'Bikin Gata': Gwamna a Arewa Zai Aurar da Mata 300, An Fara Rabon Gado da Katifu

'Bikin Gata': Gwamna a Arewa Zai Aurar da Mata 300, An Fara Rabon Gado da Katifu

  • Gwamnatin jihar Kebbi ta fara raba gado, katifa da kujeru ga amaren da za a aurar a shirin "Auren Gata" na ranar 27 ga Fabrairu
  • Gwamna Nasir Idris zai yi amfani da shirin wajen aurar da mata 300 daga sassa daban-daban na jihar domin rage musu dawainiyar aure
  • Kwamishinan labarai, Alhaji Yakubu Ahmed-BK, ya bayyana cewa shirin 'Auren Gata' na bana zai fi wanda aka yi a bara inganci

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kebbi - Gwamnatin jihar Kebbi ta fara shiri gadan gadan na aurar da mata 300 a ranar 27 ga watan Fabrairun 2025.

A shirin aurar da matan mai taken 'Auren Gata', gwamnati tare da hadin gwiwar gidauniyar NANAS sun fara raba kayayyakin ga wadanda za su ci gajiyar shirin.

Gwamnatin jihar Kebbi ta yi magana da game da shirin auren gata na shekarar 2025
Gwamnatin Kebbi ta fara rabon kayan daki ga ma'auratan da za a aurar a 2025. Hoto: @KabiruAmadu_MP
Asali: Twitter

An fara shirye-shiryen auren gata a Kebbbi

Kara karanta wannan

'Ya aikata laifuffuka 5': An gurfanar da fitaccen mawakin Najeriya a gaban kotu

Jaridar Punch ta ruwaito cewa gwamnatin Kebbi ta shirya yin bikin "Auren Gata" a fadar Sarkin Gwandu da ke jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Nasir Idris ne ya kafa shirin "Auren Gata" da nufin tallafa masoyan juna, mata da maza 300 daga sassan jihar daban-daban.

Gidauniyar NANAS da Gwamnatin Kebbi ne ke jagorantar shirin, wanda kuma shi ne wani bangare na ayyukan jin kai na uwargidan gwamna, Nafisa Nasir Idris.

'Shirin bana zai fi armashi' - Gwamanti

Da yake jawabi yayin raba kayayyakin a Birnin Kebbi ranar Alhamis, kwamishinan watsa labarai da al’adu, Alhaji Yakubu Ahmed-BK, ya ce wannan shiri zai fi na bara tsari.

Ya bayyana cewa isowar kayayyakin tun da wuri ya ba da damar fara rabawa cikin lokaci domin tabbatar da nasarar shirin a bana.

"Gwamnatin jihar Kebbi da gidauniyar NANAS sun nuna cikakken goyon baya ga wannan shiri. Muna fatan za a ci gaba da wannan yunƙuri," in ji kwamishinan.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba zai jiƙa mutanen Kano da ayyukan alheri, ya ware sama da Naira biliyan 30

Kebbbi: Kayayyakin aure da aka fara rabawa

Gwamnatin Kebbir ta kammala shirin aurar da mata 300 a watan Fabrairu
Gwamnatin Kebbi ta fara rabon kayan daki domin aurar da mata 300 a Fabrairu. Hoto: Yahaya Danjada
Asali: Facebook

A nasa jawabin, sakataren kwamitin sufuri kuma mukaddashin shugaban kwamitin, Alhaji Kabiru Alaramma, ya bayyana shirin a matsayin wata babbar ni’ima ga jihar da al’umma baki ɗaya.

"Mun fara rabon kayayyakin aure da suka hada da gadaje, katifu, kujeru da rigunan da amare da mazajensu za su sanya."

- Kabiru Alaramma.

Tsohon shugaban ma’aikata kuma memba a kwamitin sufuri, Safiyanu Garba-Bena, ya tuna cewa makamancin wannan shiri ya gudana cikin nasara a bara.

Ya shawarci amaren su yi amfani da kayayyakin da aka basu yadda ya kamata domin samun rayuwar aure mai inganci da kwanciyar hankali.

Tasirin 'Auren Gata' a jihar Kebbi

Shirin "Auren Gata" ya samu karbuwa sosai a Jihar Kebbi, inda ake sa ran ya rage radadin matsalar rashin auratayya da kuma taimaka wa gajiyayyu.

Gwamnatin jihar ta sha alwashin ci gaba da irin wannan shiri domin karfafa gwiwar matasa wajen yin aure ba tare da wahala ba.

Kara karanta wannan

Saukar farashi: Gwamna ya kawo shirin raba abinci kyauta a Ramadan

Masana sun bayyana cewa irin wadannan shirye-shirye na da tasiri wajen rage aikata munanan dabi’u da kuma bunkasa zamantakewa a cikin al’umma.

A bara, an gudanar da shirin cikin tsari, inda aka tabbatar da cewa dukkan ma’aurata sun samu tallafi da kayayyakin da suka dace don fara sabuwar rayuwa.

Gwamnonin Arewa sun shirya auren gata

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatocin jihohin Arewa da dama sun fara kawo tsarin yiwa matasa maza da mata auren gata domin tallafa masu su raya Sunnah.

Jihohi biyu na baya bayan nan su ne Kano da Kebbi, wadanda gwamnonin su suka shirya kashe miliyoyin kudi domin aurar da daruruwan 'yan mata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.