ce yana neman wanda zai gaje shi a siyasa domin yana gab da mutuwa. Ya rasu a safiyar yau Asabar. Allah ya gafarta masa kuma ya ba shi Aljannatul Firdausi. Amin."

- Cewar Ladan Salihu

An yi rashi bayan sanar da mutuwar tsohon sanatan Bauchi
Bidiyon Sanata Lawal Yahaya Gumau ya girgiza mutane da yake cewa ya kusa barin duniya. Hoto: @BauchiVsion.
Asali: Twitter

Kalaman marigayi sanata a faifan bidiyo

Marigayin a cikin bidiyon ya ce:

"Dama zai maimaita abin da ya yi da, idan za mu samu ya maimaita abin da ya yi a baya, to kwalliya ta biya kudin sabulu.

Kara karanta wannan

Mutuwa mai yankan kauna: Fitaccen basarake ya rasu, Tinubu ya jajantawa al'umma

"Kun gan ni nan jama'a, wallahi tallahi na yi kusan mutuwa, wallahi tallahi da gaske na ke yi muku.
"Ina neman magaji a siyasa, ina neman wanda yau idan babu ni zai ci gaba da abubuwan alheri da muke yi, jama'a ba su da yawa ka da ka yaudari kanka.
"Waye ba a sani ba ne a siyasa, waye ba mu sani ba, waye ne ba mu ga takunsa ba? duk karyar lokacin zabe ne ana yawo gidan sarki ana yaudararsu ana cin zabe shikenan."

Wannan kalaman ya girgiza mutane inda suka yi mamakin irin wannan baiwa da Allah ya yi masa yana daf da barin duniya.

Tsohon sanatan Bauchi ya rasu a Abuja

Mun ba ku labarin cewa tsohon sanatan Bauchi ta Kudu, Lawal Yahaya Gumau, ya rasu a Abuja bayan gajeriyar rashin lafiya.

An ce Sanata Gumau ya rasu ne da misalin karfe 3:45 na daren ranar Asabar 22 ga watan Faburairun 2025 yana da shekaru 57 a duniya.

Rahotanni sun tabbatar cewa Gumau ya fara zama sanata a 2018 bayan mutuwar Ali Wakili inda aka sake zabensa a 2019, amma bai yi nasara a 2023 ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.