Majalisa Ta Ɗauki Matsaya kan Buƙatun Kirkiro Sababbin Jihohi 31 a Najeriya

Majalisa Ta Ɗauki Matsaya kan Buƙatun Kirkiro Sababbin Jihohi 31 a Najeriya

  • Majalisar Wakilai ta hannun kwamitin gyaran kundin tsarin mulki ta ce bukatun kirkiro sababbin jihohi 31 a Najeriya ba su cika sharuɗɗan doka ba
  • Shugaban kwamitin kuma mataimakin kakakin Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu ne ya bayyana haka a wani taro da suka shirya a Akwa Ibom
  • Ya ce kwamitin ya ƙara wa'adin miƙa bukatu zuwa 5 ga watan Maris domin bai wa mutane damar ba da gudummuwa a aikin gyarin kundin tsarin mulki

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Akwa Ibom - Shugaban kwamitin gyaran kundin tsarin mulki na majalisar wakilai, Rt Hon Benjamin Kalu, ya ƙara bayani kan batun kirkiro jihohi 31.

Hon. Benjamin Kalu ya bayyana cewa buƙatun da aka gabatar na kirkiro sababbin jihohi 31 ba su cika sharuɗɗan kundin tsarin mulkin Najeriya ba.

Benjamin Kalu.
Majalisar wakilai ta ce bukatun kirkiro sababbin jihohi 31 ba su cika sharuɗdan doka ba Hoto: @HouseNGR
Asali: Facebook

Majalisar Wakilai ta shirya taro

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda na kara karfi, sun kai hari kan jami'an tsaro inda ake zargin Turji ya boye

Kalu, wanda shi ne mataimakin kakakin Majalisar Wakilai, ya faɗi haka ne a wani taro a Ikot Ekpene da ke jihar Akwa Ibom ranar Juma'a kuma ya wallafa shafin X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taron, wanda aka gudanar daga 20 zuwa 23 ga Fabrairu, 2025, an shirya shi ne domin ƴan kwamitin yi wa kundin tsarin mulki garambawul.

Majalisar Wakilai ta 10 ta shirya taron tare da hadin gwiwar cobuyar tsare-tsaren doka da da goyon bayan UK Foreign, Commonwealth, da ofishin FCDO.

Ina aka kwana kan batun kirkiro jihohi 31?

Hon. Kalu ya amince da cewa bukatar kirkiro sababbin jihohi na da muhimmanci a tsarin mulki, kuma yana nuna burin al’ummomi daban-daban.

Sai dai ya bayyana cewa bukatun da aka gabatar kawo yanzu na kirkiro jihohin ba su dace da sharuddan da doka ta shimfiɗa ba.

Bisa haka, ya ce kwamitin ya kara wa’adin gabatar da bukatu kan gyaran kundin tsarin mulki zuwa 5 ga Maris, 2025, don bai wa jama’a karin dama su ba da ta su gudummuwar.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba zai jiƙa mutanen Kano da ayyukan alheri, ya ware sama da Naira biliyan 30

Ya kara da cewa za a iya ƙara wa’adin nan gaba idan har kwamitin ya ga akwai bukatar hakan bayan kammala tattaunawa a taron.

Benjamin Kalu.
Majalisa ta kara wa'adin miƙa bukatu kan gyaran kundin tsarin mulki Hoto: @OfficialBenKalu
Asali: Twitter

Majalisa ta duƙufa gyaran kundin doka

Ya kuma bayyana cewa majalisar wakilai na duba kudurori 151 na gyaran kundin tsarin mulki, abin da ke nuna kokarin ‘yan majalisa na kyautata tafiyar da mulki a Najeriya.

“Duk da cewa mun karɓi bukatu 31 na kirkiro sababbin jihohi, babu ko guda ɗaya da ya cika ka’idojin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.
“Saboda haka, mun kara wa’adin shigar da bukatu har zuwa 5 ga Maris, 2025. Amma idan bayan wannan taron muka ga har yanzu akwai matsaloli da ke hana jama’a gabatar da bukatunsu, za mu iya kara wa’adin.”

- Benjamin Kalu.

Ɗan Majalisa ya bukaci kirkiro jihohi 3

A wani rahoton, kun ji cewa ɗan majalisar wakilan tarayya, Hon. Oluwole Okeya gabatar da kudirin neman kirkiro ƙarin jihohi uku a Najeriya.

Jihohin da ɗan Majalisar ya bukaci a ƙirƙiro a kudirin da ya gabatar sun haɗa da Oke-Ogun, Ijebu da Ife-Ijesa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262