Gwamnati Ta Sanar da Fara Daukan 'Yan Sanda a Karon Farko a 2025

Gwamnati Ta Sanar da Fara Daukan 'Yan Sanda a Karon Farko a 2025

  • Rahotanni na nuni da cewa hukumar kula da aikin 'yan sanda ta kasa tare da sufeton 'yan sanda IGP Kayode za su debi sababbin kuratan 'yan sanda
  • Bayanan da 'yan sanda suka wallafa sun nuna cewa za a dauki wadanda suka taba rubuta jarabawar CBT a watan Maris 2024 amma basu samu nasara ba
  • Ana bukatar su duba sunayensu a shafin yanar gizo sannan su je gwajin lafiya daga daga Fabrairu zuwa Maris domin samun damar shiga aikin a bana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - An bayyana sabuwar sanarwa daga Hukumar kula da aikin ‘yan sanda na kasa tare da hadin gwiwar rundunar ‘yan sandan Najeriya kan daukar sababbin kuratan jami'ai.

Sanarwar ta fito ne daga bakin SP Abdullahi Haruna Kiyawa, mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda reshen Kano.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun dakile shirin masu garkuwa da mutane, sun cafke miyagun masu laifi

Yan sanda
Za a fara daukar 'yan sanda a 2025. Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanan da SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya yi ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Asabar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda za a dauki 'yan sanda a 2025

A cewar sanarwar da rundunar 'yan sanda ta fitar, babu bukatar sake cike takardar neman aikin wannan karo.

Sai dai duk da haka za a dauki wadanda suka taba neman aikin a shekarar 2024 har suka rubuta jarabawar CBT a ranar 5 da 6 ga watan Maris, amma basu samu nasara ba.

Wadanda suka dace su shiga cikin wannan tsarin ana bukatar su duba sunayensu a shafin yanar gizo na hukumar 'yan sanda domin tantance su.

Lokacin gwajin lafiya da muhimman matakai

Rundunar ta ce duk wanda ya ga sunansa a jerin wadanda aka amince da su zai ya fitar da takardar gayyata domin halartar gwajin lafiya.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda na kara karfi, sun kai hari kan jami'an tsaro inda ake zargin Turji ya boye

Za a gudanar da wannan gwaji ne a asibitocin 'yan sanda dake hedikwatar yankuna 17 a fadin Najeriya daga 26 ga Fabrairu zuwa 12 ga Maris 2025

Hakan na nuna cewa wanda bai samu damar zuwa a lokacin da aka tsara ba, to ya rasa damar shiga aikin a wannan karo.

'Yan sanda sun dauki matakin daukar wadanda suka taba yin rajista ne domin kurewar lokaci idan aka ce hukumar za ta fara daukar mutane daga matakin farko.

Kiyawa
Kakakin 'yan sandan Kano, SP Kiyawa. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa.
Asali: Facebook

Kiran 'yan sanda ga jama'a

Hukumar ‘yan sanda ta bukaci jama’a su yada wannan sanarwa musamman ga wadanda ke kauyuka domin kada su rasa wannan dama.

Duk mai bukata zai iya ziyartar shafin yanar gizon 'yan sanda domin duba cikakken bayanai kan sanarwar domin sanin matsayinsa wajen daukar aikin da sauransu.

A karshe, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya yi addu'ar Allah Ya ba wa mai rabo sa'a a tsakanin matasan da suke neman aikin a wannan karon.

Kara karanta wannan

Adamawa: An shiga fargaba da bindiga ta tashi a wurin ibada, mutane sun jikkata

Sojoji na bin diddigin Bello Turji

A wani rahoton, kun ji cewa dakarun sojin Najeriya na bin diddigin jagoran 'yan ta'adda, Bello Turji domin kama shi ko hallaka shi.

Shugaban sojin kasan Najeriya ne ya bayyana haka a yayin ziyarar farko da ya kai jihar Zamfara a kokarin jaddada manufar yaki da 'yan bindiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng