Zamfara: Sojoji Sun Lalata Sansanin Rikakken Dan Ta'adda, Sun Kwashe Buhunan Abinci
- Dakarun 'Operation TSAFTA DAJI III' sun fatattaki 'yan bindiga a yankin Zurmi da ke jihar Zamfara
- Sojojin yayin farmakin sun kwace makamai da kayan soji bayan 'yan ta’adda sun tsere cikin daji
- Dakarun sun kai farmaki Tungar Fulani, inda suka lalata sansanin Sani Black da kuma kai hari Gidan Baye Auta, suka kashe dan ta’adda daya
- Rundunar ta kuma yi nasarar kwace babur da kayan abinci daga ‘yan ta’adda a Kalage
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gusau, Zamfara - Dakarun 'Operation TSAFTA DAJI III' Mataki na 2, sun kai hare-hare kan ‘yan bindiga a Zurmi, Jihar Zamfara.
Dakarun Sojojin sun kwace makamai, harsasai, da kayan soji da kuma babura yayin harin.

Asali: Original
Dan majalisa ya fadi inda Turji yake
Bisa bayanan sirri, sojoji sun kai farmaki sansanin Sani Black a Tungar Fulani ranar 20 ga Faburairu, 2025, cewar rahoton Zagazola Makama.

Kara karanta wannan
Sojoji sun yi ragargaza mai zafi, sun kashe 'yan ta'adda 82, sun kwato tarin makamai
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasu rahotanni sun ce an gano Bello Turji a gabashin Sokoto, inda ake zargin ya kakaba harajin ₦25 miliyan kan wasu kauyuka.
Wani dan majalisar jihar ne, Hon. Aminu Boza ya tabbatar da hakan yayin zantawa da manema labarai.
Hon. Boza ya neman a dauki matakin gaggawa don dakile ayyukan Turji saboda yadda yake cutar da al'umma.
An lalata sansanin dan ta'adda, Sani Black
Majiyoyi sun tabbatar da cewa lokacin da sojoji suka kai harin sun tarar ‘yan ta’adda sun tsere amma sun lalata sansanin Sani Black.
Bincike ya kai ga gano makamai da kayan yaki, ciki har da manyan bindigogi, kwanson harsasai, takalman sojoji, da kayan sadarwa.
Bayan hakan, sojoji sun nufi Gidan Baye Auta, inda suka gamu da farmakin ‘yan ta’adda, sun mayar da martani, suka kashe guda daya, sauran sun tsere.

Asali: Twitter
Sojoji sun kwashe buhunan abinci da makamai
Dakarun sun kwace babur daga wanda aka kashe daga baya bayanan sirri sun kai su kauyen Kalage, inda suka gano kayan abinci na ‘yan ta’adda.

Kara karanta wannan
'Yan sanda sun dakile shirin masu garkuwa da mutane, sun cafke miyagun masu laifi
Sun kwace buhunan dawa 10 da ake amfani da su wajen ciyar da ‘yan ta’adda wanda ke kara musu ƙarfi.
Wannan na daga cikin kokarin dakile hanyoyin samun kayan masarufi da rundunar sojoji ke yi.
Dakarun Najeriya na ci gaba da kai hare-hare a yankunan ‘yan ta’adda a Zamfara da Arewa maso Yamma, suna hallaka ‘yan ta’adda da lalata sansanoninsu.
Jami’an tsaro sun bukaci jama’a su rika ba da rahoto kan duk wata shakka, domin kawo karshen ‘yan ta’adda a yankin baki daya.
Hafsan sojoji ya kai ziyara jihar Zamfara
A baya, kun ji cewa Shugaban sojojin kasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya kai ziyarar aiki ta a Zamfara tun bayan nadinsa, a ranar 30 ga Oktoba, 2024.
Oluyede ya karɓi bayanai daga manyan kwamandojin soji kan nasarorin baya-bayan nan da matakan dakile ‘yan ta'adda a jihar Zamfara.
An ce Laftanar-janar Oluyede ya gana da dakarun rundunar don karfafa musu gwiwa da kuma tabbatar da ci gaba da yaki da miyagu, irinsu Bello Turji.
Asali: Legit.ng